P17

71 9 7
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...17*

             Jin canza salo da tambayar tasa tayi ne ya sanya Zaitun 'dago idanun ta ta dube shi suka hada idanu, saurin kawar da kanta tayi gefe...kawai sai taji zuciyar ta ta aminta da shi 'dari bisa bari, take damuwar ta fara rage nauyi a zuciyar ta, haka kawai sai take jin sa tamkar wani garkuwa ne a garesu baki 'daya.

Wani sabon hawaye ne ya 6alle mata na tausayin kansu, amma sai tai saurin share hawayen, a hankali ta bu'di baki tace" Ni ban san su ba...Hajiyar ce ta kaini gidan bayan mun baro asbiti a wancan lokacin, ita ta taimaka mana ba tare da  nasan su din wa'danne irin mutane bane, lokacin da nazo na farga da hakan na fara tunanin rabuwa da su a lokacin su kuma suka shirya raba ni da 'yata shiyasa na gudu, jiya na bar gidan da dare saboda in tseratar da yarinya ta garin hakan Allah ya hada mu da wadancan a bakin titi...yanzu bani da kowa bani da inda zanje, kawai zan tafi ne, ina so inyi nesa da su inda bazasu sake gani na ba".
Tana gama fadin hakan hawayen ta ya kara karfin kwaranya.
Bai ce mata komai ba illa kallon ta da ya tsaya yi sosai yaji ya tausayawa mata, domin shi yasan wace Hajiya Mardiyya, farin sani yai mata tun ba yau ba,  kusan mintina biyu yana tsaye a wajen kamar ba zai sake magana ba sai kuma can ya furta" Kafin ha'duwar ki da Hajiya Mardiyya...?"
Bata ma bari ya kai karshe ba tayi saurin tarar sa da fa'din..." Bara nake bamu da kowa kuma a haka muke rayuwar mu..."
Tayi saurin fadin haka ne gudun kar yace zai tambaye ta asalin garinta da kuma dangin ta balle yayi tunanin mayar da su...

Kallon sakanni Dr Rasheed yai mata sai kuma ya juya ya fita yana me ciro wayar sa dake aljihun sa.

Parlour ya koma yy kira wanda Zaitun sam ba fahimtar abinda yake fada take yi ba sai dai ko kadan hakan bai sa taji shakka ko tsoron kasancewar ta anan din ba.

Mahaifiyar sa ya 'kira yayi mata bayani bayani a takaice ta kuma fahimce shi dan macece mai saukin kai sam bata da matsala.
"…Ba komai Abbah..indai kaga hakan ba zai zama wata matsala ba kayi yanda ya dace kawai, Ni dama tunani na Hameeda ce kar taki amincewa.."
" erh dama zanyi magana da ita Hameedan tukunna.."
Ya fadi hakanne kuma saboda ya kwantarwa da mahifiyar tasa hankali amma ba wai dan ya damu da amincewar ita Hameedan ba.
"..Toh shikenan Ubangiji Allah ya 'kara rufa asiri..."
Da Ameen Ya amsa gami da ajiye wayar.
Tunani yayi na 'yan mintina sannan ya tashi kawai yayi waje.

Fitar sa da kusan mintina talatin kenan yanzu...Zaitun na zaune tana ta zuba ido, jira take taga ta inda shi kuma zai 6ullo da nasa lamarin amma shiru...tana so ta shiga bayi ma amma sam ta kasa tashi daga inda take zaunen.
Allah ya sota ma tana hutun sallah ne amma sosai take da bukatan rsaftace jikin ta.
Haka ta cigaba da zama ba wai dan bata san ta inda zata fara ba ko kuma bata fahimci inda bathroom din yake bane kawai dai fargabar abinda ke jiran ta agaba ne ya hanata tashin.

Shahada kawai tayi ta yunkura ta sauko cikin sa'a kuwa tana saukowa sai taga ledan kayan ta a kasan gadon wanda ta sako musu 'yan kayan su a ciki.
Hamdala ta saki cikin zuciyar ta gami da daukan ledan tana me gyara rikon Mufeeda da kyau.
Bathroom ta shiga da be wani yi mata wahalar ganewa ba, dan ta koyi wannan tun a asbiti da kuma gidan Hajjaju, duk da yake na nan din haduwar sa daban ne amma bai bata matsala ba.

Da yake taga Mufeeda Fes da ita so bata yi tunanin sake yi mata wanka ba tunda taga har sabuwar riga aka sanya mata da bata san takamamme wanda yayi hakan ba..sai dai tasan koma menene an yishi ne bisa umarnin Dr Rasheed.

Sai da ta tsaftace jikin ta ta canza Pad din da Na'eema ta koya mata amfani da shi, canza shiga tayi zuwa doguwar rigar abaya sannan suka fito..sai ma da idanun ta suka yi arba da yagaggiyar rigar ta kafin ta kare godewa mahalicci daya tseratar da ita ya kawo mata wannan mutumin, ko bakomai iya taimakon da yayi matan ba karamin tallafawa bace kuma yaci ace ta girmama shi..domin badan zuwan sa ba bata san iya abinda ze afku gareta ba, da kila ba wannan zancen ake yi ba yanzu.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now