P20

69 5 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...20*
 
           Yana gama fa'din hakan yy gaba abin sa batare da sake jiran wata kalma tata ba, da kallo kawai Hameeda ta bishi cike da tsananin mamakin sa..." is this real...?"
Ta tambayi zuciyar ta.
Dr Rasheed ne ke mata irin wannan surutan akanta..me kenan hkn ke nufi?..kenan...kenan laifi ne dan ta nuna bazata iya zama da yarinyar ba?
Kasa ko 'daga kafafun ta tayi a wajen tana jin wata karaya na tsirga mata cikin dukkan ga6o6in ta.
Ji take tamkar ta sanya hannu aka tayi ihu ko zata ji saukin zuciyar ta.
Gaba 'daya ji tayi ya 'karawa zuciyar ta zafi..sosai taji tsanar Zaitoon har can kasan zuciyar ta fiye ma da farko, akanta ne Rasheed ke buga mata irin wannan tsawar da rabon da ta ji yamata irin sa baza ma ta iya tunawa ba?

Da gudu ta koma dakin ta hawaye na zuba mata babu kakkautawa.
Waya ta lalu6o ta dannawa mahaifiyar sa kira nan ta zayyano mata komai har ma da kari, ga mamakin ta hakuri kawai ta bata tare da kalaman da zasu kwantar mata da hnkl.
Inda ta kara da fadin in kuma taga zuciyar ta bazai kwanta da zaman yarinyar acan ba zatai masa magana ya kawo ta nan wajen ta.
Godiya kawai Hameeda tayi mata ta kashe wayar, tana nufin itama tasan da batun kenan? Kenan kalaman ta ta fahimci tamkar lbrn ba sabo yk agare ba, baki suka hada ko kuma mene...tun yaushe Rasheed ya shirya wannan lamarin bata da masaniya.
In kuwa har mahaifiyar sa ma tasan da batun dole itama ta nuna nata ikon in ba hk ba zasu kaita kasa.
Dole akwai wani boyayyen abu da ita bata sanshi ba..zata bincika za kuma ta 'dauki mataki.
Ta jima tana tunanin yadda abubuwan zasu iya wakana, ita zama da yarinyar tare da su din bata bukatar sa sam sam kuma shi tafi tsana sannan abinda zai iya biyo bayan zaman, ko da tace akai ta can gidan ta din ma Hameeda sai taji bata aminta da hakan ba, da aje can ana hada kullin da bata sani ba gwamma ayi agaban idanun ta yafi, koba komai zata san shirin su.
Kai anya ba baki aka jada za'a mata sakiyar da ba ruwa ba..tunanin ta ya kasa tsayawa waje guda.
     Wannan yarinyar in ta wanku ai ko bakin farcen ta ba ta isa ta kama a kyauba, in kuwa akace yau ta zama kishiyar ta ta gama kadewa har ganyen ta.

Kuma in dai bb wata akasa me yasa shi aminta da ita  yarinyar har da kawo ta gidan sa.
me yasa Rasheed dagewa akan ta, shi da ko 'yan aiki bai yadda da ko guda cikin gidan sa ba, duk girman gidan ita kadai ke kula da abinta..ita kadai ke shawagi cikin sa sai 'ya'yan ta, sai kuma me sharar haraban gidan sai duk bayan kwana biyu shima yake zuwa yayi sharan sa ya kama gaban sa..gateman kadai ne yk nan.

Karshe dai dole ta yanke shawarar zaman Zaitun din tare da su a gidan taga gudun ruwan su kafin kuma ta 'dau nata matakin.

Dr Rasheed bai sake bi takan Hameeda ba har ya gama shirin office ya fice abinsa shi da Wildan ya ajiye sa a schl.
Shi kansa yana mamakin kansa, dan bai san dalilin da ya sa yake jin yarinyar ba, yake kuma son su zauna tare da shi, yana ganin dukkan motsin ta, ya san dai tun washe garin ranar da ya taimaka mata yk jin zuciyar sa nayi masa nauyi game da ita ya kuma ji baya son tai masa nisa..amma bai ta6a zaton zai iya tsawatar wa Hameeda akan ta har hakan ba.
Idanu ya lumshe gami da shafo kansa da kansa yasan bai kyauta mata ba amma baiga laifin sa wani cancan ba, batun yau yasan Hameeda da tsananin kishi ba, sarai yasan ta, sai dai abu guda da take birge shi kokadan bata da mummunan zargi akansa sai wanda ta gani da idanun ta, shiyasa duk irin zirga zirgar da yake yi bata ta6a tanka masa ko nuna zargi kan hakan ba.
      Kuma sarai yasan ta fisa gaskia akan Zaitun, amma ba yanzu ya shirya barin ta tafiya ba, bai ma yi niyyan kawo ta ba bayaga gudun kar Hajiya ta gano ba'a gidan take ba ta dasa masa wata ayar tambayar da yake tun farko ya riga ya sanar da ita batun Zaitunar.
Kuma jiya kannen sa sun ce masa zasu zo gidan nashi yini kwanan nan...shiyasa ya kawo ta.

Ranar Zaitun taga rayuwa, tun safe bata sake jin motsin kowa ba balle idanun ta suga abinci tun na karyawa da aka basu, damuwar ta ma Mufeedah ce bata ta kanta, da rana ma ragowar bread din su na safe tai ta hankara mata ta kuma yi bacci gashi har yamma babu motsin kowa ita kuma tsoron fita take dan ta lura matar gidan bata yi na'am da su ba tun ganin yanayin fuskar ta safe.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now