P55

85 14 12
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...55*

                .......Tun kafin azahar yake faman neman layin ta amma wayar bata tafiya, sosai yake jin hankalin sa a tashe, ranar ko office ha'kura yayi da shi ya dawo gida musamman yadda yake ji zuciyar sa na mai zafi, fargaba ya gama cika masa zuciya, duk wani 'kwarin gwiwa tasa tuni ta bar shi.

Kwance yake a 'dakin sa har wani zazza6i zazza6i yake ji na shigan sa yayin da Amrah ke gefen sa tana 'ko'karin kwantar masa da hankali sai dai koka'dan bata ga alamun nasara ba.

'Karshe shafa kansa ta koma yi a hankali tana taya shi jimantawa.
Bayan yawan Dialled call dake wayar sa na numbern Nadia ita kanta Amrah ajiye batun kishi tayi sbd yadda taga ya koma ta gwada kiran layin Nadia fin sau goma sha biyar amma duk basu same ta ba.

       Akai- akai yake 'kiran Auwal yana tambayar sa ta iso gida ne Auwal nace masa "a a" shima cab tuni hankalin sa yake atashe musamaman da yake da labarin harin da akai yau a garin na Damaturu sun kuma tuntu6i Anty Yakura ta tabbatar musu da cewar Nadia takwas ma bata same ta a gida ba.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Auwal da Abbahn su ke nanatawa.
Umman Nadia kam tuni ta fara kuka.
Abban su ne ke kokarin kwantar musu da hankali duk da shima 'karfin hali kawai yake amma tuni lamarin ya sanya shi cikin fargaba.

Numbern drivern da Auwal ya kar6a ma yayi ta gwadawa bata tafiya.

Rayyan kam mutuwar jiki bata tashi kama shi ba har sai bayan da Sultan ya 'kira shi yake tambayar Nadia ta iso gidane.."
" Rayyan yace a a
atakaice ya masa bayanin halin da suke ciki ma yanzu haka...na rashin samun ta har ya fara tunanin bin bayan ta.

Ashe Sultan na tare da Ammi ne alokacin sakamakon labarin da suka ji ayanzu nan yasa ta saka shi nemo Rayyan 'din a waya.
Sai dai jin amsar da ya bawa Sultan ya saka ta amshe wayar tace kul kar ma ya fara batun tafia, Maiduguri har Damaturun yau ba su tashi cikin yanayi mai da'di ba, ya bari a cigaba da neman ta awaya a kuma cigaba da addu'a Insha Allah babu abinda zai samu Nadia.

Duk Rayyan bai da wannan labarin sai yanzu domin tuni ya na gida kuma basu kunna television ba.

Amma jin wannan labari shi ya sake ta'azzara yanayin sa dan hatta Auwal da yake 'kira balbale shi yayi na 6oye masa da yake tuntuni bai sanar da shi ga abinda ke faruwa ba.

Wasa- wasa har yamma babu Nadia babu labarin ta.
Kamar wasa kamar gaske sai ga labarin na neman girmama izuwa wani abu daban har wayewar safia.

Rayyan da ya kasa hakuri dole sai da Ammi ta hakura  ta barshi ya tafi.
Tuni ma an riga an saka doka 48hrs a garin so bashi da damar isa har bayan wannan awannin.
Tare da Sultan zasu kuma yaso suyi tafiyar mota amma Rayyan yace sam mota 6ata musu lokaci zata yi...dole badan Sultan yaso ba sai da suka yi bi jirgi bayan cikar awanni arba'in da takwas wanda yake dai dai da cikar Nadia kwanaki uku kenan ba asan inda take ba.

A cikin tsawon kwanakin nan irin ramar da Rayyan yayi har sai ya baka mamaki,  domin lokaci guda ya zabge tamkar bashi ba, bai ta6a zaton yana yiwa Nadia irin wannan 'kaunar ba sai yanzu...ji yake inama inama, inama tun farko bai amince mata tayi tafiyar ba...da yasan wannan tashin hankalin ne zai biyo ba da bazai ta6a amince mata tafiyar ba...sai dai komai nufin Allah ne..komai Allah ke tsarawa.

Kwata- kwata ma mancewa da cikin da take dauke da shi yayi saboda tashin hankalin rashin ta yafiye masa wannan, sai dai lokacin da cikin ya fa'do ransa ma da wuri ya kawar da tunanin sa domin yasan matu'kar ana raye inda rabon sa Allah zai sake bashi wani amma Nadia fa, baya jin zai iya samun mace a duniyar nan kamar ta, mace mai sau'kin yanayi, fahimta, juriya, hakuri da da'din zama.
Mace ce da ya san indai har da gaske damar shiga aljannar ta a hannun sa take toh indai ya kasa bata wannan damar toh bai yiwa kansa da ita kanta adalci ba, babu ta inda ta rage shi sai dai abinda ba'a rasa na daga ajizanci irin na Adam.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now