P30

71 14 4
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...30*

           .........Ido ta waro sosai ganin irin girma da kyan gidan da suka shigo bayan an bude gate din gidan, sosai jikin ta ya fara rawa saboda tsoro, sake rungume Mufee tayi tana me dawo da kallon ta ga Hajiyar da ke zaune gefen ta, magana take son yi amma yadda bugun zuciyar ta ya rinjayi duk wani 'kwarin gwiwa da take ikirarin tana da shi haka ya rinjayi harshen ta ma yayi mata nawi.

Dagaske tsoro da fargaba ya tsarga mata nan take, tuni ta raina kanta ta jinjinawa rashin wayo irin nata, sai lokacin ta fara nadamar yadda da tayi ta biyo matar nan.
            Tsayawar motar yayi dai dai da tsayuwar wasu mutane har guda biyu sanye da kayan da take kyautata zaton na aiki ne..." Alhamdulillah"!
Hajiyar ta furta a fili gami da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu bata tare da wata damuwa sa6anin Zaitun da ta raku6e ta kasa ko da motsin kirki.

        Wa'dannan da suka zo tar6ar Hajiyan ne suka bu'de motar batare da 6ata lokaci ba matar nan ta fara kokarin sanya 'kafafun ta waje.

Ganin haka yasa Zaitun tai saurin ri'ke mata hannu idanun ta da kullum suke nan ruwa- ruwa ta 'daga ta dube ta da shi wanda take wasu sabbin hawayen suka taru cikin idanun ta.

Kai ta fara girgizawa batare da ta saki hannun matar ba yayin da 'daya hannun ta ke rike dam da Mufeeda tamkar za'a 'kwace ta.
"...Dan Allah Hajiya ki sa a maida mu inda aka 'dauko mu, wlh tsoro nake ji sosai...".
murmushi tayi tana duban hannun ta da Zaitun ta ri'ke sannan ta dubi fuskar ta " Karki damu daughter, kar kuma kiji tsoro nan gida na ne...sauko mu shiga ina sauri ne....".

Hawayen Zaitun tuni ya gangaro, sau 'daya ta dubi matar sai ta mayar da duban ta ga sauran matasa dake tsaye wajen motar..ita dai haka kawai sai taji hankalin ta bai kwanta da gidan nan ba.

Bu'de mata 6angaren da take akayi bata zaci hakan ba dan haka da sauri ta dubi wajen ganin wani ne sanye da bakaken kaya kamar sauran ya bude ya sa da sauri badan ta so ba ta bi bayan matar ta inda ta fita, dan ji take tamkar zasu kamata bata manta farkon haduwar ta da Dr Rasheed ba, haka ta gansu duk sanye da bakaken kaya.

Da gudu- gudu sauri- sauri ta fara bin bayan ta har yanzun kuma hawayen ta bai daina sauka ba..." Easy madam.. kar ki fa'di..".
Taji an fa'da daga bayan ta, hakan sai ya 'kara mata sauri, matar nan murmushi kawai tayi batare da ta sake duban Zaitun ba, bata damu bane dan tasan tana nan biye da bayan ta har suka ratso cikin tsakiyar 'dakin da duba 'daya Zaitun tai masa ta fahimci Palor ne irin ma wanda ya amsa sunan san nan.

A iya yawon da ta yi ta san faluka iri- daban daban sai dai wannan 'din yasha bambam da kowanne, girma da tsarin sa na musamman ne, wani ni'imtaccen 'kamshi yake fiddawa da duk yadda kake jin zuciyar ka da ka ratsa palon nan sai kaji 'yar nutsuwa ta shige ka.

Wata mata ce ta shigo tsab da ita sai dai, rissina tayi fuskar ta cike da fara'a take fa'din "..Barka da dawowa Ammi...an iso lafiya...?"

" Lapia 'kalau Alhamdulillah Raleeya ina Hajja Ladi fa...?"
" Tana kitchen".
"  Kice ta same ni dan Allah..."
Hajiya tayi maganar tana me hawa saman stairs tare da bawa Zaitun umarnin samun wajen zama.

Ita har wacce aka 'kira da suna Raleeyan bb wanda yayi ma 'dan uwan sa duba sau biyu.
Zaitun banda bin parlon da kallo da tunanin makomar ta bb abinda take yi.
Lokaci lokaci takan gyara rikon da ta yiwa Mufeeda da har yanzu ke bacci tamkar wacce wani abu ke tsikarin ta haka take yawan gyarata.

Sau 'daya tak in ka kalle ta zaka fahimci cewa a matukar tsorace take.
Haka kuma ta kasa bin umarnin matar na cewa da tayi ta zauna.

Ta ina zata iya zama a wannan wajen, ta zauna ma tayi me..?
Tana nan tsaye kallo mai kyau bata iya bin parlorn da shi ba sbd wasi wasin da zuciyar ta ke ciki... 

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now