P76

113 10 1
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...76*

               .......Ko da ta fahimci nufin sa akan itama ta ci abincin ne sai taji sam bazata iya ba yau 'din, dan ba hk suka saba ba, ganin bazata cin ba take nufi ya sanya shima yin baya ya jingina da jikin kujera alamar shima kenan bazai ci ba sai ta ci.

Tasan yana jin yunwa sosai tunda da kansa ya zo dinning 'din batare da an gayyato shi ba balle ya 6atawa mutane rai, har ma ya riga ta zuwa kuma gashi da rana bai ci abinci ba, hakan yasa taji hankalin ta ya kasa kwanciya, kallon 'yan da'ki'ku suka yiwa juna sannan ya lumshe idanun sa alamun" ba ruwa na ni..."
Dan ya karanci ro'kon da tayi masa cikin idanun ta hadda ma karya wuya gefe.

Abincin ta tsurawa idanu tana tunanin yadda zata yi da shi, ita har ga Allah ba wani son cin abinci da take a yanzu, a hankali ta kai hannu ta 'deba ta kai bakin ta...idanun sa a lumshe amma hakan bai hana shi 'kare mata kallo ba, yana matu'kar son natsuwa a rayuwar shi, shiyasa sau da dama yake shagala wajen kallon ta batare da yasan yana yi ba, yadda take taunan abincin ma wani salon yake badawa, wani kalan atsuwa ne tattare da yarinyar da ya tabbatar ba kowa ke da irin ta ba...wanda hakan ya kuma kara bada babban gudun muwa wajen ingiza sa ga son kusanta kansa gare ta...bai kuma yaushe ya fara jin hakan game da ita ba.

Zuba mata idanu yy wanda bai masan lokacin da ya bu'de su tarwai akanta ba...ita kam bata kalle shi ba sai da ta tabbatar ta ha'diye abincin sannan ta 'dago suka ha'de idanu.

Murmushin gefen baki yy sannan ya sake 'dagowa ya gyara zaman sa, da idanu yy mata alamar ta bashi shima, cike da natsuwa ta 'debo ta bashi abincin tana lura da yadda yau 'din ma yake ta faman tsare ta da manyan idanuwan sa, sai dai ita ko ka'dan bazata iya jurewa kallon sa ba, hakan yaso yasa ta daburce nan gaban sa but bata bari hakan yy tasiri gare ta ba, kawai ta riga kauda idanun ta daga ha'de idanu da shi, yasan dama bazata yi hakan ba, ko da da take iya 'kure shi da kallo ma yasan sbd yarinyar ta ne kuma takan yi haian ne out of 6acin rai, sbd zargin da take ne na ya cutar mata yarinya, wanda ya tabbatar a lokacin ji take da ita ce sama da shi ko kuma zata samu dama da ba 'karamin bugu zata yi masa ba amma bb damar haka.

'Daya ya kar6a ya kuma no'kewa, dole sai da ta sake ci sannan ya sake kar6a...
tasan shi ma'abocin shan ruwa ne idan yana cin abinci kamar dai ita dan wannan ga6ar kam tarayya suka yi kan 'dabi'a guda.

Cup 'din abin shan da ta 'dazun ta 'dago ta nufi bakin sa da shi amma sai ya rintse idanu gami da 'dan ja baya ka'dan cikin ransa yace" Idan kk shayar da ni wannan kuma ai kin yi dani 'yan mata".

Bu'de idanun sa yy akan ta dan ita ma shi take kallo da mamakin sa, sai dai a fili ta fahimci cewa madarar ce baya ra'ayi...

Hakan yasa ta 'dan kalle shi sai kuma tayi 'kasa da idanun ta zuwa kan lips 'din shi dake motsi.." Exotic zaki bani..".
Yace a hankali kamar wanda bai son yin maganar.

Tsaye ta mi'ke ta je ta 'dauko masa mai sanyi cikin 'dayan cup 'din ta tsiyaya sannan ta koma ta zauna, da kansa taso yasha amma yayi fuska dole ta 'daga ta kai bakin sa, ka'dan ya kur6a ta cire ta sake mayarwa ganin tana son sake cirewa ne ya sanya shi 'dago hannun sa na hagun ya 'daura saman nata wanda hakan ne tilasta mata tsayar da cup in abakin sa idanun sa na kallon nata idanun amma ta ki yadda su hade ido.
Sanyin hannun sa da sanyin jikin cup 'din a hankali yake ratsa mata jiki har 'kwalwalwa..hannun nasa ta ritsa da idanun ta, ita dai wannan gargasar da ke jikin sa ba 'karamin tafiya da imanin ta yake ba...sosai yake birge ta ta yadda bata iya hana zuciyar ta bayyana 'kaunar sa.

Shi kansa ma Rayyan ya riga ya gama 'dago ta tunda jimawa, cuz idan tana shafa masa magani ya kan lura da ita yanda take wasa da gashin hannun san wani bin har shagala take batare da ankare ba, balle wancan hannun da ba amfani yake da shi ba 'din shi nashi wani luf yy ya kwanta gwanin birgewa...Wani bin addu'an da take yi masa ma da biyu ne, idan ta na son ganin hannun san ne take zuwa ta janye rigar ta fara tofa masa addu'ah tana shafawa a hankali batare da ta yadda ta kalli fuskar sa ba, shikam har lumshe idanu yake yi domin ba'kon yanayi ke ziyartar sa.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now