P15

61 8 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...15*

        "...Hajjaju Zaitun ta gudu..."
Shine abinda take fa'di tun ma kafin ta isa ga Hajjajun...
Sameera da ta leko bayan ta tabi da kallo cike da rashin fahimta...
Yanayin yadda Na'eema ke maganan da karfi ya sanya duk wani dake cikin gidan ankarewa lokaci guda duk akayi haduwar kaska a babban parlourn Hajajjun..kowa na son jiyewa kunnuwan sa rahoto...." Wlh bata 'dakin kaf na bincika Hajjaju.."!
Cewar Na'eema tana duban Hajjaju.

" Kamar ya bata dakin?...kin tabbatar bata bathroom...?"
" Hajjaju duk na duba da alamu ma ta dade da barin dakin dan hadda wasu kayan amfanin su ma babu...".
'Dunguma duk suka yi tamkar umarni ne ya riske su kowa so yake ya gani da idanun sa ba sai an bashi labari ba.

.....Wayam suka ga 'dakin kamar dai yadda Na'eema ta labarta musu..." Zonan ina Sa'eeda? je kira min Baba Habu da Allah...yaushe yarinyar nan ta bar gidan nan fisabilillahi babu wanda ya sani...wannan wani irin asara take shirin janyo min...?"
Tayi tambayar tana duban 'yan matan ta yayin da Sa'eeda tayi hanyar waje  zauwa wajen mai gadi dan cika umarnin Hajjaju.

Tare suka dawo da Sa'eeda yana bayan ta inda ya same su tsatststaye kan kafafuwan su illah Hajjaju da tsayuwan ya gagare ta ta zauna bakin katifa.

Tun kafin ya kara sa isowa gaban su Hajjaju ta jefa masa tambaya," Baba Habu an samu matsala, ya akayi ka bar yarinya ta bar gidan nan batare da ni na sani ba..?"
" Yarinya kuwa Hajiya...wlh bansan anyi hakan ba.."
" Ga shi dai an duba bata nan Baba Habu, kuma dole nasan ta 'kofan gate ta fita  tunda ba wata 6oyayyar hanya bace ta daban a gidan".
" Hajiya wlh ni dai ban ga fitan yarinya ba, ban san kuma yadda akayi hakan ya faru ba, amma ki kwantar da hankalin ki Hajiya bari a dubo ko batayi nisa ba....."
"   Daga haka ya juya ya fita abinsa dan baya so maganar tayi tsayi da shi, cikin ransa yake mitar kun kawo yarinya taga bazata iya irin hallayar ku ba badole ta gudu ba, babu wani inda zani neman ta Allah ya kara rufa miki asiri yarinya..."
Ya fada cikin ransa yana me nufar bakin gate, shima kansa zaman dole yake saboda rashin madafa amma me za sa ya tsaya zaman gadin karuwai 'yan iska...shi be san yarinyar da Hajiyan ke magana akai ba dan bai san an kawo ta bama sauran 'yan matan Hajiyan ne duk ya san fuskar su kuma sukan fita koda su kadai ne su kuma dawo abinsu....koda ya fita yawata wan sa yaje yayi ya dawo yace bai fa ganta ba shi kam.
   .." Wlh Baba Habu yarinyar asara zata ja min, da yake ban fara saka ta cikin harkoki na ba kafin yau din yanzu ne na gama komai akanta har an shigar da sunan ta alayi amma ta gudu yaushe ma na maida gurbin asarar da 'yan fashin nan suka jaza min sai ga wani kuma...?"
Hajiya ta fada da raunin murya.
" Sai hakuri Hajiya Insha Allahu za aganta ".
Daga haka ya juya ya fice abinsa.
Yana Allah wadaran halin su.

   .......Zaitun zama tayi kan tabarmin nan bayan ta kwantar da su batare da ta warware su ba ta zubawa ttitin idanu wanda zuwa lokacin daidaikun motoci ke wucewa har suka zo suka daina wucewan ma gari yayi 'dib, ko'ina shiru kake ji, tana nan tana tunanin duniya tana tunanin irin tata kalar rayuwar, ada kafin Mufee ta shigo rayuwar ta ba haka komai yake tafiya mata ba, amma tun daga ranar da 'kaddarar Mufee ta same ta shikenan rayuwar ta ta canza salo...amma har yau 'din nan har yanzu da take zaune bakin titin bata ji tana danasanin kasancewa da yarinyar ba, bata sani ba, bata kuma san dalili ba amma tana ji har cikin ranta cewa duk rintsi duk tsananin wuya tana tare da yarinyar...tasan jarrabawa ce ta yiwu kuma alhaki ce ta wata fannin, amma Insha Allahu zata jure zata daure komai da zai sameta, tasan dole inda rai watarana Allah zai dube su, Allah zai yaye musu wannan kuncin suma suyi farin ciki.
A kullun adduar ta shine ko da allah yasa rayuwar ta gajera ce to ya sada Mufeeda da ingantacciyar rayuwa inda zatai farin ciki inda za'a kula mata da ita tunda ita ta gaza sama mata farin cikin.

        Sosai ta zurfafa a tunani har bata san tana 'kwalla ba, bata kuma san da wanzuwar wasu matasan samari har guda uku ba tsaye a kanta, irin street boys din nan ne fitsararru marasa imani.
Tsaye suke kowa na kallon ta ta hasken da farin watan ke haskawa.

        Motsin da Mufeeda tayi ne ya dawo da ita hayyacin ta, hannu ta kai ta share hawayen fuskar ta da ta fahimci ya jike, yayin da 'daya hannun ta kai bayan ta tana bubbuga bayan Mufee alamar rarrashi.
                Cire hannun da ke kan idanun nata ke da wuya sai taga tamkar tsayuwar mutun a gaban ta sake goge idanun tayi gami da waro su dan tabbatar da abinda idanun suka gani tabbas mutun ne rungume da hannun sa a kirjin sa tsaye jingine da Pillarn Varandar ya kwantar da kansa jikin pillar.

Da gaske Mutun ne ba ma 'daya ba har su uku jere suna kallon ta.

Zabura tayi kamar zata tashi amma yadda tsoro ya riga ya karya mata zuciya haka taji kafafun ta ma sun karye sunyi sanyi sun gaza daukan nauyin ta.

Dur'kushewa tayi kan gwiwoyin ta ta saki kuka mai tsuma zuciya hannayen ta duk biyu ta kai kan bakin ta tana kuka wanda duk rashin imanin ka daka ji sa kasan cewa abin a tausaya wa ce a lokacin, domin cike da rauni take kukan gami shashsheka duk zaton ta mutanen Hajjaju ne suka biyo bayan ta, dan haka cikin kukan ta fara rokon su..." dan Allah kuji kaina bayin Allah, ku dubi girman Allah da manzon sa ku rabu da mu, wlh yarinyar nan marainiya ce, in kuka rabani da ita bazan taba jin dadi ba dan Allah ku bar mu muyi tafiyar mu, na muku alkawari Insha Allahu bazan sake waiwayar gidan Hajjaju ba har abada.."
Babu wanda yace mata ko _'kala_ cikin samarin nan uku illah 'daya cikin su da ya 'daga siraran 'kafafun sa ya matso gaban ta, ya tsaya a saitin kanta, tsabar tsoro Zaitun rintse idanu tayi da karfi take fadin" Dan Allah kar ku rabani da ita, dan Allah ku bar min yarinya ta, kuji tausayin mu bayin Allah..."
Dukkanin ilahirin jikin Zaitun rawa yake.
_Fiiit.._ taji an fizge mata Hijab a bazata daga kanta...wani zabura ta sake yi da niyyar yin baya take ta bude idanun ta...nan taga ashe har duk su ukun sun matso kusa da ita sun gewaye ta..." BK bayan ta goyo fa...?"
Karo na faro da 'daya daga cikin su yayi magana.

Wanda aka kira da BK 'din ne da wata kalar murya irin ta 'yan 'kwaya yace " ta kwance mana...in kuma bazata iya ba a kwance mata...".

     Jin hakan yasa Zaitun tayi wani kukan kura ta zabura zata gudu ta tsakanin su, da sauri wanda ke daga bayan ta ya rike mata hannaye duk biyu wanda hakan yasa ta kasa guduwan kamar yadda tayi niyya, 'daya mai suna BK 'din ne ya sa hannu ya kwance goyon ta gaban ta, jin Mufeeda na shirin fa'di ne ya sanya ta 'dan gwada yunkurin fizgan jikin ta daga hannun mutumin amma ta kasa, zuwa lokacin kuwa tsab kukan ta ya tsaya hawayen ma tuni ta neme su ta rasa tuni zuciyar ta bushe, bata kuma sake yunkurin rokon su ba dan ta lura ba fahimtar rokon nata suke ba.

    Ganin da suka yi tana musu fizge- fizge ya sa 'daya daga cikin su rike mata 'kafafu yayin da Bk da ke tsaye kanta ya sauke mata wata lafiyayyar mari, sosai marin ya shige dan har jini sai da yan 'dan fito daga hancin ta amma duk da hakan bata bar fizge- fizgen ba, so take ta gwada iya iyawar ta ko Allah ze taimake ta ta iya tseratar da su dan har yanzu a tunanin ta mutanen Hajjaju ne.

       Fizgo Mufee wanda ke bayan tan yayi wanda hakan ya firgita yarinyar har yasa ta sakin kuka mai karfi a razane.
Kukan Feefy shi ya dawo wa Zaitun da nata hawayen, dagaske ta tsorata cin sun cire mata yarinyar a bayan ta, bata fatan wannan ya kasance shine karshen ganin  ta da Mufeeda.

Take ya dangwarar da yarinyar gefe ya kuma sa hannu ya farke bayan rigar Zaitun 'din daga sama har 'kasa batare da yayi la'akari da Zip da rigar ke dauke da shi ba.. nan take kuwa ya raba rigar biyu wanda jin haka ne yasa Zaitun dawo da hankalin ta waje ta guda sa6anin da data raba dan kula da yadda zasu yi mata da yarinya.

Fahimtar abinda mutanen nan ke nufi ya sanya ta jin mafi girman tsoro ya shige ta, yau ka'dai taga illar kwanan titi.

Iya kokari tayi wajen ganin ta kwaci kanta amma abin ya gagara kawai sai ta saki kuka, irin kukan nan mai cin zuciya, kuka na rashin mafita, cikin ranta take rokon Allah tseratar da ita ya tseratar da su baki 'daya...

Wanda ke tsaye daga bayan tan ne ya fisgi hannayen ta baya da nufin kwantar da ita sai akayi rashin sa'a 'kafar sa ta bige Mufeeda take ta 'karawa kukan ta volume lokaci guda tamkar wanda a gutsiri wani sashe daga jikin ta, karan da ya ratsa kaf kewayan wajen baki 'daya, dai-dai tahowan wata ba'kar mota da gudu ta wuce musamman da yake babu kowa sai su kadai so babu wata mota da zatai musu shamaki da gudun da suke shararawa....har motar ta gota sai kuma ya tsaya cak....

_Salmerh_ 😘

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now