P4

106 8 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️...4

         ......Bata yi kasa a gwiwa wajen fara bawa yarinyar kunun ba sai dai me kokadan Feefy bata son shi, idan ta bata ma ta rinka amai kenan sam ta rasa dalilin hakan..gefe guda kuma tsananin tashin hankali take shiga idan taji ko ta ga yarinyar cikin wani irin yanayi.

Maman Abdul ce ta bata shawaran cigaba da bata a hakan inda a hankali zata saba da shi tunda watannin ta sun riga sun kai gejin da zata iya sha din.

Inda tace ai ba dan ma shakkan zuciyar Zaitun da take ji ba da tuni yarinyar ta jima da fara cin abinci dan ko ba ita ba hatta su Siyama sun so su fara bata abinci idan suna ci amma Maman sun ke hana su.

Ido Zaitun ta waro kan Maman Abdul din.." bakya ganin tayi karama ne Maman Siyama watannin ta hudu ne fa kacal ko zama me kyau ma yaushe ta fara shi, ni da cewa ma fa sai ta kai watanni takwas kafin in fara bata abinci".
"..ahh haba har watanni takwas be yi yawa ba Zaitun, wai ni tausaya miki nake ne duba da yadda kike ta fadi tashin nan.."
"...saboda ita duk nake yi ai Maman Siyama"
"Nafi kowa sanin hakan Zaitun shiyasa nake so ki dan sassauta afara bata kunun yanzu muga yadda hali zaiyi.."
Zaitun bata sake musu wa Mmn Abdul din ba, dan tasan duk abinda matar ke dora ta akai bai ta6a cutar da ita ba, bata ta6a dana sanin bin shawaran Mmn Abdul ba dan haka wannan din ma tana da yakinin Insha Allahu bazata yi ba.

Kudi kawai ta bawa Mmn Abdul din ita ta aika aka siyo gyada ta gyara aka marka'da mata dashi ake yiwa Feefyn kunu amma ba'a saka mata tsamiya shiyasa duk ranar da Zaitun ta samu sukuni ta kan kara mata garin madara akai.

Cikin rashin sa'a Mufeeda sam bata son kunun nan in an bata dawo dashi take yi in an matsa akai mata dura kuwa..haka zata harar da shi gashi ta rika kuka kenan taki yin shiru.

Hankalin Zaitun tashi yake idan taga hakan, cike da marairaita idanu ruwa ruwa ta dubi Mmn Abdul tace" dan Allah a daina bata haka nan Mmn Siyama ki ga fa yadda take kuka.."
" Ki bari a hankali zata saba ne, ba'a biye ta yara Zaitun in ba ke bama har tsawon wani lokaci zaki dauka kina wannan hidima da celarac da madaran bacin ina da tabbaci ko cikin ki baki bashi kula yadda ya dace kwatankwacin yadda kike bawa yarinyar nan, dubi kanki fa Zaitun sittirar kirki baki sawa baki damu da duk wani farin ciki ko jin dadi naki na kanki ba, takalmi idan kika siya kika fara amfani dashi ke da canza sa har sai ya daina amfanuwa a kullun ke dai Mufeeda! Mufeeda!!..babu abinda Mufee ta rasa a yanzu, kema ki ringa yiwa kanki adalci dan Allah Zaitun".

Jikin Zaitun sanyi yayi sosai..tarasa meyasa a kullun Mmn Abdul ke gani kamar ta zurfafa a kaunar da take yiwa Mufee ne, bata san cewa ita din ita ce jigon farin cikin ta ba ne, baya ga hakama alkawari ta daukan ma kanta cewar zata zame mata Garkuwa, ta kula da ita gami da bata kariya ta ko wani irin fanni matukar hakan bazai sa ta sa6awa mahaliccin ta ba.

Kalaman Mmn Abdul sosai ya sanyatar mata da jiki, hakan yasa bata kara magana ba ta jure kawai aka cigaba da bawa Mufee kunun nan ahakan kuwa tun bata so har tazo ta saba da  shansa.

Watannin su shida a gidan fitinar Baban su Siyama ya ishe ta sosai, dan har kara ramewa tayi saboda damuwa, tuntuni ta fara tunanin barin gidan amma zuciyar ta ta kasa tsaida mata inda ya kamata bayan nan din, kuma ma takan tambayi kanta da wani kudin zata sake neman hayar, ko nan din ma albarkacin wancan kudin dake hannun ta ne kuma tuntuni da jimawa labarin su ya shude, 'dan wanda ake biyan ta wajen aiki kuma hidimar kanta da ta Mufee ba barin kudin yake sukai wani lokacin ba, dan ma ahakan Mufeeda kadai take siyawa abinci ita kam lissafin cin abincin ta a cikin kudin duk babu shi.

Da gari ya waye idan ta tashi ta dama kunun Mufee ta juye cikin 'yar teaflask din da Mmn Abdul ta bata shawaran siya ta kuma bata shawaran siyan karamin kettle tunda ba girki take yi ba duk wani hidimar ta ta ruwan zafi ce.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now