P5

90 9 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
       *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️...5

                    ....Adam shi ya fara koyawa Mufee kiran sa da Daddy dan acewar sa da izinin Allah karkashin inuwar gidan sa Mufeeda zata taso shiyasa gwamma ta saba tun yanzu.

Ya jima da fallasawa Zaitun asirin zuciyar sa sai dai har yau din nan bai samu gamsashshiyar amsa daga wurin ta ba, yayin da Zaitun ke tsananin mamakin Adam, kokadan bata ga dacewar su ba, Adam kyakykyawan matashi ne 'dan gayu ga ilimi ta kowani fanni yana da shi.  Sau da dama ma takanyi mamakin yadda yake cinye musu lokacin sa wajen ganin ya faranta musu ita da yarinyar ta dan farko ma kokadan bata sake masa fuska sai da Maman Abdul ta dage kafin ta dan fara sakewa sai gashi Adam ya shigar da haske cikin rayuwar su sosai suka canza ita da 'yar ta batare da tasan takamamman lokacin ba.

Adam shike dora mata karatu da kansa kullin idan yazo yakan bata hadda kuma Alhamdulillah tana kokarin ganin ta kawo haddan ta adaidai.

Yaso ta shiga Islamiya tun yanzun amma yace baya so ya dakatar mata da aikin ta tunda yini take amma da zarar sunyi aure dole ne ya sata a amakarantar Islamiya hadda boko.

Ba karamar rawa Adam ya taka cikin rayuwar Zaitun ba shiyasa a yanzun take matukar girmama al'amarin sa.
Hajja tasha yada musu habaici bayan ta ta6a binsa har kofar gida watarana da ya zo bayan Zaitun sun shigo gida.
Zaitun dai bata san me Hajjan tace da shi ba amma tasan ba magana me dadi bace..abin mamaki Adam ko dis maganganun Hajjan basu dadashi ba ganin hakan yasa Hajja ringa sakin habaici idan ta ganshi bai ta6a daga ido ya dube ta ba..." Sau 'daya tak ya ta6a bata amsa inda yace"..Mama ai ita kaddara babu kan wanda bata iya sauka kuma in ma abinda kike tunani kan Zaitun hakan yake ai ni ne da kaina nace naji na gani babu wanda ya tilasta ni.."
Daga ranar bai sake tanka Hajjan ba har ta gaji da ganta ta sarara masa.
Ita kuwa da tasan halin Hajjan tasan ba sabon abu bane indai akan ita da 'yar ta ne.

Adam ya nuna musu zallar kauna ya fito musu da martabar su ya kuma nuna wa duniya cewa su din wasu ne masu daraja, su din mutane ne masu matukar muhimmanci a idanun sa.

Ita kuwa a ganin ta me zatayi ta sakawa wannan bawan Allah da ya wuce ta bashi dama wajen ganin ya cimma muradin sa.

Baban su Abdul kadai ne damuwar ta a yanzu, kuma ko da wasa ko cikin mafarki bata tunanin zata iya aikata abinda yake nufin ta da shi, gashi da zarar ya tafi kamar tsungulin sa ake acan din yake sake dawowa gida, ada kafin zuwan ta gidan kamar yadda Mmn Abdul ta ta6a bata labari tace yakan shafe akalla watanni uku, hudu zuwa biyar bai zo gida ba amma ta lura tun zuwan da yayi ya ganta a gidan sai komai ya canza daga 6angaren sa, dawowa yake duk bayan wata guda, tsaraba kuwa daga ita har Mufee baya wuce su.

Yayin da ta 6angaren Zaitun gwanin tan nasa bai ta6a birge ta ba, bata san dalili ba kam amma har cikin zuciyar ta ta tsani taga yayi musu wani abu makamancin kyauta ko wani abu ta tsani komai da zai fito daga hannun sa.

Baban Abdul shine mutun na farko a tarihin rayuwar Zaitun da ya nuna kaunar sa ga Mufee wanda hakan bai birge Zaitun ba, bata kuma sanya shi cikin layin masoyan ta ba.
Maman Abdul kuwa da ta riga ta gama fahimtar inda mijin nata ya dosa sosai take mamakin sa ganin cewa abin nasa har na cikin gida bai bari ba.
Sau da dama ya kan siyo abu dangin sitira, kayan wasa ko kuma kayan tea ya bata yace ta kaiwa Zaitun din kuma bata ta6a jin haushin hakan ba duk da cewa ta san dalilin sa nayin hakan, amma kuma bata ta6a jin haushin Zaitun kan lamarin ba saboda ta riga da ta san da wa take zaune.

Tsoron ta daya kar wannan mugun halin nasa ya kai shi ga janyo musu abin kunya watarana, dallilin kenan da ya sanya kawai saboda ta canza tunanin sa yasa da kanta ta bashi shawaran auren Zaitun din duk da tasan abu ne mai matukar wahala Zaitun ta amince da shi, ko Adam ma da yaya ta amince masa ballantana Bbn Abdul, gefe guda kuma ga Hajjah ma tasan ko sama da kasa zasu hade bazata ta6a barin sa ya auri Zaitun din ba domin ita datake zaune dasu itace tasan adadin irin kiyayyar da Hajjan ke musu.

BINTEEE ( 'Yata ce)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora