P7

89 9 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
      *(' Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...7*

      ....Sai da ta koma daki sai taji kuka ya kufce mata, kukan da ita kanta bata san dalilin yin sa ba, sai kuma taji nawin da zuciyar ta yayi mata ya dan sauka, bayan wani dan lokaci da ta nutsu sannan sai ta ji kamar kuma bata yiwa Mmn Abdul adalci ba, baiwar Allahn bata san wace ita ba amma ta kar6e ta hakanan, bata san daga inda ta fito bata san meke 6oye cikin rayuwar ta ba amma a hakan ta nuna mata kauna ita da 'yar ta, tai musu halacci ta bada gudunmmawa cikin rayuwar su gwargwadon iyawar ta, bata ta6a kyarar su ba bata ta6a kyamatar su ba iya zaman su, meyasa kuma ita bazata bude mata zuciyar ta ba.

A daren ranar ta yanke shawaran washe gari zata bawa Mmn Abdul amsan tambayar da tai mata game da tarihin rayuwar ta, sai dai kuma kaf din daren kasa tsaida hawayen ta tayi haka ta kwana kuka bacci ma kauracewa idanun ta yayi, Mufeeda na kwance kan cikin ta tana shafa bayan ta duk wani motsin yarinyar tana lura da shi.

Abubuwa ne masu yawa suke yawo cikin zuciyar ta da ta jima tana danne su, ba karamin kokari tayi ba iya tsawon lokacin nan tana hana kanta tuno su, karfi da yaji ta hana kanta samun lokacin da zata ware domin tunawa da su.
Amma a yau hakan ya gagare ta, yau din ji take tamkar zuciyar ta zata fashe ne, sosai take jin kewa, tana jin dana sani na son taso mata, zafi take ji cikin kirjin ta sosai...zafi na rashin madafa rashin sanin tudun dafawa.

Washegari cikin rashin sa'a sai ta tashi da zazzafan zazza6in da take kyautata zaton matsantawa kanta da tayi da tunani ne ya haifar da shi.

Da kyar ta lalla6a ta yi wanka ta yiwa Mufee ma, Tea ta hada musu suka sha da guntun bread din da Adam ya kawo musu tun shekaran jiya da yazo, wanda a jiya da safe wata 'yar tafiya ta kama shi da take kyautata zaton har a yanzu ma bai dawo ba.

Kayan Mufeeda set biyu da suka yi datti tayi zaman wankewa su cike da karfin hali, dan gabobin ta duk ba karfi take jin su, hatta hannun ta ma ji take nan da wani dan lokaci tamkar bazasu iya amfanuwa ba saboda zafin zazza6in.

So take tayi ta kammala ta lalla6a wajen Mmn Abdul ta bata hakurin abinda tai mata jiya...dan tasan dole ne zata ji babu dadi.

_"...Salam Alaikum..."!_
Tajiyo tashin sallamar da tun ma kafin me rero sallamar ta bayyana Zaitun ta fahimci wace ita.

Amsa sallamar tayi tana mai kakalo murmushi ta dorawa fuskar ta na karfin hali.
"...Yau Anty Rauda ce da sassafe haka..."
"...ai dai ba yawon bariki naje ba balle ace na aikata ba daidai ba.."
Ta fada tana wani yatsina cike da kallon raini take watsawa Zaitun da ke Zaune  har yanzun bakin kofar ta.

Sanye take da dan Hijab din ta da ta riga ta sabawa kanta dashi matukar zata fito harabar gidan.
"...Barka da zuwa Anty Rauda fatan an iso lpy..."
Ta sake fada duk da tasan cewa abu ne mai wahala ta samu kyakykyawar amsa daga Raudan..ga mamakin ta kuwa hakan ne.
" Da ba lafiyar ba ai baza'a ganni gidan 'yar uwa ta ba a wannan lokacin...kuma zikau aka ganni babu 'yar jagora balle tukuicin bariki..."

Wannan karon kam Zaitun bata sake tanka ta ba dan batun yau ba in da sabo yaci ace ta saba da halayyar Raudan da a kullun indai tazo gidan sai ta yada mata magana makamancin wannan, wani bin sosai take mamakin Raudan, yadda take daukan zafi akan Zaitunan kai kace akwai wata mummunar gaba da ya ta6a hada su, amma ba komai ne ya kawo hakan ba face zaman Mufee tare da su Siyama da suka kasance  'ya'yan yar ta kasantuwar ita din kanwa ce ga Mmn Abdul uwa daya uba daya sai dai akwai banbancin halayya karara.

Tun da jimawa farkon zuwan Zaitun gidan da Rauda tazo Hajja ta fesa mata karya da gaskiya shikenan tun daga ranar ta dauki karan tsana ta dora musu.
Mmn Abdul ke taka mata birki wani bin dan matukar taji ko ganin Raudan tayi mata ba dai dai ba takan tsawatar mata..wana Zaitun din ke kyautata zaton ko na yau din ma da ace taji bazata ta6a yin shiru ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now