63

88 12 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...63*

               ........ _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...._ Sai da ta maimaita har sau uku kafin wani kuka ya 'kwace mata mai 'karfin gaske, hawayen Amrah kasa tsayawa yayi kawai ta kwantar da babyn kusa da ita, meyasa zai mata haka?, meyasa Sultan zai mata haka?
Dama dakon cikin sa tayi batare da ta sani ba, dama dakon cikin 'dan da bana Rayyan ta yi ba?

Kuka sosai take sai dai cikin kukan take fatan kamar yadda taga fuskar yaron nan ita ka'dai har ta fahimci bashi da ala'ka da Rayyan Allah yasa har abada ya kasance ita ka'dai 'din Allah zai bawa damar ganin kamannin sa, tun daga can cikin zuciyar ta kukan ke tasowa, sosai jikin Nurse yayi sanyi, kasa cigaba da aikin da ke gaban ta tayi ta tsurawa Amrah idanu, sai ma ta rasa da wani kalma zata fara yi mata magana.

Kusa da ita ta matsa daf tasa hannu ta 'dauke yaron daga kusa da Amrah ta maida shi gefe can inda ake saka jarirai ta kwantar da shi sannan da mugun sanyin jiki ta dawo ga Amrah ta 'dan dafa kafa'dar ta..." Haba Hajia, wannan kukan naki zai iya kawo illa ga lafiyar ki fa, dan Allah kiyi hakuri ki bar kukan nan, ke da ya kamata ace kinfi kowa farin ciki da kyautar da Allah ya baki sannan ya baki dama kika haifo 'danki lafia, shi lafiya kema da lafiyar ki meyasa kuma kike 'ko'karin saka masa da butulci irin wannan....?"

Kai Amrah ke faman juyawa hagu da dama, " Ki barni nayi kuka dan Allah, ki barni nayi kuka na, dan sam bani da mafita ban san yadda zanyi ba..."
Hannu duk biyu ta ha'de tana kallon Nurse hawaye na bin fuskar ta ta fara fa'din..." Nurse dan Allah ki taimake ni, ki sanar da ni taya zan cire kaina, nasan babu wanda zai sake yadda dani a halin yanzu kafin hakan ma bansan ta yadda zan fuskanci kowa ba harda mijina, _wallahi yaron nan ba 'dan Rayyan bane na Sultan ne, ki fa'da min yanzu ya zanyi kenan kowa idan ya ga Babyn zai gane na waye ne...?"_

Ido Nurse ta zaro sosai tana duban Amrah..." Ban fahimce ki ba Madam..kina nufin wannan babyn ba na Dr Rayyan bane...shi waye Sultan kuma...?"

" Kanin sa ne, kani yake a wajen sa..."
Ta bata amsa da sauri.
" Ohh 'kanin sa..? Lallai... _wannan shine matar me gida ta haifi 'dan maigadin gida_ Nurse ta furta cikin zuciyar ta ta jinjina kai..ji wani al'amari.
"..to ke me ya kaiki wannan danyen aikin? Ko ba Sultan wannan daya kawo kun ba..? Haba 'yar uwa, dubi Dr Rayyan fisabilillahi, dubi kyan zubi da tsarin halittar sa banda baiwa kala kala da Allah ya bashi amma har wani namijin banza da be kama 'kafar sa a komai bane zai ru'de ki....?"
" Wallahi nima sai yanzu naga rashin kyautawa ta, yanzu ne na fahimci kuskuren da nayi ta aikatawa abaya, for now mafita kawai nake bu'kata daga gareki ta yadda babu wanda zai gane kamar yaron tashin farko.."

Baki Nurse ta kya6e" ni dai babu wata hanya da na sani..amma tunda 'yan uwa suke ai babu wata matsala,  zai kasance ne tamkar kawai yaron ya 'dakko kamannin 'kanin mahaifin sa ne..."

" Ke akwai fa matsala babba ma kuwa, that it'snt possible hakan ya faru.."
" As in..?"
" Babu wata ala'kar jini fa tsakanin su kawai sunan 'kani yake amsawa a wajen sa..."
" Toh kawai ki masge karki nuna damuwar ki ma balle wani ya fahimci halin da kike ciki, idan babu wanda ke zargin ki dama can toh babu wanda zai fahimta...."
" Ina jin tsoro...."
" Kar ki damu babu abinda zai faru da iznin Allah, amma a ringa kiyaye dokokin Allah musamman in ya kasance da aure akanki hukuncin ba 'daya bane, kuma idan ka daure ranka nawa ma rayuwar take jindadin nan duniyar fa bai ko kama 'kafar can ba....."

   Duk maganganun da suka tattauna a kunnan Dr Fawwaz ne, dan yazo 'daukan yaron yaron dan kaishi ai masa kaciya yaji abinda yaso rikitar da shi, da 'kyar ya iya daurewa ya basar kamar bai ji komai ba.

Bashi da tantama na neman Hujja ko wani abin daban tunda da kunnuwan sa yaji Amrah da bakin ta take fa'da 'karshen shaida kenan.

Ji yayi ko 'kaunar ganin Amran bai yi hakan yasa yasa shi juyawa ya fita da niyyar fasa shiga dakin, amma tuno Rayyan abokin sa ya sanyashi dakatawa, yanzun nan rabuwar su a masallaci da shi ya kuma fahimci kwata- kwata ba cikin yanayi mai da'di yake ba, Rayyan wani sa'in na bashi tausayi matu'ka, sbd yadda abubuwa marasa da'di ke yawan yi masa 'kawanya, sai dai yasan duk jarrabawa ce ta ubangiji kuma bayin sa da yake so.yake jarabta masu hakuri kadai ke iya jurewa su cinye jarrabawar su.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now