P56

83 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...56*

               ........Ammi bata iya ta sake 'kwakkwaran motsi ba har sai da taji tashin sallama da shigowan Rayyan bayan sa kuma Huzaifa ne.

Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sau'ke da ganin Rayyan lafiya 'kalau.

" Afternoon Madam.."
Cewar Huzaifa yana 'dan rissinawa.

Hannu kawai ta 'daga masa amma idanun ta na kan gudan jinin ta ne da ya koma gefe da ita ya zauna yana fitar da huci mai zafi.

Huzaifa bai sake 6ata lokaci ba yayi gaba abin sa domin yasan ko ba'a fa'da masa ba da kansa yasan ba'a bukatar sa a wannan zaman.

" Ammi barka da isowa..."
Yace bayan fitan Huzaifa.
Bata amsa shi ba illa duban sa kawai da take yi.
Jin zuciyar ta take tamkar na tafarfasa ta ciki saboda taraddadi.

Kallon 'kwayar idanun Rayyan ka'dai ya sake 'dimauta mata tunani, domin tasan shima 'din cikin yanayi na damuwa yake.

Bata masan me zata ce ba a yanzun saboda rsananin.karaya da taji tayi, ashe tsugunne bata 'kare musu ba tsoro take kar labari ya sake maimaita kansa.

Rayyan bai ankara ba sai gani yayi hawaye na sakkowa cikin idanun mahaifiyar sa.
Da sauri ya gyara zama daga kishingi'dar da yayi.
" Haba Ammi...haba dan Allah Ammi...idan ke da kanki zaki dinga zudfa hawaye akan irin wa'dannan 'kananun abubuwan ai 'kwarin gwiwar mu zaki kawar mana...ni banga abin damuwa ba tunda gashi Allah ya tseratar da ni...komai 'kaddara ne fa, kin manta ke ke tunatar da mu hakan, kuma kinsan 'karfen bature ba'a iya musu ai...."

Da sauri Ammi ta tareshi.
" Kaimin shiru Rayyan, bana san wannan rufa rufar...irin wannan abin ne kake 'kira da suna 'kananun abubuwa? a tunanin ka idan 'kananun abubuwan da kake ikirari suka cigaba da faruwa har akwai wani sauran 'kwarin gwiwa da zai mana saura ne? mu kam mu labarin mu.shudewa zaiyi talkmore of wani 'kwarin gwiwar mu...?"

Sosai jikin Rayyan yayi sanyi, da duk hannuwan sa biyu da ri'ke kansa da yake ji na juya masa sam yama rasa ya zai yi da Ammi a wannan yanayin baya son wannan 'kwallar tata sam, a cikin 'kirjin sa yake jin ciwon su.

Cike da raunin murya yace" Ammi pls..ki bar kukan haka nan dan Allah.."
Bata kula da maganar sa ba illa cigaba da magana da tayi..." Tsoro nake ji Rayyan, kai kasan abubuwan da sukai ta faruwa a gidan nan bana so wani abu ya same ku, a yanzu ku ka'dai nake dashi kuma kune farin ciki na..taya kake tunanin zan iya kwantar da hankali na bayan irin wa'dannan abubuwan na cigaba da faruwa...?"
Hannun ta yayi saurin kamawa" Ki kwantar da hankalin ki Ammi, Insha Allah babu abinda zai faru da mu, kin manta yaranki are kinda warriors? Insha Allah together we would succeed   tare zamu rayu har 'karshen rayuwar mu..."

Wannan kalmar ce ta sanyaya ranta har yasa ta murmushi.." Rayyan bani labarin abinda ya faru pls.."

Shiru yayi ya kalle ta, a yadda yaga ta 'dan saki rantan nan baya 'kaunar abinda zai sake dama mata yanayi balle har ace shine da kansa ya furta mata da bakin sa.

Tsaye ya mi'ke ya shiga kitchen Ammi ta bishi da idanu, nan ya kawo mata ruwa mai sanyi da cup ya tsiyaya mata ta sha, yana shirin 'karawa tace a a.
Yana ajiyewa kan center table yake cewa" Ki kwanar da hankalin ki Ammi komai ya riga ya wuce ai, bagani zaune agaban ki lafia ba...?"

" Hakane Rayyan but u must tell me saboda gaba, dole musan yadda zamu 6ullowa lamarin ba akan ka ka'dai ba har da sauran 'yan uwan ka, karka manta akwai Sultan, akwai Marwa akwai Raihana sannan ga ni kaina toh idan bamu san ta inda matsalar ke tasowa ba ta ya zamu magance ta...?"
" Ammi ai kowa da kalar 'kaddarar sa..."
Bata ma bari yakai aya ba ta dakatar da shi da 'kiran sunan sa.
" I said u must tell me dole in san komai Rayyan..."
Dole ba dan yaso ba ya bata labari beriefly kuma bai fa'da mata yadda suka yi da Zaitoon ba, domin in tasan cewa yes akwai hannu aciki dole hankalin ta zai 'kara tashi ne.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now