P97

90 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...97*

               .......Yadda kuwa jama'a suka yi fata da buri hakan ne ya faru.
Yayin da da yawan su suka kwana da burin zuwa kotu a wannan ranar...gaba 'daya hankalin jama'ah sai ya raja'a akan shari'ar Rayyan duk da shi ba hakan yaso ba, ita kanta Ammi bata san maganar da tayi tamkar sake janyo hankalin jama'a tayi kan shari'ar tasa ba kasantuwar tayi abin ne bisa zafin rai cike kuma da jin haushi, sa6anin yadda taso a janye ma gaba 'daya sai salon abin ya canza zuwa ga 'kaguwa ga sauraran wannan shari'ar.

Ammi bata san hakan ba har sai washegari da idanun ta ya gane mata yadda jama'a ke ta tururuwar zuwa, kanta daurewa yy da farko sai da ta nisa kafin ta farga da kato6arar da tafka.
Haushi kuwa ya kara cika ta.

      'Bangaren Marwa da Zaitoon sun kwana ne cikin yanayi na tsantsan damuwa da rashin sukuni banda kuka babu abinda suke yi har wayewar gari.

Anty Raihana da Ammi kuwa bazaka iya ma bayyana ainahin yanayin da zu'katan su ke ciki kai tsaye ba, Anty Madeena kadai ke cikin farin ciki marar misaltuwa, ganin cewa burikan ta na cika a hankali 'daya bayan 'daya batare da ta 'daga hankalin ta ko abin ya fito daga gareta ba.

Amra bata san wainar da ake toyawa ba dan ita ba gwanar kallon talabijin bace, har sai da 'kawar ta Ameera ta 'kira take tambayar ta abinda ya faru, dan acewar ta taji ana sanarwa da sunan mijin ta da kuma maganar kotu a gidan talabijin..?"
Cike da rashin damuwa Amra tace" wannan gayen! 'Kyaleshi ai fiye da haka ma zakiji indai Rayyan ne tunda ya saba dama..can aikin sane ya jingine ta..."!
" Aikin sa!"
Cewar Amira ta tambaya da mamaki.
" Yes...ke da can kina nufin baki san shi Lauya bane..?"
Da sauri Ameera ta tare ta da fa'din
" ke wannan fa daban ne wlh 'kawata, ni kaina abin ya 'dauki hankalina da zan samu dama sai na halacci kotun nan wallahi tallahi, fata na ma ace bai ga sanarwar mahaifiyar tasa ba ayi zaman, 'kage nake da son sanin irin shari'ar da za'ayi, mahaifiyar sa ce fa da kanta ta bada kashedin..kinga kuwa babban al'amari ne ai".
" Kai Ameerah kina nufin Ammi da kanta?"
" Ita dai.. ko ke baki ga rahoton ba ne...?"
" Ban ma bude Tv yau ba sam".
" tab an kuwa yi bb ke madam..wlh kallo ya barki, ki tuntu6i mijin naki kiji labari toh, nayi mmk ma da har sai da Ammin ta kawo nan, shi da take da damar da zata han fita ko'ina daga gidan ma, taki ka'dan fa zatayi ta cimmasa a 6angaren sa amma har sai da ta kawo nan? ko de bakwa gari ne ke da shi..inji...?"
" Muna nan.."!
Ta bata amsa a takaice da 'dan sanyin sauti.
" Ikon Allah, rabon dai muma muji labarin ne...".
" Ai kuwa! Ku kuma 'yan jiran kota kwana ko? 'yan fa'di ku 'kara"
Dariya Ameera tayi Amra kuwa tace" Wai me tace ne Ammin? Ameera dan Allah sanar da ni, kin sani a duhu fa wlh..ni kinsan ba lallai in sani ba ai..?"
" Inajin shari'a ce tsakanin shi da wasu 'yaran nata daban a yadda dai bayanan suka fito, ko kuma cikin dangi haka da alamu kuma ita bata so hakan ba, ina jin bada son ranta aka shigar da 'karan ba..."
" Yaranta kika ce Ameera..?
" Erh"!
" Anya kuwa?..Kinsan hadin.kan yaran.Ammi kuwa...bana tunanin hakan gaskia sai dai ko a dangi din..amma sunan wa kk ji ta ambata?"
Amra ta tambaya wannan karan cike da ru'dani.
Yayin da Ameera ta cigaba da fa'din" Sunan Rayyan ka'dai nima naji...ni kaina nayi mamaki, gasu sanannu a gari mafi yawa kowa ya sansu, shiyasa kowa ke 'daukin zuwa ganin tataburzar..."

" Yah Subhanallahi...!"
Amra tace tana dafe goshi, take ta nemi nutsuwar ta ta rasa, tsoron ta 'daya kar ace da Sultan za'ayi wannan zaman shari'ar, indai hakane kuwa itama ai zama bai ganta ba domin tasan kashin ta gab yake da bushewa.

Bama tasan lokacin da ta raba wayar da kunnen ta ba sbd tashin hankali.

Kalma guda kuwa ta innalillahi ta kasa zuwa mata kan harshen ta.

Safa da Marwa ta fara cike da tashin hankali har wani zufa ke karyo mata banda jiri da take gani.
Wani 'karan 'kira sake ji a firgice ta 'dago wayar abin mamaki wata tsohuwar kawarta da har ta mance ma da ita bama tasan har a lkcn tana ajiye d number din ta ba sbd rushewar da zumunchin tsakanin su yy da jimawa wai ita ke kiran ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now