P67

90 12 3
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...67*

               .......Hakan kuwa akayi, lokaci guda kawai wuta ta kama ci a gidan, gateman kuwa dukan tsiya sukai masa sannan suka kulle shi cikin 'dakin sa ko motsin kirki bai iyawa.

Daga Rayyan sai Nuwaira cikin gidan, itama tuni bacci ya fara 'daukan ta dan haka bata farga da wutan da wuri ba har sai da wutar ta mamayi ko'ina cikin gidan..Lokacin da jama'ar unguwa suka farga da wutan take suka fara kawo 'dauki, a dai- dai lokacin ma'aikatan Sultan suka dulmiya cikin su kamar masu kawo 'daukin suma.

Ihun Nuwaira ne ya fargar da shi sai kuma salatin mutane da 'kauri da tiririn wuta dake ratso shi.

A firgici ya mike zai leka window yaga babu hali sbd wutar tuni ta hauro Salati ya fara ya nufi kofa sai dai ina tuni wutar ta ratso parlorn ta kama kujeru babu ta inda zai iya tseratar da kansa ma balle wani ban da ihun Nuwaira da ya ke iya jiyowa.

'Kofofin ma munafukai da jin wutar duk suka 'kara kamewa....Jikin bango ya kalla yaga babu fire estinguisher anan 'kasa, Parlon saman Anty ne ka'dai dama yake ganin akwai basu sa a kasan ba sa6anin gidan su da yake kota ina an sanya shi ko wani 6angaren.

Kuma wutar ta haura sosai abinda ma ya takaita saboda POP dake saman parlon ne shiyasa wutar ta tsaya iya 'kasan amma yasan idan wutar ta mai yawa shima 'din na iya tsagewa so yake ya samu damar haurawa saman stairs amma hakan ya gagare shi.

Ihun Nuwaira da yake faman ji yana sake rage sauti ya fi 'daukan hankalin sa sosai.

Kalle- kalle ya fara ko.zai samu abinda zai iya tallafa masa amma bai ga komai ba, 'Karfen labile da yagani ya jawo ya take da takalmin sa da yake labilen ya riga ya kama da wutar shima, da shi yayi amfani wajen kawar da abubuwan da ke cin wuta agaban sa ya tsallaka gefen da yake jiyo ihun Nuwaira.

Bakin 'kofar ta take tsaye tana ihun, wutan ne ya hanata wucewa tuni kuma haya'kin ya gama ratsata duk ta fara yin sanyi...cikin sa'a sai yaga daga waje ana faman 6alle windown nata ma da yake suma awajen suna jiyo ihun nata.
Ana gama 6allewa ya taimaka mata ta fita 'yan waje suka kar6e ta cikin sauri yayin da hankalin wasu ya koma kansa cike da hanzari ya fara yun'kurin fita shima amma kafin ya kaiga hakan window ya 6antaro ya fa'do masa kan hannun sa, cike da tsananin wahala ya wani saki ihun aza6a ya zube kasa numfashin sa na 'kokarin 'daukewa.

Hankalin masu taimakon tashi yayi sosai, dayake ma kuma unguwar ta manya ce tuni sun yi magana da 'yan kwana kwana hakan ma basu tsaya jiran su ba ruwa suke 'debowa suna watsawa a kokarin su na ganin 'karfin wutar batai tasirin da zata iya illata wa'danda ke cikin ba cikin sa'a ma da fa'duwar Rayyan sai yan kwana kwanan suka iso har motoci biyu.

Su Anty Madeena ma Neighbours din su sun 'kira su sun dawo, fahimtar cewar da Rayyan acikin gidan ya sa Anty Madeena fara kuka sosai tana fa'din ataimaka mata...yaron ta na ciki.

Ganin abinda ya faru da shi kuwa ya sake 'dugunzuma hankalin ta..ta tashi hankalin ta ta kuma tada na sauram mutanen da ke wajen.

Hakan ne yasa da isowar 'yan kwana kwanan aka fara kashe wutar daga inda Rayyan ya fa'di,....da mutuwar wutan kuwa wasu matasa suka fito da shi kawai aka wuce da shi hospital batare da wani.6ata lokaci ba...daga shi har Nuwaira da tuni take a sume.

Babu wanda yasan mafarin wutan balle asan makasudin ta...babu wanda yasan dalilin ta.

Amma ba 'karamin tada hankalin ahalin Sa'ad Auta wutar nan tayi ba.

Daga Rayyan har Nuwaira jikin su bai kone ba but dole suna bu'katar kulawar likititoci...Musamman Rayyan da ya sha'ki hayakin sosai fiye da Nuwaira, an daiyi nasarar zu'ke haya'kin da ka'dan ya rage yayi masa illa ma dan tuni hayakin yayi masauki cikin zuciyar sa dalilin kenan da yasanya duk da an cire hayakin amma sai da sai da ya fa'da doguwar suma, domin kansa ya bugu sosai ga muguwar karayar da yayi a hannun sa na dama ga kuma zafin wuta da  hayakin da ya sha'ka.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now