P82

102 8 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...82*

               ......" Asalin suna na shine Zaitoon Ahmad Kyari, 'yar asalin jahar Borno ce ni cikin 'kabilar Barebari, mahaifi na kanuri ne na asali dake zaune a wani 'kauye ne dake 'kar'kashin wata 'karamar hukuma acan jahar ta Borno, yayin da mahaifiya ta ta kasance bafulatana ce usul sai dai bazan iya fa'din asalin 'yar wani yanki bace ita.

Tun tasowa ta na budi ido da ganin mata biyu a gidan mu wato matan mahaifi na, Iyami itace babba sai mahaifiya ta da ta kasance biyu.

Mu biyar ne a wajen mahaifin mu, Yah Bukar shine babba sai mai bi masa Yaagana ( Zahra) sai Muhammad ( Goni) sai ni Zaitoon, autar mu itace Khausar..Duk 'yan uwana guda hu'dun nan sun kasance 'ya'yan da Iyami ta haifa ne, ni kuwa tilo mahaifiya ta ta haife ni a gidan daka kaina Allah bai sake bata wani haihuwar ba.

Yah Bukar yana da mata 'daya mai Azeema da yaran sa biyu Ummaru da Haneefa ( Aisha)..sai Yaaganan mu dake aure a nan cikin garin itama tana da yaran ta uku.

Duk da yake ni kadaice gaban mahaifiya ta amma hakan bai sa na taso cikin kula da gata yadda ya dace ba sakamakon tsangwama, rashin sukuni da kwanciyar hankali da Innata ke fuskan ta a gidan har nima ya shafe ni.

*****
            Shesh- she'kan kukan da kunnuwan sa suka fara cin karo da shine ya 'dauki hankalin sa da shigowar sa gidan kenan, mahaifiyar sa yake gaidawa amma hankalin sa da idanuwan sa na ga 'kofar 'dakin da yake jiyo kukan duk ya 'kagu ya shiga yaji abinda ya sani kuka yau kuma da wannan farar safiyar.

Tsaye ya mi'ke fuskar sa cike da alamun tsantsan damuwa yake fa'din" Iyami yau kuma me ya samu Zaituna da sassafen nan take kuka?"
Baki Iyami ta kya6e gami da komawa tana fiffita wutan da take hurawa a tsakar gidan na abin karin safe...'kasa- 'kasa cike da jin haushi tace " Wannan kuma sai ka isa gare ta kunnan ka ya jiye maka ai...tunda ni banyi darajar a zo a sanar da ni abinda ke faruwa ba dan munafurci sai dai a zauna a kukan 'karya..."

Bai damu da kalaman Iyamin ba sbd ba yau yasan halin ta ba, da hanzari ya juya ya nufi 'kofar dan duk hankalin sa tashe yake jin sa dan ma na tsagaita kukan tun lokacin da na tsinkayo muryar sa...

Tsaye yake daga bakin 'kofan 'dakin ri'ke da labile yake duba na cike da tausayi da alamun tambaya saman fuskar sa.

Ganin hakan yasa nayi 'kasa da kaina ina mai share hawayen dake bin kunci na suka kuma kasa tsayawa.
" Hamma Bukar barka da safiya.."
Bai amsa ba sai ma tambaya da ya jefe ni da shi" 'Kanwa ta me ya saki kuka kuma da safiyan nan haka..ko yunwa ce..?"
Madadin in bashi amsar tambayar sa, a a sai ma wani kukan da ya kufce min mai karya zuciya.

Sosai jikin sa yayi sanyi a hankali ya saki labilen gami da 'karasowa ciki bayan ya zame takalman 'kafafun sa.

Gaba na ya 'karaso ya dur'kusa da sanyin murya mai tafe da kulawa cikin yaran kanuri yace dani" Baki da lafiya ne...?"
Ina kukan na girgiza masa kaina alamar a a batare da na dubi idanun sa ba.
" To menene?"
Ya sake tambaya ta da kulawa sai de har yanzun ban iya na bashi amsar tamabayar sa ba kuka na kawai nake yi mai sanyin sauti gwanin ban tausayi...da Hijabin da ke kaina na rufe fuska ta nake kuma share hawayen da shi.

Shiru yayi yana sauraron kukan nawa tsawon da'ki'ku sai yama rasa kalmar 'daurawa, har cikin zuciyar sa yake jin kukan nan domin na kasance mafi soyuwa a zuciyar sa duk cikin 'kannan sa gaba 'daya.

Shakuwar ta daban ne, kamar yadda Yah Bukar ya kasance na daban cikin dukkan yayye na.

Sam baya so ya sako sunan mahaifiyar sa cikin maganar duk da yana iya zargin makadmsudin kukan daga wajen ta ne, amma yana iya raba zargin nasa zuwa gida biyu musamman da yasan cewa da wannan safiyar mawuyaci ne ace wani abu ya ha'da mu domin rayuwar gidan kaf cikin tafin hannun sa yake...sanin hakan da yayi yasa shi tafiyar da zargin sa izuwa 6angaren zargin sa na biyu.

BINTEEE ( 'Yata ce)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang