P66

184 16 33
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...66*

               ........Bai manta dalili da kuma yanayin da suka rabu a jiya ba.

Gaisar da Anty Madeena yayi yana me duban Rayyan dan sosai tausayin abokin nasa ya tsaya masa arai tun a jiya.

Anty Madeena ce tayi masa takaitaccen bayanin abinda take so ayi.
Ya kuwa kallo RAYYAN a firgice yana me mi'kewa, shi dama ya ta6a zargin hakan, ba kuma yaji aransa cewar zargin nasa ll totally go.in vein hakanan kawai ba, amma dayake Rayyan bai bashi 'kofa ba yasa dole ya watsar da batun.

Rayyan daya san dole da jin maganar Fawwaz zai dube shi sai ya ki 'daga idanu ya kalle shi balle su ha'da idanu...ji yake tamkar Fawwaz din na 6ata mai lokaci, 'kage yake da son jin 'karshen sakamakon...ba dan ba zai iya ta6uka komai ba da ko sauraran wani ma bazai yi ba da kansa zai yi komai.

Fawwaz da kansa ya ja jinin su duka yayin da Mufeeda dake rungume jikin Anty Madeena ta saki kuka jin yadda allura ya 6ula mata jiki.
Sosai Anty Ta rungume ta yayin da Rayyan ya zuba musu idanu.
Ji yake tamkar yaje ya kar6e ta ya lallashe ta sbd yadda kukan ke ratsa masa zuciya...amma baya so Anty taga kamar ya za'ke da yawa...amma da ace zai bi umarnin zuciyar sa da tabbas hakan zai yi.

Fawwaz tsaye ya tsaya kan 'kafafaun sa a Lab 'din har aka yi komai aka gama, duk da yake sun zone kusan za'ace a 'kurraren lokaci amma yadda Rayyan ya shiga damuwa yana fatan wannan sakamakon ya wanke masa dukkanin bakin cikin dake cikin zuciyar sa.

Tun da ya fito da sakamakon yake sakin hamdala gami da murmushi ya nufo office 'din sa da sassarfa, ji yake tamkar wani babban kyauta akai masa.

Hakika Allah gwanin baiwa ne kuma sarkin sarakai, Allah mai kyauta da 'kari, ya hana ka wani abin ya kuma baka wani a lkcn da bak zato, sai gashi ya dawo ma Rayyan da farin cikin sa a lokacin da yake tunanin ya rasa ta.

Da zuwa bai ko kalli inda Anty Madeena take ba ya nufi Rayyan ya mika masa Papers 'din fuskar sa kumshe da yalwataccen murmushi, yayin da ya tsurawa Rayyan idanu dan ganin nashi yanayin.

Idanu Rayyan ya zuba akan Papers din tunda ya fara karantawa da ya fahimci abinda suka 'kunsa kawai sai ma ya kasa 'karasa karatun ya tsura musu idanu...sai ya ma rasa shin nazartar rubutun yake ko kuwa irga yawan su, bai ta shi sanin 'kwalla ke bin 'kuncin sa ba har sai da Fawwaz ya dafa shi.

A lokacin ya 'dan motsa kansa sai kuma ya 'daga kai ya kalli Fawwaz dake tsaye kansa da rinannun idanuwan sa, Kai Fawwaz ya jijjiga masa..." Hamdala ya kamata kayi ba kuka ba Dr...ka godewa Allah da ya nufe ka da fahimtar haka tun kafin 'diyar ka ta dulmiya cikin dunia batare da ka san da zaman ta ba, baka ma gode Allah ba da ya sake dawo maka da ita gaban idanun ka ta rayu gaban ka, karkashin inuwar ka da dukiyar ka duk da kuwa baka san cewa jinin ka bace...?"

Karo na farko tsayin ranar ya saki murmushi, murmushin da ya fito tun daga zuciyar sa ya kuma kore masa dukkan 'kuncin da yake jin sa ciki lokuta 'kalilan baya.

A hankali ya sau'ke idanun sa kan cinyar Anty Madeena, Mufeeda ce, yarinyar Zaitoon, hakika ita din jini na nace, 'diyar ciki na....

Daga kan kujerar kawai gani suka yi Rayyan ya zame ya bi kasan tiles basu fahimci abinda yake shirin yi ba sai da suka ga ya sada goshin sa da 'kasan tiles suka fahimci sujudush shukr yayi.....

Anty Madeena kallon sa take yi amma sam hankali da tunanin ta basu a wurin kwata kwata.

Hakika dole a godewa Baiwa, buwaya da kuma cikan ikon ubangiji, bayaga shi wa zai iya wannan abin....Ita kanta 'kwalla take sharewa lkc zuwa lkc.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now