P22

74 7 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...22*
  
               ........Daf da 'kofan Palor tai parking motar sannan ta koma ciki bayan ta bar Naina cikin motar.

Bata zame ko'ina ba sai 'dakin Zaitun tana me 'kara 'daure fuska tamau, sosai take jin tsanar Zaitun 'din har cikin jinin ta, burin ta kawai ta budi ido taga bata tare da su, koma me zai biyo baya ta shirya tar6ar sa daga wajen Rasheed din indai bb idanun yarinyar.

Kallon kallo suka tsaya yi Zaitun da Hameeda, Zaitun duba take mata na mamaki da firgicin abinda ya kawo ta, kallo 'daya idan kaiwa Zaitun zaka fahimci a tsorace take sosai, manyan idanun ta da suka kasance ruwa-ruwa su ta zubawa Hameedan yayin da ita Hameeda ke binta da kallon tsana da takaici, tsana irin marar mix din nan da ba'a iya 6oye shi.

Sai da ta banka mata harara kafin cike da 'dacin rai tace " Ki shirya yanzun nan, Abban su Naina yace na kaiki wajen uwar'dakin sa..".
A yanda tayi maganar a yatsine zaka 'dauka cewa tilastata yin hkn akayi bada niyyar ta bane, amma ga wanda yasani ya kuma san halinta da shirin ta tashi guda zai zaka fahimci tsagwaron tsana ce kawai da rashin kirki ke damin Hameeda.

Zaitun bata yi musu ba ta tashi tsaye kan kafafun ta..." Ki tattaro duk da kayan ku..." Hameeda ta sake fa'da wanda ne hakan ya sanya Zaitun cikin wani yanayi marar misaltuwa, shin farin ciki zata yi ko kovbakin ciki, farin cikin zata bar gidan Dr Rasheed ko bakin cikin bata san inda za'a kuma jefa ta ba.

Cikin wani babban ledan kayan shopping da Rasheed ya kawo musu kaya ta tattare musu kayan nasu duk aciki.
Bata bar komai ba kamar yadda Hameeda ta bata umarni, ita dai lalla6a su take su rabu lpy sbd bindiga bama 'daya ba data tabbatar suna dashi da kuma kashedin Rasheed a gareta.

Goye Mufee tayi ta dauko ledan suka fito..baya Hameeda ta bude mata ta shiga ta kuma rufe shi tana sakin nannauyan ajiyan zuciya, da 'karfi take jin fargaba wanda ya haddasa mata bugun zuciya amma sam bata bawa hkn dama ba ta ci gaba da aiwatar da niyyar ta.

Kamar yadda ta tsara hkn ne ya faru, gateman bai ga shigar su motar ba illa Hameeda ya gani, kuma tinted ce mai duhu da motar, ita kanta ma motar ba'ka ce, sanin hakan kuma ya sa ta yanke shawarar amfani da motar gudun kar kowa yasan sun fita tare.

Unfortunately kuma bata san cewa motar na 'daya daga cikin motocin mugayen fataucin mijin ta ba.

Babu wanda ya tanka kowa cikin motar nan dan kowa nashi tunanin daban, burin Hameeda kawai taga ta isa inda take da buri wanda shine mabudin farin cikin ta ya rufu kwanaki kadan baya, yayin da Zaitun ke ta rarraba idanu da son ganin inda kuma za'a jefa ta.

Dukkan su basu farga ba, basu lura da yadda wani Police bike ke ta bin bayan su ba, basu lura da yadda yk ta magana da wani abu dake makale kan kunnan sa ba har Hameeda ta bar babban titi ta hau by- pass din da zai kaita gidan Antyn ta Saleeha,  kawai bazata kamar daga sama suka ga an musu kawanya an tare gaban su bakaken hilux da ya kasance na jami'an tsaro har guda biyu gaba da baya ga Bike din nan ta gefe saitin Hameeda dake tuki ya saita mata bindiga ga dukkan alamu so ake ta dakatar da driving 'din.

Daga Zaitun har Hameeda bb wanda bai rikice ba, dama ko basu nemi ta tsaya ba dole ne sai ta tsaya 'din taji ba'asin bibiyar tata, balle ma sun nema.

Da gudu 'yan sanda nan suka yi kan Hameeda da ta fara fitowa daga motar sannan suka bu'de da kansu suka fito da Zaitun da tuni har ta fara kwalla.
Me yasa hakan ne wai? Me yasa kusan ko wani lokaci abubuwa ke mata shamaki ga duk wani cikan burin ta, me yasa bindiga ke yawan bibiyar rayuwar ta..?

               Tattara su duk akayi aka wuce da su ofishin 'yan sanda batare da an ba ko guda daga cikin su damar furta ko kalma guda ba...kamar yadda ba ba' sanar da su laifin da ake tuhumar su akai ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now