P86

102 11 1
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...86*

             .......Ban gama watsar da wancan al'amarin cikin raina ba sai gashi yau ma Iyami na shirin turani jejin, wani lokaci sai in ga kamar da gangan kawai take yi min hakan saboda mugunta ko kuma wani abin daban.

" Zaituna!"
Na sake jiyo muryar ta a akaro na biyu.
Ko.nace zan amsa sautin murya ta bazai fito fili har ta ji sakamakon zazzafan yaanayin da nake ciki.

" Ke Zaituna!!
N sake tsinkayo muryar Iyami dake furta sunan nawa cike da izza da masifar da ya cika mata zucia.
Hakan kuwa shi ya ankarar da ni cewa ashe fa tun 'dazun take faman 'kira na ina can ina shirin zurfafa tunani.

Wani abu ne me 'daci naji ya tokare min zuciya, 'kirji na ne ya cigaba da bugawa da 'karfi yayin da sautin muryar Iyami ya cigaba ta kara'de gidan namu, masifa take da iya karfin ta tana faman aibatani.

Tsawon wani lkc tana abu guda, yayin da nake sake ji jiki na na min nawi sosai, bansan lkcn da 'kwalla ya fara kwaranyo min ba, kalma guda ce da kusan kullum sai na ambace ta har yau din kuma na rasa amsar ta.
" Shin da wanne zanji...?"
Kusan kowace rana sai abubuwa sun ca6e min na rasa mafita guda.
" Yah Allah ka dube ni, ka saukaka min al'amura na...Yah Allah idan bari na duniya shine min alkhairi kuma sau'ki ga zazzafar rayuwar da nake ciki Yah Allah ka 'dauki raina badan na gaji da yi maka bauta ko gajia da jarabtar da ka 'daura min ba, Yah Allah ka 'dauki raina kana mai yarje min cikin aminci da salama ka sani cikin bayin ka salihai..."

Duk yadda naso katange kaina da kunnuwa na daga sauraren masifar da Iyami ke sauke min abin ya faskara.

Da 'kyar na bawa kaina 'kwarin gwiwar da har na iya sakko da kafafu na na zauna da 'kyar ina me sakin wahalallen numfashi.

Na 6ata kimanin mintina uku kafin na iya mi'kewa tsaye saboda yanda nake jin 'kirji na, banda jiri da nake ji na shirin 'diba na.

Gyara zaman hijabin da ke kaina nayi idanu na kokarin lumshewa..bango na dafe na fara takawa a hankali, amma bazan iya mi'kewa tsaye tsaf kamar yadda na saba ba.

Sam bana so, bana so bana 'kaunar wannan dambun da Iyami ta nacewa yin sa kullum, watan azumi fa muke amma dan mugunta irin ta Iyami sai dai ta dafawa mutane dambu shi kuma Abbah ba zai ce komai ba.

Hamma na ne ma idan ya sani zai yi magana amma shima gidan sa yake bu'de baki sai dai ya aiko mana 'dan abinda ya sauwa'ka wanda ni kam ma ban ta6a gani da idanu na ba sai dai in ji 'kamshi ko kuma Ummaru ya bani labari ko ka'dan kuwa ban ta6a sawa raina damuwa ba, ni Hamma na ya wanke min komai, dalilin sa nake yiwa Iyami uzuri bisa abubuwa da dama ban fiya ganin laifin ta ba.

Shi da kansa yanzu ya hana ni wanke-wanke yace sai dai Khausar ta ringa yi ai itama ba yarinya bace tunda shekarun ta goma sha biyu yanzu..dole badan sun so ba Khausar 'din ke yi amma 6angaren Iyami da Khausar 'din kuwa tsanata ne ya 'kara ninkuwa musu a zuciya.

A hakan ma ba bari nake kullum tana yi ba na kan kar6a in tayata kusan kowacce rana amma maganar kirki bata hada ni da ita.

Haka na tabbata da Hamma na ya san ba'a bani abin da yake aikowa da zai ringa kawo min nawa ne daban, amma ban damu ba, ban kuma ta6a 'daura aniyar sanar da shi ba, na riga nasan komai da lokacin da Allah ke 'debar masa, ko babu aure akwai mutuwa ai, watarana sai labari...dole sai dai wani ne zai tuna da wani, ni kuwa ko da wani lokaci fata na shine a ko'ina a tuna da Alkhairi na ba sharri ba. 

Kaina a 'kasa na tako da 'kyar 'kafafuna na har'dewa, wallahi lokuta da dama har fargaban shigowar yanayi na damina nake yi saboda irin wannan lamari.

Ga shi ni a rayuwa ta babu abinda nafi tsana cikin abinci sama da dambu, ban sani ba ko sanin hakan da Iyami ta yi ne ya sanya ta nacewa yin sa kullum ta kuma tilasatwa kowa cinsa domin daga shi bata sake dafa wani abin sai ta ga dama....kowa ma agidan yanzu ya saba hatta Abba cin abin sa yake yi ya sha ruwa hankali kwance.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now