39

67 4 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...39*

               ........Hawowa yake cikin takun sa mai matukar birgewa da tafiya da hankalin duk mai kallon sa, tafiyar sa cikin natsuwa yake yin ta, tun da ya fara haurowa ya lura da yarinyar da bama tasan da tahowar sa ba, ba 'karamin mamaki yayi ba ganin ta bakin stairs ita ka'dai ayau 'din, iya sanin sa da 'yar gwal 'din nan ba kasafai zaka ganta ita daya batare da uwarta ba, da wuya ne ma idan uwar tasan cewa ta iso har nan dan ya lura tafi bawa yarinyar muhimmanci fiye ma da kowa da cikin rayuwar ta, sai dai tunda ya ganta saman Ammin yasan cewa uwartata ma na nan kusa da ita dan a yadda ya fahimce ta bata iya yin nisa da yarinyar sosai, shi kam kallon ta yake yana jinjina kyau irin na yarinyar, sai kuma akayi dace ta yi sa'ar uwa mai son farin cikin ta da son gyara mata jiki, domin tun da yake ganin yarinyar be ta6a ganin ta cikin yanayin da ba shine ba..kullum tsab zaka ganta cikin kayan ta masu 'daukan hankali.....

Bai ma gama wannan tunanin ba Mufee ta 'dago ta kalle shi bayan ankarewa da tayi da mutum na tahowa kusa da ita sanadiyyan 'karan takun sa da taji.

Ai kuwa take ta gigice ta fara kyabe baki tana 'daga hannuwa sama kamar mai 'daukan nata na a kusa da ita ne da alamun 'kage take sosai ta bar wurin kafin ya cimmata, cikin rashin sa'a sai ta zame tayo baya, step biyu ya rage masa ya hauro  amma ganin yarinyar na shirin gangarawa yasa shi take su a taki 'daya caraf ya riqo hannun ta hakan ya taimaka wajen hanata fa'duwa.
   Hakan ma gaba 'daya ya faru ne cikin sakannin da a'kalla baza fi biyu zuwa uku ba, shikan sa bazata abin yai masa, bai zaci faruwar hakan ba, yayin da Moopy ta sake razana jin ta ya riketa fin ma razanar da tayi abaya da ganin sa, hakan ne ya sanya ta sakin kuka mai 'karfi.
Rintse idanu yy yana jin ihun nata na neman hargitsa masa kwalkwalwa...yau ka'dai yaji tashin hankali har ransa saboda kukan yarinyar nan...lokaci guda tunanin yadda zai lallasheta tayi shiru yazo ransa amma ya rasa me zai mata.

A hankali ya sau'ke idanun sa a kan fuskar ta yayinda yake jin bugun zuciyar sa na 'kara tsanantawa..wanda yayi dai-dai da fitowar Zaitun da gudu daga bedroom 'din Ammi....
Turus taja ta tsaya ganin 'diyar ta a hannun sa cike da mamaki ta zuba masa idanu tama kasa kasa 'karasawa inda suke.
Ganin yadda ta ritsa shi da idanu ya sa shima 'din kallon ta, fuskar sa babu yabo babu fallasa bazaka ta6a fassara yanayin da yake ciki ba.

Ido cikin ido suke kallon juna kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa gefe guda kuma kukan Mufeedah na tashi har yanzu bata da alamun tsagaitawa...tuni idanun Zaitun sun cika da 'kwalla har bibbiyu take ganin sa banda tu'ku'ki da zuciyar ta ke yi, dama ta sani tunda taji kukan Mufee tasan bakowa bane sai shi.

Tsawon mintina biyu suna kallon kallo da shi ko zuciyar  sai lokacin ma Moopy dake ta faman zillewa tana son barin hannun sa ta lura da Zaitun dake tsaye can nesa ka'dan dasu, hakan sai ya 'kara mata kaimi wajen son barin jikin nasa tare da fa'din Mam...my..., Mam...my cikin kuka sosai tana mi'ka hannayen ta ga Zaitun.

Shi kam bai wani damu ba sai ya 'dage gira 'daya ya 'daga 'kafa ya taho a hankali zuwa gaban ta yana fa'din" Kin wani tsaya kallo na..so kike sai ta toshe min kunnuwa da ihunta kafin ki kar6e ta dan mugunta ko?"
Bata ce dashi 'kala har yanzun kallon sa take tana mamakin abinda yai wa yarinyar.

Mi'ka mata Mufeedahn yy gaba yana sake fa'din " amshe ta ko in sake ta ta fa'di.."
Da sauri Moopy ta bar jikin sa ta cakume jikin Zaitun 'din tana rage sautin kukan ta itama tana duban Rayyan.

Zaitun ma sai ta rungume ta 'kam tana sake bin shi da kallon tuhuma har da waigawa, kamar bazai yi magana ba amma ganin irin kallon da take binsan da shi yasa shi batare da ya jiyo ba ya furta" Dan Allah kar ki cinye ni....zamewa zatayi na tare ta".
Daga haka ya tura 'dakin Ammi da sallama ya shiga.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now