P10

69 8 1
                                    

💕 *BINTEE* 💕
       *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...10*

       _"...Assalamu Alaikum"_
Zaitun dake zaune tana kokarin juye musu taliyar da ta tafasa a kettle kunnuwan ta suka jiyo tashin sallamar da ya taho mata da bugun zuciya...dan tana jiyo sallamar gaban ta ya fa'di sai kuma ta kasa amsawa duk da bata san da wacce Hajiyan tazo ba da yake gidan mallakin ta ne, gashi kuma itan ma'aikaciyar ta ne, duk da haka sai taji ta kasa natsuwa da zuwan Hajiyan tuni ma cire batun aiki a lissafin ta mafitar da Adam yace zai nemo musu shine kullun cikin zuciyar ta dama.

Hajja ce ta fito jin sallamar Hajiyan inda ta amsa cike da fara'a mai tafe da fadanci tana kokarin bawa Hajiyan wajen zama.

Kokadan bazaka dubi fuskan Hajiyan kayi tunanin akwai wani abu cikin ranta ba...ganin da tayi Hajja na shirin bata wajen zama ne yasa tai saurin dakatar da ita da fadin " a a Hajja dama nazo wajen Zaitun ne".
" aww inajin tana ciki ai ki shiga mana..."
Cewar Hajja tana me kokarin komawa dakin ta da fatan Allah yasa kudin haya Zaitun ta kasa biya aka kawo mata Notice har gida.

_" Salamu Alaikum"_ !!
Saukar tashin Sallamar Hajiyan akaro na biyu sai dai wannan karon tayi sallaman ne gami da tura kofan dakin Zaitun dake a kare ta shigo ciki wanda yayi daidai da dawowan Zaitun cikin hayyacin ta.
Hijab din ta tayi saurin lalu6owa tana sakawa take amsa sallamar Hajiyan.
"..Hajiya sannu da isowa... ke da kanki kuma Hajiya haka..?"
" Dole ce ta sani zuwan nima ba'a son raina ba".
Hajiya tayi maganar tana mai samawa kanta wajen zama bisa karamar daddumar da ta gani shinfide a dakin.
Zama Zaitun tayi itama tana gaida Hajiyan a 'darare tamkar wacce tayi wa sarki karya.
" Zauna me kyau Zaitun magana nazo muyi da ke".
Cewar Hajiya Talatu bayan ta amsa gaisuwar Zaitunan.
Gyara zama Zaitun tayi jin cewa magana zasu yi.
" Zaituna kinsan Shahid Adam ko...?"
Kallon Hajiya tayi tana me girgiza mata kai..." Shaa..hid Adam Hajiya kina nufin...Adam din ki..?"
" Shi 'din dai, shi nake nufi..dama yana zuwa gidan nan ne..?"
" erh...Hajiya yana..zuwa amma ba...sosai ba..."
Tayi maganar ne a rarrabe sbd bugun da zuciyarta da ya kara tsanan ta.
" Yana dai zuwan kuma wajen ki yake zuwan ko...?"
Shiru Zaitun tayi bata bawa Hajiyan amsa ba...sbd ta fara hasaso dalilin zuwan Hajiyan.
Bata damu da rashin amsawar ba sai ma wata tambayar da ta sake jefa wa Zaituna.
" wace iriyar ala'ka ce tsakanin ke da shi..?"
'Kasa Zaitun tayi da kanta tana mai jin wani nauyi da kunyar Hajiyan na taso mata wanda sai yau din kadai ne taji haka game da Hajiyan.
" Zaitun ki fada min gaskiya..."
Haka kawai sai ta tsinci kanta da furta" Hajiya babu komai".
Shiru ne ya ratsa dakin na 'dan wani lokaci, kowa abinda yake sa'kawa cikin zuciyar sa daban, ita Zaitun rudani ta shiga yayin da Hajiyar ke kissima abubuwa da dama sam bata ga wata dacewa tsakanin Zaitun da Adam ba, bata san me ya jashi har ya birge shi game da yarinyar ba, baza'a kira Zaitun mummuna ba kam dan kyau tana da kyanta daidai gwargwado amma ita ai a ganin ta kyan dan maciji tayi.
Sai da Hajiya ta saki huci abinka da masu dan qiba sannan ta cigaba..." kikace babu komai?"
Kai Zaitun ta daga cikin taraddadin abinda ya dace tace da Hajiyan.
" Amma me yasa ya same ni da batun yana san auren ki..? Nasan kinsan komai gaula kawai kike son maishe dani"
" Toh kiji in fada miki wani abinda baki sani ba Zaituna".
Kadan ta dago ta dubi Hajiyan ta kuma 'dauke kanta da sauri" nasan a iya matsayin shekarun ki bazaki rasa sanin waye tsohon Sanata Jibrin Adam 'Dan maliki ba ko..?"
Shiru Zaitun tayi tana tunano inda tasan sunan, 'dagowa tayi ta kalli Hajiya lokacin da ta tuno wani dan siyasa ne me irin wannan sunan..."
Kamar tasan abinda ke ran Zaitun sai cewa tayi" 'Dan Maliki da kika sani wannan 'dan siyasan shine asalin mahaifin Adam Shaheed"
Hajiya ta fadi cike da tabbatarwa.
Idanu Zaitun ta zaro cike da mamaki...yayin da Hajiya ta cigaba da fadin.
" Adam da kike gani ba sa'an auren ki bane, bar ganin sa haka nan Adam mutun ne shi mai matukar kima da daraja uwa uba kamilallan yaro ne da kowa zai yi alfaharin kasancewar sa 'da agareshi, bar ma natun wannan, ta ya ma ke da shi din 'karamar kwakwalwar ku take muku tunanin ni Talatu zan amince 'da na, yaro irin Adam ya auri mace wulakantacciya irin ki?  Mace mai zaman kanta? Mace marar ilimi?
Macen da bata san kanta ba? Macen dana tabbatar ba kamilalliya bace, macen da ta bar gaban iyayen ta ta za6i tai zaman kanta..? haba baiwar Allah ki yiwa kanki adalci mana...bana raba 'dayan biyu ma korar ki iyayen ki suka yi saboda abin kunyar dakika jajibowa kanki..? kuma ni sai in zuba idanu ina ji ina gani in bar 'dana ya kwashe ki?..me ne suna na kenan?"
Shiru babu amsa tuni hawaye ya 6allewa Zaitun hakika in dai hakane ta zurma da yawa, amma me yasa sai Hajiya ta sata a gaba da wannan irin zagin cin da cin mutuncin dan kawai tana so ta rabu mata da 'dan ta...'daya bayan 'daya zagin da Hajiyan tai mata suke shiga kwakwalwar ta suke samun wuri..ji take ba'a ta6a ci mata mutunci irin hakan ba kaf din rayuwar ta.
Mufee dake zaune gefe ma tuni ta taso izuwa jikin Zaitun din ta jingina daga gefen ta tamkar tasan cin mutunci akewa uwar ta haka ta tsura idanu wa Hajiyan tana kallon ta.
" Dubi kanki fa? dube ki? dubi inda kike rayuwa?
inda ta fadi hakan tana me rarraba idanu a dakin Zaitunan...ita kam bata bukatar sai ta kalla ko Hajiyan bata fada ba tasan cewa ita din kaskantacciya ce batun yau ba..."Ko kusa Zaitun ko alama kai ko a wasan yara sam baki dace da auren 'daa na ba, kuma matukar ina raye matukar ina numfashi bazan ta6a kuskuren barin hakan ya faru ba har abada..."
" Dan haka daga yau daga yanzu..mintina ashirin ban amince ki sake karawa cikin gidan nan ba ki bar min kaya na..ki tafi duk inda zaki je, duk inda ya miki, akwai gidajen bariki da dama wadanda suka dace da zaman mace irin ki amma ba gidan Shaheed 'dina ba, gidan auren tsarkakke ne bai kuma dace da zaman mace watsatstsiya irin ki ba, ki tafi dan Allah kiyi ne sa da rayuwar yaro na.."
Numfashi Hajiya ta sauke sbd dogon maganar da tayi kuma ya kasance a zuciye take yin sa dole sai da ta sauke numfashi kafin ta cigaba.
" Na hada ki da Allah ne saboda in tabbatar miki cewa da gaske nake, in kuwa kika qi, kika bijirewa magana ta bisa son zuciyar ki da kwadayin da ke ranki wallahi Zaitun duk abinda na aikata agareki ki zargi kanki da kanki...".

Daga haka Hajiya ta mike tsaye ta kama hanyar barin dakin jakar ta rataye a dantsen hannun ta...sai kuma ta tsaya tace.." Karki manta mintina ashirin kacal na baki ki bar min gidana kashedi na na karshe da ke kenan...".

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now