P46

76 10 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...46*

               ......Duk yadda Zaitoon ke kokarin kauce mata Amrah dole sai ta shiga sabgar ta, sau tari takan gama aikin ta tayi mopping ta tsabtace ko'ina amma Amrah sai tace sam bai yi ba sai ta sake, ko kuma idan Zaitoon ta saka freshner Amrah tace bata son kamshin sa ta san yadda zata yi ta raba mata daki da warin freshner din dan iskanci wai wari bacin Rayyan da kansa ke siyo su masu shegen kamshin da ko ita kanta Zaitoon suna birgeta haka Amrah zata ce turaren wuta take so, sosai take gara Zaitoon da wannan cikin nata da ya 'dan fara bayyana kansa, ga Moopy ma bata tsira a wajen ta duk da 'karantar yarinyar sam Amrah bata gani.
        Akwai ranar da Amrah ta kai ta bango akan Moopy ranar ne ta nuna mata cewa ba zata iya 'daukan wasu maganganun akan Moopy ba, Amrah na cikin sanba'do zagi kawai taji sau'kan mari lafiyayye saman kuncin ta...zaro idanu tayi ta dafe gurin, nuna mufeeda tayi tace" akan wannan banzan wai kk mare ni?"
Sau'kan wani marin taji abinki da ba'a saba ba har 'kasa ta dur'kushe tuni hawaye ya fara fito mata.
Kasa magana tayi dan har kunnuwan ta ji take tamkar sun bar jikin ta banda ra'da'di babu abinda take ji ilahirin jikin ta duk yabi jini zafin marin.

Nuna ta da yatsa Zaitun tayi tace" Kashedi na dake na 'karshe kenan akan yarinya ta, wlh idan kika sake aibanta min yarinya sai na sa6a miki kamannin ki..zan jure komai amma banda wulan'kanta min yarinya...ke kika haifa min ita ne ko kuwa kinsan matsayin ta gare ni...akan Mufeeda na 'kwammaci na rabu da kowa nawa dan haka bana tsoron kowa akan ta, kuma bazan laumci cin fuska a wajen koma waye ba, alkwari na 'daukar wa kaina cewar zan kare mata mutunci da darajar ta akanki kuma bazan karya alkwari na ba, in kin so ki sa a kore ni..."

Wani 'kwarin gwiwa Amrah taji dan ta sosa mata inda yake mata kaikayi, a zafafe ta mi'ke da jajayen idanu tace" Ke har kina gani shegu na da wata daraja ne da har zaki kare mata? 'yar zinar? Dangin fasikai...wallahi kin ji kunya da ko kunyar Allah bakiji balle na mutane kk furta irin wannan magangun..."
bata kai 'karshe ba Zaitun ta nuna ta yatsa tace" Kar ki sake ai banta min 'ya.."
" An aibanta miki 'yar me zakiyi?"
" Bazan yi komai ba, amma nasan duk wanda ya 'kira min 'diya ta da sunan 'yar zina to shine babban 'dan zinan.."

Jin haka yasa Amrah ta manta da zafin marin ta ta taho da sauri wajenta wuyan rigar ta takama tana fa'din" Ni kike so kice wa 'yar zina kome..ke har kin isa kina matsayin 'yar aiki na kice zaki min wannan iskancin, wallahi yau ko ubanki da ya 'daure miki gindi kika je kika yo cikin shege be isa ya hanani korar ki daga gidan  nan ba..."
" Sakar ni to"
tayi maganan tana bin hannun Amrah da kallo..
a hargitse Amrah ta furta
" Baza'a sake ba me zakiyi...?"
Saukan mari kawai ta sake ji saman fuskar ta da ya sa ta sakin rigar Zaitun tayi baya...matsawa Zaitun ta sake yi kusa da ita dan ta riga ta hassala..amma kafin ta 'karasa gaban Amrah ta ganshi kamar daga sama agaban ta, daga shi sai dogon wando ba'ki da alamu bacci yake yi hayaniyar su ta tashe shi.
Amrah na ganin sa ta dafe ciki ta saki wani sautin wani wahalallen kuka tana fadin " cikina, wayyo cikina zata kashe ni.."
ta durkushe a wajen dafe da cikin ta.
Da sauri Rayyan ya maida duban sa gareta cike da mamaki ya nufe ta yana tallafo ta zuwa jikin sa tare da cusa hannun sa 'daya cikin rigar ta yana shafo cikin nata yake mata sannu cike da kulawa.

Sai da ya kaita kan kujerar ya zaunar da ita da kyau gami da daidaita mata zaman yadda zata fi jin dadi kafin ya dawo da duban sa ga Zaitoon da tuni tayi mutuwar tsaye jin sharrin da Amrah ta kirkiro.

Ganin irin kallon da yake bin ta da shi ne ya sanya ta kawar da kanta gefe zuciyar ta na harbawa...kan Moopy dake ma'kale da 'kafafun ta ya sau'ke idanun sa.

Kallon rainin hankali ya 'dago yayi mata bata damu ba ta 'dago Moopy saman jikin ta...tana niyyan juyawa ta tsinkayi muryar sa yana fa'din" 'Ya'ya da dukiya halaka ne ga 'yan Adam, ban tabbatar ba sai yanzu da na ga misali akanki, Matata kk duka akan 'diyar ki? 'yar kin ma mara asali mara gata irin wannan..? Mata ta dake 'dauke da cikin gudan jini na..?"

Waigowa tayi bata kalle shi ba idanun ta ta sau'ke akan Amrah dake kuka harda sheshsheka..da gudu itama hawayen ta suka gangaro...wannan kalmar ta ishe ta haka, wace iriyar rayuwa ce wannan da son kai ya yiwa kowa 'kawanya? duk babu 'kaunar Moopy cikin zu'katan su, duk zuciyoyin su babu gaskiya, duk gidan nan Ammi ka'dai ke son Moopy sai Marwa in basu ba kowa tsana yake nuna mata, dan haka a yau ba sai gobe ba dole zata bar gidan nan, zata bar musu gidan su taje inda zata samawa Moopy farin ciki da walwala.
" Bakya tunanin irin 'daurin da zan iya miki dalilin dakar min iyali da kika yi acikin gidana, baki tunanin hanyar halaka kika dauko wa kanki bayan na baya da kika aikata akan 'diyar ki...Baki tunanin zan iya halakaki idan wani abu ya samu cikin dake jikin ta sanadin ki? iyali nace fa Amrah ko kin mance ne..?"

Duban inda Amrah take tayi suka sake ha'da idanu, bata kalle shi ba kamar yadda koka'dan bata ji tsoron sa ba ko tsoron abinda zai iya biyo baya ba...cikin maganganun sa abu guda kawai tafi ri'kewa kuma shine yake ta mata yawo a 'kwa'kwalwa har ya dasa ayar maganar sa.
" 'Diya ta ba shegiya bace ku sani, kuma nasan duk abinda ya faru dani kaddara ce kowa kuma baifi karfin ta faru gareshi ba...".

Daga hakan bata ce da shi komai ba kawai ta juya tayi gaba abinta.

Shi kam rintse idanu yayi yana jin zuciyar sa na 'daukan zafi, shifa ba nufin sa ya zagi 'diyar ta ba, sam bai yi niyyan zagin ta ko 'yar ta ba amma haushin ganin dukan da tayiwa Amrah ne ya 'dan ta6a ransa duk da yasan ba cikin Amrah ta buga ba kamar yadda idanun sa suka gane masa yasan kawai Amrah tayi hakan ne sbdcwata manufa kuma ko maganar da yayin yayi ne kawai dan Amrah taji dadi aranta, ko ba komai Amrah iyalin sa ne kuma shi ke da alhakin kare dukkan hakkokin ta...
" Wallahi Baby ka kora ta agidan nan mari na fa tayi dan kawai nace da 'yar ta shegiya kuma ai shegiyar ce Baby ba 'karya nayi ba".
Muryar Amrah ya tsinkaya tana fa'din hakan.
ko juyowa ya kalle ta bai yi ba kawai ya koma 'dakin sa, yasan itama Amrahn da laifin ta, ta fiye shiga sbgar su yana lura da ita batun yau ba kawai magana ce bai ta6a yi mata kan hakan ba bai kuma san dalilin shirun sa ba kamar yadda bai san matsayin abinda Amrahn ke aikatawa cikin ransa ba musamman idan yayi duba da rashin jituwar da ke tsakanin Zaitoon din da shi sai ya rasa shin abinda Amrahn ke yi da'da'da masa yake yi ko kuma ba'kanta masa sam ya rasa takamammiyar amsa shiyasa bai ta6a tankawa ba.
Amma lokuta da dama ya kanji babu dadi idan yaga ko jin faruwar wani abu tsakanin ta Amrah, sai yaji yafi so shi da kansa yayi ta ba'kanta musu amma kar wani ya kwatanta irin hakan sai shi ka'dai, atimes kuma sai yaji bai damu ba koda an ci zarafin nasu.

Ita kam Amrah zama tayi nan kan kujera tana 'karasa kukan ta da bata 'karasa ba cike da takaici.
Ba haka ta so ba, taso da Rayyan ya fito ya rama mata dukan ta...amma be yi hakan ba, dama can ta san shi ba gwanin bugun mutum bane especially mace baya so yaga ana cin zarafin 'ya mace amma ai wannan kamar cin zarafin ta akayi itama kuma yayi biris da al'amarin.

Wayar ta 'dauko tana kuka ta irgawa mahaifiyar ta tas hadda 'kari ma, da 'kyar ta lallashe ta tayi shiru da alkwarin zata 'kira Ammin nasu idan ta dawo ma zata zo da kanta su yi magana.

Tace bazai yiwu yar aiki ta samu wannan babbar damar ba bacin asali 'diyar ta da gatanta, ba gidan aure ne ya bata gata ba balle a dinga karya mata darajar ta, baya ga hakama ciki take dauke da shi ita da yakamata a ririta kuma ace itace zata zam abin banza bazai yiyu ba ..."

Shin ko Ammi zata amince da hukuncin mahaifiyar Amrah...?

Salmerh😘

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now