P53

109 7 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...53*

                .......Bai zame ko'ina ba sai part din Sultan zuciyar sa cike fal da tunanin me ya sake jefa Sultan cikin wannan yanayin kuma.

Bell ya ta dannawa amma shiru kamar ciki ba kowa.

'Karshe kai Kawaicya girgiza ya wuce babban part 'din..a hankali yake tafiyar sa cikin natsuwa, jin kansa yake tamkar ba shi ba da kansa yake jin weight 'din sa ya ragu sosai, gaba 'daya ya zabge ramar sa ta fito fili cikin kwanaki 'kalilan....Bai tadda Ammi a parlorn 'kasa ba dan haka sai yayi zaman sa bisa kujera, Hajja Ladi mai aiki ce tafi to ta ganshi tana niyyan komawa ta kawo masa abin sha sai yy saurin yafi to ta da hannu.

Da sauri ta 'karaso tana risinawa take fa'din" Ranka ya da'de barka da yamma..."
Bai bi ta kan gaisuwar ba kawai yace" Kira min Safaah".
Da sauri ta wuce 'dakin Safaah tai 'kiran ta.

Mintina hu'du basu cika ba sai ga ta fito, tun bata 'karaso ba yace" duba min Ammi pls kice mata ina 'kasa..".

Zama ya cigaba da yi ya 'kurawa wayar sa idanu..bansan me yake dubawa cikin wayar ba har lokacin da yaji sautin tafiya daga matakalar bene.

Bai 'daga kai ba ban sani ba ko bai san da tahowar Ammin ba.
Fuskan ta wasai babu alamun damuwa, sosai tayi 'ko'kari wajen 6oye musu damuwar ta har 'yar powder ta shafawa fuskar ta ta ramba'da kwalli cikin idanun ta inda ya fito ras da shi, idan ba sani kayi ba bazaka ta6a tunanin akwai wani abinda ke damun ta a rai ba.

" Rayyaan..shine kuma ka zauna anan kamar wani ba'ko me ya hana ka hawo wa saman yau kuma?"
Idanu ya lumshe ya kuma bu'de su tare da ajiye wayar hannun sa gefe da shi.

Sai da ya saki ajiyan zuciya kafin ya dubi Ammi yace
" Haka nan kawai Ammi".

Zama tayi tana sake duban sa dan ko 'dazu da ya shigo suka gaisa bata kula da yayanin sa ba kamar yanzun ba, ramar da yy ne ya matu'kar bata mamaki sosai.

" Anya Rayyan kana ganin kankacikin madubi kuwa? wannan ramar tayi yawa ko baka jin da'di ne kake 6oye min kaima...?"

Murmushi yy yana gyara zama yace" Safaah ta fini shiga damuwa Ammi..dan Allah ki tausayawa yarinyar nan ki rage damun kanki kar damuwa ta yiwa zuciyar ta illah, abinda ya faru ya riga ya faru..in kuma tunanin ki mu ne to ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru insha Allahu Rabbi..."

Shiru tayi tana kallon cikin idanun sa..sai ya sake yin murmushi yana 'dan lumshe idanu dan ta yarda da shi.." Rayyan..!"
Na'am Ammi.
" Bana son ku sake saka kanku cikin wani ha'darin ne daban, dan Allah ka bawa 'kanin ka ha'kuri ku barwa Allah komai na tabbata shi yasan da mu da duk abinda ke faruwa damu, kuma zai yi mana sakayya dan baya barin zalunci, amma bazan iya juran rashin 'daya daga cikin ku ba, i wish ni in mutu kafin in ga ranar da 'dayan ku zai barni, kai da kanka kasan saka baki ciki irin wannan lamarin dai- dai yake da saka kai tsakanin mutuwa da rayuwa...dan Allah ku rufa min asiri..mu fawwalawa Allah komai.."

" Ki kwantar da hankalin ki Ammi insha Allah babu abinda zai faru, kuma ma mu ina muka ga damar saka kai cikin lamarin? ba fa musan kowa bama balle musan ma'kasudin faruwar lamarin balle akai ga batun tuhumar sa, so kinga kuwa bamu da hanyar saka kanmu, in kuma Sultan ne ki kwantar da hankalin ki zan masa magana...".
Sosai yayi ta kwantar wa da Ammi hankali har ta saki ranta sannan suka cigaba da hira.
Dan shima kokari sosai yy wajen danne abinda yake ji cikin zuciyar sa kawai dai baya son Ammi tasan shirin su ne.

Annan Ammi ke sanar da shi cewa tayi magana da Kabeer anjima zata tura adaeo da su gida tunda akwai isahsshen wajen zama kuma zai fu samun kula idan yana kusa da su.
Rayyan kansa yayi wannan tunanin dama dan haka yace mata..." hakan ma yayi, Allah ya kawo su lafiya..".
Wancan part dake gefen nawan inaga zaifi ko?"
" Erh ai har ma nasa an gyare shi"
Cewar Ammi.

Kai Rayyan ya jinjina yana fadin" masha Allah".

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now