P40

73 5 3
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...40*

              .......A rikice ta shigo gidan tana nufan babban part 'din dake gaban ta...bata zame ko'ina ba sai saman Ammi dan ba ai mata shamaki da ko'ina na gidan ba musamman 6angaren Ammin da ya kasance nan ne wajen aikin ta.   
"...Ammi, Ammi...kalli jikin Mufeeda."
Ammi da ke zaune a parlourn saman nesa kadan da ita Rayyan me suna kan tattauna batun dadoear Sultan gida kawai suka tsinkayi muryar Zaitun da yau ko sallama bata tuna yi ba.
Ba'karamin tashi hankali Ammi yayi ba ganin tahowar Zaitun a hakan da ko ba'a fa'da ba tasan ba lafiya ba, tun kan ta 'karasu tasan cike da tashin hankali ta tunkaro ta.
Tsam Ammi tayi ta zubawa inda tasan Zaitun 'din zata 6ullo idanu tama kasa ta6uka komai jira kawai take taji meke faruwa da fatan Allah yasa ba wani abun bane babba, amma 'kasan ranta take jin kamar ba 'karamin abu ne fa zai tayar da hankalin Zaitun har haka ba.
" Ammi, dan Allah ki taimake ni Ammi dubi jikin Moopy abinda yayi, Ammi dan Allah kice kar ta mutu ta barni wallahi ina son ta..."
Abinda take cewa kenan tana zubda 'kwalla ta zube gaban Ammi.
Sai lokacin ta saki asalin kuka tana kifa kanta saman cinyoyin ta gaba 'daya nutauwar ta tafi.

Da mamaki ya 'dago ya kalle ta, take kuma ya sake kawar da kansa yana tsakin tsaki kasa kasa, haushin tsayar musu tattaunar da suke nema yafi cika shi..'karshe wayar sa ya ciro ya fara danne dannen da shi ka'dai ya san meke yake yi cikin wayar.

Ammi zubawa Moooy idanu tayi bayan ta kar6e ta tana tambayar Zaitun abinda ya same ta, sai dai ganin yadda jikin yarinyar yayi yasa mamaki cika ta banda zafi da jikin ya 'dauka...
Cikin kuka Zaitun ta fara yi mata bayanin "
Wallahi Ammi ban san komai ba, muna cikin magana da Dada ( haka ake cewa tsohuwar) kawai naga jikin ta ya koma haka ga shi ya 'dauki zafi, kuma fa Ammi ko iya tsaida idanun ta ta kalle ni bata yi 'karshe ma idanun rufewa sukai"...
Ta 'karashe da sakin kuka sosai mai ta6a zuciya, gani take tamkar yarinyar ta mutu ne Ammi ke 6oye mata.

Ammi rasa ma abin fa'da tayi har yanzun duban jikin yarinyar take, sosai yanayin abun yai mata kama da na yaranta, wanda tasha fama abaya kuma har a yanzun basu daina samun irin wannan attack 'din ba, sai dai da yake sun manyanta sukan kiyaye shiga inda suka san zai dame su balle irin hakan ya faru da su..tuno wani abu yasa ta 'dan so ta sa a fahimci abinda ke faruwa..zazza6i ne ya shige ta mai 'karfi Zaitun dole sai an kaita clinic, amma gidan Dada har yanzu akwai mage ne dama..?"
" Erh akwai naga wata 'yar fara fara haka ajikin Dadan".
Zaitun ta bata amsa tana mai jin haushin shigo da wannan tambayar bacin ga damuwar da yake gaban ta.

Ammi bata sake fa'din komai ba illah mamakin samun me irin jinin yaran ta a dunia da take....
"...Toh ya isa, daina kukan haka nan bari a kaita  hospital ko...".

Ga Rayyan ta maida duban ta tana fa'din" Rayyan abin mamaki, kalli yarinyar nan, she is also allergic to...".
Bai bar Ammin.ta 'karasar bama ya tare da fa'din" Kai Ammi..da ganin abu, kika san ko 'kazanta ce ta kawo mata hakan..".
Yayi maganar yana maida wayar sa aljihu dan tun farkon maganar ta su bai sanya musu baki ba sai yanzun da Ammi ta gayyato shi.
Hararar sa Ammin tayi tana gayara zaman yarinyar da kyau a jikin ta.

A fakaice ya saci kallon Zaitun ganin turereniyar da hawayen ta ke yi...shi kam sosai yake jinjina irin wannan soyayyar, bai ta6a ganin irin wannan 'kaunar ba, shin hauka ne ma ko kuwa dai 'kaunar ce dagaske? sai kace akan ta aka fara haihuwa..to in mutuwa tazo ta isa hana yarinyar tafiya ne...?

Kya6e baki yayi yana kawar da kansa.
" Rayyan akwai abinda za'a iya mata a gida ne ko sai an kaita hospital? her condition is as exactly as you people more especially Raihana, Safaa nd u Rayyan... tun kuna yara haka jikin ku ke yi sak matukar kuka kusanci mage kuma har girman ku...i wonder why itama takeyin irin naku..?"
Ta 'karashe tana duban Rayyan fuskar ta cike da tsantsan mamaki.

Cike da haushin wannan dogon sharhi na Ammi yace"  Toh Ammi duk mu ba halittun Allah bane? shi ya haliccemu ya kuma raba mu jinsi- jinsi, ya raba mu kala daban daban, ya bamu kamanni mabanbanta, haka ya raba mu wasu lafiyayyu wasu masu 'karancin lafiya, wasu masu hankali wasu akasin hakan, duk tsananin yanayin da kake ciki dole a wani wajen daban inma kusa da kai ne ko kuma nesa da kai dole sai ka samu me yanayi makamancin naka, bazaka ta6a cewa kai ka'dai ke fama da abu kaza duk duniya ba dole akwai irin ka a wani wajen..kar kiyi mamaki Ammu, buwayar Ubangiji ta wuce misali...".
Kai Ammi ta jinjina tana sakin.ajiyar zuciya tace
" Hakane Rayyan, Ubangiji Allah yasa mu dace da Rahamar sa ya bamu dacewa duniya da Lahira".
" Ya amsa da " Ameen".
Yayin da Zaitun ke share 'kwalla kawai, tuni ta daina sheshshekan kukan amma hawayen ta ya kasa tsayawa.

Yasan ba son ta bane ace shi yakai yarinyar asbiti, bazata ta6a son hakan ba,  amma ko dan sbd ya sake 'kona ranta sai ya mi'ke, rigar sa ya gyara sannan ya sa hannu ya karbi yarinyar daga hannun Ammi.

Zaitun kam kafewa tayi wuri guda ta zuba masa idanu, ji take kamar tace ya bata 'diyar ta dan tasan halin muguntar sa amma sai ta kasa furta komai illa 'kure shi da kallo da tayi.
Tana son 'diyar ta ta samu lafiya amma me yasa sai shi.
Gira Rayyan ya 'daga mata alamar.
" Ya dai"...murmushin mugunta can 6oye saman fuskar sa.

Bai jira jin abinda zata ce da shi hatta Ammin kawai yy waje rungume da yarinyar, tsabar yadda ta kasa kunnuwa hatta takun steps da yake tamkar a tsakar kanta yake yi, har ya sau'ka 'kasa ne ta daina jiyo takun sawayen sa...tanajin tamkar zai dawo yace ta tashi su tafi amma shiru..har bayan wasu mintina babu shi babu alamun sa.
Ammin kam da ke ta jimamin lamarin shiru tayi tana nazari.

Haushin bai ce suje tare ba ya sanya ta tashi ta sauka da gudu ta koma 'dakin ta, a hanya ta ha'du da sabuwar mai aikin Ammin tana tambayar lafiya ko kula ta ma batai ba tayi wucewar ta 'daki ta saki wani sabon kuka zuciyar ta a hargitse...dan sam bata ji zuciyar ta ta nutsu da fitar ta su ba.

Shi kam dama ba wani hospital da zai kaita, yana da ragowar maganin da yashafa kwanaki da yake shima bai jima da samun attack 'din ba, kawai 'kin bayyana hakan yayi ga Ammi.
Kuma attack 'din na sa ma ba kowa ya sani ba sai Amrah ka'dai.
Daf da zai shiga 6angaren sa ya dubi fuskar yarinyar.
Murmushi yy 'kasan zuciyar sa yace..." 'yar gold, 'yar gatan Maman ta...yau dai gaki a hannu na ni 'din da dai ake gudu na...".

Ko da ya shafa mata maganin, wani 'daki ya kaita gefe bedroom 'dinsa ya kwantar da ita.

Alluran bacci yayi mata wanda zai sa ta baccin awanni biyu zuwa uku ya gyara mata kwanciya ya kashe A'c ya koma bedroom 'din sa.

Lokaci- lokaci ya kan shiga ya duba ta, Bai tashi kai yarinyar ba har aka yi azahar har kusan la'asar da yayi shirin fita sannan ya mi'ka ta, ranar ma Amrah taje bikin wata friend 'din ta.
Shi kuma yau hutu yake dama baije aiki ba.

Lokacin da ya kai yarinyar tuni Zaitun tayi laushi, idanun ta ko bu'duwa da kyau ba sayi tsabar kuka.
Ammi ma tayi ta 'kiran wayoyin sa duk akashe shiyasa hankalin Zaitun ya tashi sosai.

A palorn 'kasa yaci karo da ita, ta zubawa kofa idanu da alamu dawowar su take tsumayi, bai yi mamaki ba da ganin yadda Zaitun duk ta firgice yini guda kacal amma har 'yar rama tayi, ji yayi daria na shirin 'kwace masa." _firituwa kenan_ ".

Ya ma san da 'kyar ne yau idan anci abinci sbd ba'aga 'yar gold ba...
Da ganin sa ta mi'ke tsaye amma sai yayi tamkar bai ganta ba.
Direct saman Ammi ya wuce, da sassarfa Zaitun ta mara musu baya.

Da sallama ya shiga ya yiwa Ammi barka gida sannan mi'ka mata yarinyar yana fa'din" gata Ammi kurajen duk sun koma, zafin jikin ma ya sau'ka, za ta dawo to her normal condition da zarar ta farka...".
" Amma ya akayi wayoyin ka duk basa tafiya Rayyan..? Yini nayi ina 'kiran numbers din ka duk akashe".
Tayi maganar tana duban fuskar sa while tana gyara ri'kon yarinyar.

" Ammi mota na mance su gaba 'daya..".
"..and they ar all switchoff a motar ko..?"
Murmushi yayi tuno karyar sa bata hau kan seti ba dayake ba saba yin ta yai ba.
Yana shafa kansa yace..
" i'm sorry mum...zan 'dan fita gari..."
" Adawo lafiya..ka kyauta ai.."

_Salmerh_ 😘

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now