P84

103 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...84*

                   .......Ban iya na sake motsawa a wurin ba har akayi sallar isha'i sannan na tashi na kunna 'yar tocilar da Yaah Bukar ya siya min kwanaki ganin 'dakin nawa babu wadataccen haske...to ma gashi batirin duk yy sanyi..yau kuwa ban yini a gida ba balle na tuna na sa su arana su 'dan farfa'do.

A haka na lalla6a na gabatar da sallan ta hasken tocilar na kara sau'ka, 'karshe ma 'daukewa yayi gaba 'daya.

Idanu na lumshe ina ta sake maimaita karatun da ya yi min 'dazun dan kar in manta, a haka na gama dukkan addu'o'in da zan yi na shafa daga haka na hau kan gadon kwangwala ta da babu komai akai face wata 'yar tsohuwar tabarma.

Da hannu na nayi pillow idanu na tsam a wuri guda ina tunanin rayuwa ta gaba 'daya, kwata- kwata bana jin da'din zaman gidan namu a halin yanzu, domin bana samun walwala da sakewa yadda ya kamata, idan an ganni da fara'a cikin gidan nan toh ni da Ummaru me ko Yayana, amma ni da damun sakewa sai dai in bana cikin gidan amma matukar ina gida komai a takure nake yin sa, a hakan ma abin da 'dan sau'ki domin kwana biyu Iyami bata tura ni jeji ba.

Ajiyar zuciya na sau'ke tuno abinda ya faru da ni watanni 'kalilan baya da suka wuce.

Hannu na na kai cikin riga ta kan saman ciki na nake shafawa, bazan ta6a mantawa da 'dan karen wahalar da nasha ba a lokacin da naji ciwon nan..wannan ma Iyamj ce ta tura ni 'debo mata kara a jeji wai na hura wuta, ranar sai na taki sa'a Ummaru yace zai rakani, haka muka tafi muna 'yar hirar mu ni da shi sama...tare muka harha'da karan na 'daura ina shirin 'dagawa sama kafin na 'daga har na kai hannu kenan sai naji Ummaru ya kwalla min 'kara da iya 'karfin sa a lokaci guda kuma yake 'dan jan baya idanuwan sa warwaje yace" Yaah Zaituna maciji...maciji ki matsa..."
Yayi maganar yana mai yi min nuni da inda ya hango macijin.

Da sauri na saki karan na mi'ke tsaye ina mai kai dubana wajen da yake nuna min 'din... ido hudu nayi da macijin nima nan na tabbatar da gaske yake, take nayi baya jiki na na daukan rawa..hannun Ummaru na kama muka fara gudu gudu sosai tamkar ance min bayan mu macijin ke bi, ko ganin inda nake sanya 'kafata ban yi, bamu kuma bi ta kan karan da muka daura 'din ba.

Muna cikin gudun ne nayi tuntu6e da wani abu da ban san ko menene shi ba, ai kafin nayi wani yunkuri ko dabara tuni na fa'di da ciki na cikin rashin sa'a kuma sai na fa'di akan wani gurbin karan dawar da ake yanke amma ba'a gama cire shi gaba 'daya ba, kuma ta sai tin ciki na....

Sau 'daya nayi ihu mai cike da azaba daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bu'de ido nayi na ganni kwance a wani babban asbiti dake cikin garin Maiduguri, wanda kusan zan iya cewa wannan shine shiga na cikin garin na farko.

Ashe Ummaru ne yaje gida da gudu arikice ya sanar da su wai Zaituna ta mutu da jini a jini .."
Jin hakan yasa mutane suka yi saurin kawo min 'dauki nan aka tarar da ni sume na kuma zubda jini ba 'dan ka'dan ba.

Yaah Bukar shine ya 'dauki nawin komai da akayi min a asbitin har suka dawo gida, kama daga kudin jinya 'karin jini da akai min har zuwa 'dinkin da akai min a wurin nan 'kasan cibiya ta ka'dan, kafin ya warke kuwa ba 'karamin wuya na ci ba sbd rashin samun cikakken kulawa.

A wannan kwanciyar tawa ma sake tabbatar da cewa ni din marar galihu ce, mutun 'daya ke tausayi na kuma shine ke min dukkan 'dawainiya sai 'kawa ta Dije da muke kusan yini tare da ita.

A lokacin na sake tabbatar da cewa babu 'kauna ta ciki kuwa hadda mahaifiya ta.

Domin har nayi ciwon na gama na cigaba da harkoki na ko da sau 'daya mahaifiya ta bata ta6a shigowa gidan mu da sunan duba ni ba...sosai abin ya bani  haushi amma bani da matakin 'dauka...domin bani da ikon yin komai face illar da hakan ke sake yi min a zucia ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon