P41

89 10 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...41*

    _Washe gari_

                 Tana cikin bathroom 'din Ammi tana wankewa, daga cikin bedroom 'din kuma Ammi ce ke waya da 'diyar ta Raihana yayin da Moopy ke gefe tana wasan ta tamkar ba ita ce ta kusa shekawa jiya ba.

" Erh baza dai su wuce this week ba, kinsan 'dan uwan naku sai a hankali...Rayyan ne ya matsa akan su dawo gida..".
       Da fitowar Zaitun abinda kunnuwan ta suka fara tsainkaya daga wayar Ammin kenan, kuma shi ta tsaya tunani har Ammi ta kammala wayar bata 'kara fahimtar komai da ta fa'di ba.

Tunani take toh su waye zasu dawo Allah yasa Marwa ce, dan wlh sosai tayi kewar ta, tayi kewar abokiyar hira, duk da yake wasu lokutan Marwa kalaman Marwa sai a hankali, takan iya furta kalma marar dadi sai ita a wajen ta bada wata manufa take hakan ba, fahimtar halayyarta da Zaitun ta yi yasa take yi mata uzuri, ba mamaki ta saba da hakan ne shiyasa.

Maganar Ammi ce ta dawo da ita"..Mutumiyar ki an kusa dawowa..dama kullum muka yi waya mita take wai ita ta gaji tana so ta dawo Sultan ya ki..".
Murmushin jindadi ne ya wadaci fuskar Zaitun.." Masha Allah....Allah ya dawo da su lafiya..".

A fahimtar ta ita kanta Ammi annurin fuskar ta yafi na kulluma ga dukkan alamu itama ba son zaman su can wata kasar take ba kawai ba yadda zata yi ne shiyasa.

            Koda ta gama aikin ta koma 'daki tunanin moments 'din su da Marwa ke 'dan zuwa mata, har mamakin kanta take yi, bata ta6a sanin tayi kewar Marwa har hakan ba sai yanzun.

           Akwai halittu da dama cikin zuciyar ta da take tsananin kewar su fin ma Marwa amma bata fiya bawa zuciyar ta isashshen damar tunowa da su ba.

Abu ne me sauki tayi ta zubda kwalla matukar tace zata bada 'kofar da kewar su zai shiga jikin ta, amma taya zata yi ta ta iya manta karamci irin na ma'kwabciyar Mmn Abdul, taya zata iya mancewa da Adam a rayuwar ta, taya zata iya mance rayuwar ta ta baya.

Hatta Hajja da sauran mutanen da suka munana mata ma bata iya mancewa da su balle wa'danda sukai mata halacci.

           Marwa kuwa abokiyar hirar ta ce kuma 'kaunar da take nuna wa 'diyar ta ya sanya ta bata babban matsayi.
              A hankali tunanin ta ya gangara ranar da Hajja Ladi ta bar gidan....
    
                 Maganar Sultan ne ta dawo da Hajja Ladi daga 'dan guntun tunanin da ta lula" Yanzu akan wannan 'yar yarinyar kk wannan hassadar Hajja Ladi...?"

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta, sai da ya sake maimaitawa da tsawa kafin ta ce" Ranka shi da'de dan Allah kayi min rai kayi ha'kuri nayi alkwari bazan sake ba wannan 'din ma kuskure ne.."
" Ri'ke al'kawarin ki Hajja, idan wannan ya zam kuskure sauran na baya fa..?"

Shiru tayi kanta na kallon 'kasa.
" Kice kin zama shai'dan kawai, salon na bar ki watarana muma ki sam6a'da mana magani mu fice mu bar miki gidan...?".
" Sultan miye haka...?"
" Jin muryar Ammi yasa Hajja Ladi maida hankalin ta ga Ammin da alamun ro'ko.
" Kalli nan...".
Sultan yace da nufin maido da hankalin ta gare shi.
" nima albishir zan miki yanzun nan..."
Nuno Zaitun yayi yace" kinga wannan da kk shirin koran ko..to ita zata maye gurbin ki, ke kuma daga yanzu 15mints bana so ki kara sakewa cikin gidan nan kije ki cewa bokan ki asirin ki yau ya tonu sultan ya kamaki..dan bazan iya barin ki zama tare da mu ba, in dai har zaki iya cutar da masu aikin da kuke tare to ko mutanen gidan ma basu tsira daga sharrin ki ba wa ya sani ma ko da ke aka ha'da baki...".
" Um um Sultan please..".
Ammi ta dakatar da maganar da yayi niyyan furtawa tana girgiza masa kai.

"...dan haka ki bar mana gida kawai yanzun nan, ko kuma in sa afasa min kwakwalwarki da harsashi...".
Da fa'din haka ya tashi yayi hanyar waje bai ko sake waigowa ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now