P101

111 12 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...101*

               .......Duk yadda yake jin damuwa gami da 'kaguwa da son jin abinda zai fito bakin Goggon nasa karo 'daya duk yaji wata fitinanniyar bugun zucia daya kore komai sakamakon tsinkayan sautin muryar da tayi sallama...amsa kuwwa sallamar ta rika yi masa a ka.
Dukkanin su juyawa suka yi suka mayar da hankali wajen mashigar gidan..sa6anin Goggo da dama nan take fuskanta.

Inka 'dauke goggo da tayi mutuwan tsaye cikin su bb wanda bai zaro idanu da bu'de baki da ganin ta ba.
Atare Hafiz da Adam suka furta sunan" Zaitoona...!"
Wanda hakan shi ya sanya Goggon Adam mayar da idanun ta garesu cike da tsantsan mamaki.

Ita kanta a 6angaren ta ma haka abin yake.
Cike da tsananin mamakin ganin sa tare da mahaifiyar ta tace" Yah Adam...!"
Tana toshe baki da duk hannuwa biyu.

Kasa amsawa yy kawai ya cigaba da duban ta..ji yk tamkar mafarki, ji yk tamkar idan ya motsa za ace masa ba gaskia bane abinda idanun sa ke gane masa illusion ne kawai da ya saba gani nata.

Amma duk ganin da yake mata cikin mafarkai, hasashe da tunanukan sa bai ta6a kwatanta cikin wannan ni nimtaccen yanayin ba sai dai in zai gansa tare da ita.
Shiga ta kamala, tsabta da kwanciyar hankali 'karara suka bayyana.

Hafiz ne ya sake yin 'karfin halin furta " sunan ta akaro na biyu.
Itama tace " Yah Hafiz"!
Yaushe Zaitoonan sa ta waye? Yaushe ta samu rayuwar mai ingancin da shi ya kasa bata...?
" Yayah Adam...Kai ne...?"
Ta sake tambaya cike da tsananin mamakin ganin sa anan...hakan shi ya yanke masa 'dan guntun tunanin da ya fada.

Wani 'kwarin gwiwa ne yaji ya zo masa nan take bayan tabbatar da cewa ita din ce dai.

Kai ya sosa yana mai 'ka'kalo murmushi yace" Zaitoon Nine..bayan tsawon lkc sai gashi yau ga ni ga kuma ke..."!
" Wa ya nuna maka gidan Inna ta...?"
Ta tasake tambayar sa dan har a lkcn mamakin bai sake ta ba.

Yace
" Baiwa ta ta kawo ni.."!

" Wace ita haka..?"
" Da kaina nazo Zaitoon bayan kin guje ni...?"
Tana shirin magana sai ta hango hadda Innani tayi mutuwar tsaye tana duban ta...fasa maganar tayi ta nufi Inna da gudu tana shirin rungume ta Inanni ta ja baya ka'dan ranta a matukar 6ace ta yadda ko fuskar ta bai 6oye hakan ba.

" Innani ni ce fa...".
Zaitoon ta fa'da da wata karyayyar zucia tana sake duban Innar tata.
Wani lafiyayyen mari Innanu ta sauke mata saman kuncin ta, kafin Shaheed yy wani yun'kuri sai ga Innani ta sake sau'ke mata wani marin.

Da duk hannuwa biyu Zaitoon ta dafe kuncin ta idanuwan ta na zubar da hawaye take duban Innani.
Duk yadda Adam ya shiga tsakanin su hakan bai hana Innani son sake kai mata wani bugun ba..duk da baki 'dayan su hkr suke bata amma Innani tamkar bata sauraren su, ita kuka Zaitoon kuka, Innani fa'di take ta fita ta bar min gida kafin tayi mata mugun duka.

Yadda Innani da Zaitoon ke kuka yasa hatta su Ammi dake waje suna jiran iso daga wajen Zaitoon din kawai suka nufo cikin gidan a tsorace.
Nan suka tarar da hayaniyar.

Tuni Zaitoon na dur'kushe bisa gwiwoyin ta tana kuka ta ha'de hannuwa da alamar ro'kon gafarar Innani.

Ammi ce tayi saurin shiga tsakani tace " Haba haba Innan mu...mene hakan wai, sai kace wacce ta aikata wani gagarumin laifi..?"

" Ta fita ta bar min gida nace!...bana son ganin ta, taje ta koma inda ta fito ta cigaba da rayuwar ta, mun riga mun cire ta a ran mu..mun ha'kura da ita..."
Sai ma ta kasa 'karasa abinda tayi niyyar fa'di kuka ne sosai ya ci 'karfin ta.
Nan ta koma ta zauna kukan takaici da bakin ciki na sake fizgar ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Kde žijí příběhy. Začni objevovat