P61

82 7 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
*Serlmerh-md*

🅿️ *...61*

               ........" Ina Marwa ta shiga ne? Marwa!..Marwa!!..."
     Ammi ke cigiyar ta tana 'yan dube- dube amma bata ganta ba.
        Bayan kamar mintina biyu sai ga Zaitoon ta hawo saman nata da sallama a bakin ta hannun ta 'dauke da wani kyakkyawan bowl da spoon bata dire shi ko'ina ba sai gaban Ammi.
            Sai da ta dai- dai ta zaman glass bowl 'din da kyau sannan ta koma gefe ta zauna daga gefen kujerar Ammi fuskar ta babu yabo babu fallasa.
             Ammi ma gyara zaman ta tayi gami da 'dago bowl din a hannun ta tana fa'din" banga Marwa ba hala itama tama can kitchen 'din ne ko..?"

" A a Ammi inaga dai 'dakin ta take fa.."
" Ok...wai da so nake taje ta duba min Amrah ya tashi, amma bari dai ta shigo tukunna...".

" Ko dai in 'kira ta ne kawai Ammi..?"
" a a barta zata shigo ai..."

Shiru ne ya 'dan ratsa wajen na 'yan wasu da'ki'kai...kowa sakar zuci yake amma daban, Ammi tunanin Amrah take da yanayin girman cikin ta sosai take tausaya mata, yayin da Zaitoon kewar Mufeeda ke nu'ku'rkusar ta.

A hankali Zaitoon ta 'dago tana duban gefen Ammi bakin har na 'dan rawa tace.." Amma Ammi yau in an tashi su Mufeeda gida za'a kawo ta ko...?"

'Yar murmushi Ammi tayi tana tauna fruits din bakin ta a hankali, sai da ta gama taunawa kafin tace..." Ha'kurin Zaitoon ya 'kare kenan...?"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, yayin da Ammi ta cigaba da fa'din.." Nima nan bansani ba wannan hukunci duk na Rayyan ne, amma may be ya dawo da ita yau 'din jiyan ma ai kinji yace ayyukane sukai masa yawa shiyasa kawai ya barta acan ya koma office.  "
" Hakane Ammi...Allah ya taimaka ya bada sa'a..."
" Ameen Ameen...ai naga ma kinyi 'ko'kari fa, tun jiya an yini an kuma kwana ana sake shirin wani yinin batare da kuma Mufeeda ba ai dole a jinjina miki...."
Ammi ta fa'da tana 'yar dariyar zolaya...dayake dama ta saba jan mutane ajiki, bata da girman kai sam Ammi, da kowa ma zata zauna tasha hira abinta in taso tsokanar ka ma duk yi zatayi.

Itama Zaitun murmushi tayi kana tayi 'kasa da kanta.

" Zaitoon kenan tsananin son da kike wa yarinyar nan ya zarta kowa a zuciyar ki da alama fa..?"

Murmushin ta kawai ne ya 'kara fa'da'da wanda kai tsaye ta aika shi ga Ammin cikin bayyana amsar tambayar ta yayin da Ammi ta cigaba da fa'din" na jima da fahimtar haka na kuma kasa ganewa, ko ince kin kasa sanar da ni sahihin labarin ki har yau balle in tabbatar da abinda zuciya ta ke raya min, amma tunani na yafi tsayawa akan cewa rasuwa mahaifin ta yayi shiyasa kk ninka 'kaunar da kike yi masa akan ta ko?

Kai ta girgizawa Ammin ba tare da ta dube ta ba...da alamun a a.
" Duk da yake ba yau na fara tambayar ki ko nuna miki manufata ba ta son sanin ainihin labarin ki ba amma bazan gaji da tambayar ki ba har gobe har kullum ma har sai zuwa lokacin da zanyi dacen samun amsar 'daya daga cikin tambayoyi na, Allah ya sani ban ta6a nufin ki da sharri ba balle diyarki zama nake da ke da zuciya ta daya, amma na lura ke har yanzu kin kasa fahimtar hakan balle ki iya bambance wanda ya dace da wanda bai dace yasan wace ke ba, duk da hakan zan baki shawara ko dan gaba, ba wai nufina in miki titsiye ba Zaitoon ba kuma dan zan iya tilasta ki ba, but matakin 'kaunar da kk nunawa Mufeedah ya kai matsayin da dole ne adasa ayar tambaya akai, na haifa Zaitun 'yan uwana sun haifa, 'ya 'yan ciki na sun haifa 'kawaye na, ma'kwabtana da kuma sauran mutane, amma ban ta6a ganin zahirin 'kauna da sha'kuwa kamar yanda na fuskanta game da ke da Mufeeda ba, hakan yasa bazan iya ha'kurin ri'ke wannan a zuciya ta ba domin ba tun yau na shiga tsananin kokonta da tunanin sanadin hakan ba, abaya hasashe na yana bani ne akan cewa..mahaifin Mufeedah mutuwa yy ya barki da ita shiyasa kk ha'da 'kaunar da kk yiwa mahaifin ta da nata duk kk nin ka mata su..amma kin ce ba haka ba ne, ni kaina wani sa'in kuma na kanga kamar ba hakan ka'dai ne zai saki yiwa Mufeeda irin wannan 'kauna da sadaukarwar ba..shin Zaitun bakya tunanin akwai mutuwa da zata iya raba ku watarana ne? Bakya tunanin akwai wata kaddarar ta daban da zata iya raba ki da ita..?
ban miki fata Zaitun amma kiyi tunanin irin halin da 'dayan ku zai iya shiga idan mutuwa ta gitta tsakanin ku..."
" Kuka sosai Zaitun ta fashe da shi a fili ta furta " " Ammi...!"
Sai kuma tayi shiru illa kukan daya ci 'karfin ta, ji tayi gaba daya zuciyar ta ta cunkushe.
" Idan na 6ata miki kiyi hakuri, but u need to no this bcuz ke yarinya ce 'karama, baki san me duniya take ciki ba baki san manyan 'kalubale da ke cikin rayuwa ba, matukar kika kasamce uwa dole ne ki koyi hakuri, juriya kawar da kai da kuma natsuwa...akoda yaushe ki rika ji aranki cewar wanda ya baki 'da ko 'yar zai iya raba ku duk lokacin da yaso, kuma ba lallai ne dama ku taso atare ba, baki duba marayun yaran da iyayen su ke barin su tun basu san kansu ba amma cikin ikon sa sai kiga sun taso cikin kulawa da gatan da ko iyaten su albarka, har kullum kisa aranki cewar dake ko ba ke dole ne watarana Mufeeda zata yi kuka, zata yi rashin lafiya, zata rayu inda babu ke tunda dole ne ki kaita makaranta, karshe dole ne 'dayan ku zai iya mutuwa ya bar 'daya a lokacin ya zaki ji bayan kin gama sawa aranki cewar kina tare da ita, kin manta cewar mutuwa zata iya giftawa ko kuma itama kin gama dasa mata hakan aranta ki 'kiyasta kiji yadda zaku tsinta zu'katan ku..."
Kuka sosai take da hawaye
"...Wallahi Ammi ban ta6a mantawa da mutuwa ba, taya ma zan iya mancewa da ita? ta yaya? mutuwar ce fa Ammi, mutuwar ce sanadin komai...."
Ta fa'da ne tana me 'kara sakin kuka tare da du'kar da kanta ga dukkan alamu abubuwa take tunawa, abubuwa masu zafi masu tsayawa a zuciya.."
Kai Ammi ta girgiza cike da alhini ta ce" na sani, dama nasan bazai wuce hakan ba Zaitun, da kaina na fahimci ciwo da zogin mutuwa ma'kare cikin zuciyar ki da yake saki zafafa abubuwa harma ya hana ki ganin wasu abubuwa ba'a daidai da yadda suke ba..sai dai yanayi da 6angaren mutuwar ne ban san daga wani kusurwa bane, duk da hakan zan ro'ke ki ki sassauta Zaitun ki sassautawa zuciyar ki abinda yake damun ta..ba ina nufin kar ki 'kaunaci 'diyar ki ba ne amma ki sassauta hakan kar watarana ya muku illah, mutuwa tana kan kowa kuma kowa zai 'dan'dane ta, kin ganni nan badan tawakkali da na sanyawa raina ba da yanzu ba wannan zancen ake mk ba Zaitun da sai dai abaki tarihina, domin ni.m naga mutuwa ganin idona, naga mutuwa daki daki da ba kowa Allah ke jarrabta da irin hakan ba amma dana fawwalawa Allah na mika masa kukana ba gashi yanzu nima ina rayuwa ta cikin farin ciki ba, ba abinda ya rage tsakanin mu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya illah addu'a.
ki sassautawa ranki kema ki kuma sassauta kaunar da kk yiwa yarinyar nan ki daina nuna ta a zahiri ba dan komai ba sai dan irin hakan, wani ma da wannan damar zai yi amfani ya cutar da dayan ku, yayin da wani haka siddan babu gaira babu dalili zai iya jin tsanar ki ko 'diyar kin cikin ransa, akwai masimu mu mgun baki, akwai masu kambun baka duk suna daga cikin mutane masu sharrin da a kullum muke neman tsari da su, sannan dole ne mu kiyaye faruwar wasu abubuwan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo".
...Kuka sosai Zaitun ta ke yi mai ta6a zuciya, hakika ita ka'dai tasan inda kukan ta ya dosa, ta fahimci babu wanda zai iya fahimtar asalin zuciyar ta ko inda rayuwar ta ta dosa sai ita kadai, kamar dai Ammi, ta fahimci tunanin ta daban ne..tunanin kukan mutuwa take yi na mahaifin Mufeeda ko wani abu daban..." Ammi ni kam mutuwa kyauta tai min, kyauta mafi soyuwa a zucia, domin mutuwa ta bani yarinya, ta kuma bani ita ne a gabar da ni kaina ban tsammaci hakan ba, hakika ina jin ciwon mutuwarm har cikin zuciya ta ina kuma godewa Allah kullum bisa kyautar Mufeedah da ya bani wanda hakan shi ya rinjayi komai a zuciya ta cikin duniyan nan...."

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now