P105

95 6 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...105*

               ........Kamar yadda yace haka tayi, abincin ta caccakula sannan ta ta kora maganin tana yatsine fuskar ta.

Yamma ta riga tayi sosai dan haka bata so ta sake kwanciya musamman ma sbd ganin maghrib ta gabato, hakan yasa kawai ta yanke shawarar zagawa cikin gidan, amma sam sai taji zuciyar ta bai yi na'am da hakan ba, tsoro ma taji ya tsirga mata lokaci guda.

Nan ta zauna tana tunani bata ankara ba sai jin 'kiran sallar maghrib tayi...bata 6ata lokaci ba ta mike ta gabatar da sallan ta har tayi isha'i kuwa bata jin motsin kowa ba...nan tsoro ya sake shigan ta sosai.

Tashi tayi taje ta rufe 'kofan ta da makulli, windows ma duk ta rufe su ta gyara curtains 'din ma tsaf sannan tayi shirin bacci.

Duk kuwa abinda take yi cikin sanyin jiki take yin sa dan ko motsin kirki bata iyawa balle ta6a abinda tasan zai bada sauti a zahiri sbd tsananin tsoro...wani turare ma da ta 'dakko zata fesa jin yana bada sautin 'yar 'kara da sauri ta ajiye sa ta 'dauki wanda tasan bai fidda sautin komai illah kamshi tayi amfani da shi...domin ta jima da koyon son 'kamshi wajen Marwa.

Tana gamawa tayi kwanciyar ta ta rufe har kanta cikin duvet sannan ta fara karanto azhkar cikin ranta.

Tana 'kewar Innar ta, Mufee, da su Marwa amma ba halin magana da su.
Sam bata san amfanin kawo wannan gidan ba, haka nan kawai an tsamo ta cikin 'yan uwanta aka jefo cikin wannan gida da baida maraba da kurkuku...gidan da hatta Mufeedan ta ma shamaki yy mata da ita.

Lokaci guda sai tunannin ta ya koma baya, can baya lokacin da aka ta6a sace su ita da Mufee...yanayin halin da suka shiga da yanayin mutanen, a hankali tunanin ta ya gangaro kan Sultan.

Wani sabon firgici da tsoro ne ya diran mata lokaci guda da ko dan yatsanta bata 'kaunar motsawa balle jikin ta, illah addu'a da take iya yi shima a zuci.

Haka nan kawai sai taji wasu zafafan hawaye na sakko mata.
" Banda ba'kin hali ina ma laifin akaita gidan Ammi, da yanzu suna can tare da Mufee da Marwan ta".
Ta sake ayyana hakan cikin ranta.

Haka ta dauki tsawon lokaci cikin wannan yanayin, bayan ta gaji da kukan bacci 6arawo ya sace ta.

Bata san lokacin da ya shigo gidan ba dan haka ko motsin sa bata ji ba.

Dan yakai kusan karfe tara kafin ya dawo, Mufee ya samu itama 'din nata 'kananun kuka wai Mammi, 'dan zaman da sukayi a gida garin su Zaitoon su ka'dai ya 'kara 'karfafa sha'kuwar su, ita nan Mufeeda wai har ta fara mance mutane.
Tana ganin sa kuwa ta taho wajen sa da gudu ta rungume shi..koda ya 'dago ta luf tayi ajikin sa tana sauke ajiyan numfashi, sosai ta bashi tausayi.

Ya riga yasan damuwar ta dan haka cikin ransa yake tunanin mafita.

Bahijja ya 'kira yake tambayar ta inda wani chocolates ta kawo masa dan shi babu abinda ya riko.
Anty najin haka tace" Rayyan za'kin nan fa...ban fiye son ana bata ba gaskia?"
" Ba abinda zai mata Anty".
Tace" Toh..Allah yasa".
Kafin akawo din ne suka samu daman gaisawa da Anty.

Yana bu'de mata Mufee ta dago tana duban hannun sa jin karan ledan..sai da ya sa mata abaki kafin ya bata sauran a hannun ta.
" Abbah..?!
Yaji dadi sosai da sunan da ta 'kira sa da shi.
Hakan yasa shi amsa ta cikin tsananin farin ciki yace" Na'am.. Mamana ".
Tace" Mammi.."!
" Ita kike so?"
Sai ta 'dage kanta sama.
Murmushi yayi haka ma Anty itama murmushin tayi inda ta 'kara da fa'din" ai Mufeeda badai kulafucin uwa ba..na jima ban ga yaro irinta ba gaskia".

Kusa da kunnen ta ya ra'da mata"  zanzo in kaiki wajen ta kinji mamana amma ba yau ba..".
Yasan ba fahimtar sa zatayi ba dan haka bai damu da amsawa ko rashin amsawar ta duk da yake Mufee sai da ta dage masa kai sama alamun ta amsa din.
Kafin ya bar gidan ma har tayi bacci ajikin sa, Bahijja ce tazo ta 'dauke ta zuwa makwancin ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now