P14

51 8 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...14*

        "..Kai Hajjaju Zaitunar..?...amma dai sai an raba ta da yarinyar nan ko, dan kinsan Hajiya Kameela bazata yadda ta kar6e ta da yarinya ba.."
Nisawa Hajjaju tayi kana tace
" Nima nayi wannan tunanin wlh Shaheeda na kuma samo mafita tuntuni, akwai wata Hajiyar Bangis da kwanaki muka je wajen tannan can Hayi kin tuna ni ko ba dake muka je bane? Mubeena kamar da ke ne ko...?" Ta kai karshen zancen da juyawa ta dubi mai suna Mubeenar.
"...erh Hajjaju da ni ne ban manta ba kuma..."
Amsar Mubeenar kenan dake daga can gefe tana faman latsa waya da taunar cingum lokaci guda.
" Toh ita ai tana amsar kananun yara, can take kaisu Lagos ake dillancin su ina ga itama wannan din hakan za'ayi kinga ba kare bin damo dole ta saki ranta damu in ta wayi gari taga babu 'yar...."
" Ho Hajjaju...Ho Hajjaju uwar 'yan mata, Hajjaju maganin kukan mu...."
'Yan matan nata da basu fi uku a wajen ba suka saki shewan da zai baka mamaki.
Murmushi Hajjaju tayi cike da jin dadin yadda 'yan matan ke fasa mata kai...tace" ni ina Sa'eeda ne mutumin ta fa ya shigo gari is better ta zam cikin shiri kunsan 'Dan maliki babu sauqi.."
" Wlh Hajjajun mu baki da kyau..".
Cewar 'daya daga cikin su tana me sakin dariya gami da mikewa..." Bari kuwa inje in tunatar da ita dan nasan mu ma zamu 'dan ji'ku albarkacin masu albarka..."
Tayi maganar tana me nufan 6angaren da 'dakin Sa'eeda yake.
Daya ke ko ina 'dakuna ne birjik zagaye da babban Parlourn gidan.

Zaitun kam da ta ji wani fa'duwar gaba bata san lokacin da ta juya ta koma dakin ta ba harda sa lock a kofar, ba ta ma tsaya ta saurin sauran surutan nasu ba dan bashi ne gaban ta ba, sunan ta da taji da kuma na Mufeeda shine kadai damuwar, the fact that za'a rabata da Mufee shi yafi dugunzuma hankalin ta,  tsoro da fargaba duk suka diran mata lokaci guda..banda 'kwalla babu abinda ke mata zarya...dukkanin ilahirin jikin ta rawa yake...ko nan da can ta kasa matsawa sai da tayi kuka mai isan ta kafin ta fara tambayar kanta.
" Wai me yasa kowa bai san ganin ta tare da Mufee ne? Meyasa kowa be son ta..? Shin 'yar yarinyar nan akwai abinda take tare musu ne ko me...?"

Tashin hankali da damuwar da Zaitunar ta shiga sosai ya kasa 6oyuwa agare ta...tun lokacin da taji zancen kuka bai bar idanun ta ba...karshe sai a bayi ta tarawa Mufee ruwan tasha ba ta iya ta sake fita cikin ahalin gidan ba ko kaunar ganin guda daga cikin su ma bata yi...cikin kayan kwalam da Hajjaju ke 'dan siya mata ta samawa Mufee biskuits ta ci tasha ruwa akai..dama yarinyar ba wani cin abincin azo agani take ba shiyasa bata dame ta ba tai baccin ta.

Can kusan la'asar taji ana nocking 'kofar kamar bazata bude ba amma kuma sai ta tashi ta bude jin muryar Na'eema...tana budewa kuwa Na'eeman ta gani hannun ta rike da plate din abinci suka ha'da idanu...kowa tsayawa yiwa 'dan uwan sa kallon tuhuma yayi...yayin da Na'eema ta zaro idanu kan fuskar  Zaitun din tace..." Kai Maman Mufee kin ga idanun ki kuwa..hala ciwo suke miki..?"
Kawar da kai Zaitun tayi gudun kar Na'eemar ta dago damuwar ta tana duban gefe ta bata amsa da fadin
" Zogi suke min..koda nayi bacci kuma sai duk suka kumbura..".
" Kai sannu..dama abinci na kawo miki, yau fa duk ma baki fito ba Hajjaju ma da kanta na cigiyan ki ".
" Zan fito bari na 'dan watsa ruwa kafin.."
Zaitun ta fada tana me ansan abincin daga hannun Na'eema, kamar tace bazata ciba Na'eemar ta koma da shi amma gudun kar ta gano manufar ta yasa ta ansa kawai.
" Da dai yafi gaskiya..ki 'dan fito ko 'yar hiran nan ma ai tana 'debe kewa".
Na'eema ta fada tana juyawa cikin tafiyar rausaya da a kullun ake kokarin koyawa Zaitun shi...Sai da ta sake rufe kofar kafin ta koma cikin dakin.

Ruwan ta shiga ta watsa kamar yadda ta fada dan koba komai ita kanta tana so taji dadin jikin ta sosai ta wanke fuskar ta da ruwa me 'dan 'dumi sbd kumburin fuskar ya sake.
Tana fitowa kuma sai ta ci karo da Mufee ta tashi daga baccin tana rarraba idanun neman ta dama baccin da take yi yin ne ya sa Zaitun barin ta bayan ta rufe ko'ina ta tabbatar da babu hanya ko kafar da wani zai iya shigowa..." Yauwa Mama na zo in miki wanka kema dan dukkan alamu sun nuna wata kaddarar ke son sake tunkaro mu.."
Ta karasa maganar tana 'dago Mufee gami da cire mata kayan jikin ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now