P100

187 16 22
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...100*

               ......." Nasan kowa yaji me na aikata a duniyan nan sai ya tsane ni, kowa yasan mene hali na na 6oye tsana ta zai yi, ngd sosai da baki tsane ni ba Marwa har na samu darajar da kk iya zuwa waje na duk da abubuwan da na aikata mk..ki yafe min dan Allah...ki yafewa wannan bawa mai tsananin son kansa da rashin tausayin wa'danda suka fi kowa 'kaunar sa a dunia, wa'danda suka nuna masa gatan da ko mahaifan sa basu nuna masa ba..wa'danda suka maishe shi mutum a lkcn da akayi watsi dashi...ki yafe min bisa ga cin amanar da nayi mk Marwa...dan Allah ki......"

Amra da ke tahowa a gigice 'karshen maganar Sultan ce ta fa'da kunnuwan ta ai kuwa batare da ta fahimci komai kan maganar ba kawai suka tsinkayi muryar ta da 'karfi tana fa'din" Ka cucue ni Sultan...baka kyauta min ba, ta ya zaka saka Marwa agaba kana tona min sirri?..taya zaka zauna kana fa'da mata cewa kaci amanar ta? taya zaka fa'da mata cewa Arfan ribar cin amana ne Sultan...?"
Sai kawai ta rushe da kuka ta sauka 'kasa bisa gwiwawoyin ta itama.

A yadda tayi maganar da sauti mai 'karfi yasa ilahirin wa'danda ke keway e da wajen bb wanda bai ji me tace ba, ciki kuwa hadda Rayyan.

Hakan kuma shi ya janyo hankula da idanuwan mutanen gaba 'daya kanta.
Ba Sultan da Marwa ka'dai da har sai da ta ha'da da tsayuwa ba hatta Rayyan juyowa yy yana duban ta cike da tsantsan mamaki da takaici gami da jin haushin ta, me ma ya kawo ta kuma a wani dalilin ta tazo..?"
Ya tambayi kansa.

Marwa da yake ta riga tasan zancen bata iya tace komai ba illa kawai ta dubi Amra ta kuma dubi Sultan da cikin yanayin ya 'dage mata kansa alamar tabbatarwa.

Idanun ta ne suka fara cikowa da sabbin ruwa batare da 6ata lkc ba kuma suka fara gangarowa.
Sultan ta nuna da yatsa bakin ta na motsi amma ta kasa furta komai.

Jikin ta rawa yake sosai, ta riga tasan da batun tun a gida a wancan ranar da Anty Raihana ta bayyana mata shi, sam bata ji ta yadda ba, hkn yasa hatta Zaitoon bata iya ta bawa lbrn ba...tazone dama taji gaskiyar lamarin daga gareshi sai gashi Allah ya turo Amra ta bayyana komai...a wancan lkcn sam sam ta kasa jin amincewa ne amma yanzu da kunnen ta ta tabbatar daga bakin da ta san cewa hakan kawae bazata yiwa kanta sharri ba.

Sultan take nunawa tana son fa'din wani abu amma bakin ta ya kasa budewa.
Da gudu ta juya ta fita bata tsaya ko ina ba sai jikin motar da suka zo ta rungume motar tana kuka sosai, irin kukan nan mai matukar ban tausayi a gani da sauraro.

Ji take ko ina yai mata zafi a duniyan nan, taya hakan zai zam gaskia, taya ma ya faru? Wannan wace iriyar kwamacala ce? ace matar 'dan'uwan ta uwa daya uba 'daya sukayi tarayya da mijinta kuma har da haifa masa yaro...innalilallahi wa inna ilaihi raji un...wannan jagwalgwale har ina..?wace iriyar 'kazamar rayuwa ce wannan?

Ji tayi baki daya duniyan tai mata zafi, ji tayi babu wani sauran farin ciki da ya rage mata a duniyan, ada bata yadda Sultan zai iya aikata kwatankwacin hakan ba amma zuwa yanzu tsoro ma take ji sosai kowa tsoro yake bata ba Sultan ka'dai ba.

Rayyan kallon Amra yake yana 'karawa, mamakin ta duk yabi ya cika shi, kuka take amma bakin ta ya kasa yin shiru, da kanta take faman tonawa kanta asiri a bainar jama'a bacin bb wanda ya nemi ko ya tambaye ta jin wani abu.
Shin tsoro ne ko kuwa firgici? ko kuwa tsantsan rashin gaskia ne ya sa tayi hakan.

Takaicin ta bb inda bai ratsa cikin zuciya da jinin sa ba...har wani 'daci 'daci yk ji ke taso masa tsabar bakin ciki da takaici.

'Karamin tsaki kawai yaja ya nufi hanyar fita dai- dai lkcn da jami'an tsaro ke bawa Sultan umarnin komawa ciki shi kuma yana fa'din babu wani sauran sirri da ya rage min Amra...ban san amfanin ko wani sirri tattare da ni ba a halin yanzu, Arfan ka'dai gare ni sai Allah na, dama bani da kowa taimako na akayi aka bani dangi aka bani muhalli, aka bani sittira aka bani gida aka mutuntani aka mayar dani 'da amma na butulce...ban sani ba ashe tun farkon rayuwa ta ni ba mai sa'a bane, ni ba mai nasara bane tunda banyi nasarar fara rayuwa da mahaifa na bama, ban san jinsin ina ne ni ba, ban san matsayi na cikin al' umma ba, ban san matakin daraja ko kaskantar ahali na ba, tun afarko na rasa wannan damar, na rasa damar sanin asali na, yanzu nazo ga6ar da ko da ina dasu ma basu da wani amfani gare ni balle ma babu su, toh me zan rufe, me zan rufe a rayuwata, na riga na lalata jiya na, yau da gobe na kuwa duk anan gidan suke me zan rufe da zai min amfani? Da kaina na jawa kaina, da kaina na ja wa kaina sake rasa wata damar ta daban....."

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now