P52

77 8 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...52*

                _.......Cigaban labarin._
               Abban su na da zurfin ciki,  taurin kai da kuma kafiya akan abu shiyasa itama Ammi bata tsanantawa kan tambayar sa abu domin tasan in ba niyya yayi ba he won't tell her anything.

Abinda kawai bata sani ba shine takamammen dalilin da ya sa aka kashe shi, wannan kuwa bata 'dorawa kowa laifi ba...amma batun da Sultan yazo mata da shi ya matu'kar jijjiga ta ashe da dagaske akwai abinda Alhaji ke 6oye mata ba hasashen ta bane kawai ba.
Sai gashi Sultan ya fara bincikowa domin haka ya nuna mata tamkar shi kadai yake binciken as in shi yafi damuwa da lamarin Abbah fiye da sauran.
Kai Ammi ta fara juyawa tana kuka sosai, Sultan bai ma san ya bu'de baki cike da mamakin Ammi ba sam bai san yayi hakan ba, cikin ransa ya ayyana shi kam ya gama kuka ai tun daren ranar da ya ci karo da lamarin da yake zaton suke 6oye masa har Ammi, ba 'karamin aiki ke gaban sa ba a halin yanzu bayada lokacin 6atawa wajen kuka.

Duk da ba shi da cikakken labari kan binciken da yayyen nasa ke yi amma dole sai ya san inda suka dosa, shin dagaske binciken suka fara ko kuwa, shin sun samo wata alama ko kuwa, son sanin hakan yasa yazo ga Ammi da tunanin ko zaiji wani abu daga bakin ta, dan shi 6oye masa suke da tunanin shi yaro ne, yayin da shi kuma yake gani kamar suna 6oye masa ne sbd kasancewar sa bare a cikin su.
Kuma ko wayar Abbahn nasu already tana hannun Rayyan ne, duk da Sultan yaso ya riga kowa samun wayar sbd wani dalili nashi amma hakan bai samu gare shi ba.

Shigowar sa kenan ya tadda Sultan da Ammi na tattaunawa a palorn ta dake sama.
      Sosai jikin sa yayi sanyi, musamman da ganin yadda hawayen Ammi ke zuba 'kasa abanza.
             Nan take jijiyoyin kansa suka fito sosai, sai idanun sa da suka yi ja, a hakan ya zubawa Ammi idanun sa, yana kallon hawayen ta dake 'diga, fatan sa Allah yasa ba gaskiya bane abinda yake zargi, in kuwa hakane yayi al'kawarin koma waye ke da hannu cikin mutuwar mahaifin sa bazai barsa ba.

Da sanyin murya Sultan dake gaban ta yace" Please mana Ammi ki daina kukan haka nan...ni ya kike so inji idan ke da kanki kina shiga irin wannan halin a yanzu..."
Ya 'karashe maganar yana sunkuyar da kansa gami da shafo kan nasa da duk hannayen sa biyu, duba 'daya zaka yi masa ka fahimci cewa yana da babban damuwa a zuciya.

"..Sultan"
Ammi ta 'kira sunan sa cikin tsananin karayar zuciya.
Bai amsa ba illa kai daya 'dago yana duban ta.
"...Dan Allah Sultan yadda ka fara binciko abin nan kai ka'dai ka rufa min asiri ka binne shi kai ka'dai kar 'yan uwan ka suji, Sultan mahaifin ku ya shafe shekaru a 'kalla uku yana jaddada min amanar ku..dan Allah kar ku saka kanku cikin abinda zai zo ya dame mu har in kasa ri'ke amanar da Alhaji ya bar min..."

Shi kam Sultan ido ya tsura mata na tsawon mintina biyu...a hankali da sanyin murya yace
" Ammi..!"
" Na'am Sultan dan Allah ba dan ni ba ka bar wannan zancen kaji.."
" Kai Ammi don't tell me kinsan komai dama kike 6oye mana tun ba yanzu ba...."
Kai tayi saurin girgizawa sannan tace" Koka'dan Sultan ban san komai ba, amma na jima da fahimtar mahaifin ku na cikin tsananin damuwa amma kasan halin sa, bai ta6a ko kwatanta sanar da ni damuwar sa ba...sai dai nasan babu abinda Mutum ya isa yayi wa wata halitta matu'kar ba Allah ne ya tsara masa ba, bansan tasa kalar matsalar ba, ban kuma san ta ina ta taso ba dan haka Sultan bisa umarni na..ka rufe wannan batun ka fuskanci rayuwar ka kaji 'dana dan Allah..."

Shiru Sultan yy ya tsurawa guri guda idanu.
Rayyan kam fasa shigowa ma yayi kawai ya juya ya koma da baya, bazai iya jure ganin mahaifiyar sa cikin wannan yanayin ba sam.

Bayan kamar mintina hu'du 'dakin bb komai sai ajiyan zuciyan Ammi, tashi Sultan yayi batare da ya furta komai ba ya sa kai ya bar saman sitting room 'din.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now