P94

105 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...94*

               .......Cikin zucia ta na furta Allah ka yafe min, yah Allah ka sa kowa ma ya yafe min bisa son zuciyar da na aikata, wallahi ba da mugun nufi nayi hakan ba, 'kaunar ta nake har jikin jini na, Yah Allah ka taimake ni ka bani ikon kulawa da ita, yah Allah ka hana kowa raba ni da ita har abada, Yah Allah ka raya min ita, kasa mata albarka, Yah Allah ka sanya mana nutsuwa a zukatan mu ni da ita, Yah Allah kasa itama ta soni kamar yadda nake kaunar ta Yah Allah...".
Jero Addu'ar kawai nake bansan me nake fada ba domin hankali na sam baya tare da ni a lkcn.

Kallo guda zakai min ka fahimci ba cikin natsuwa ta nake ba.

Bazata kawai naji jakar dake hannu na ta yage, dama tuni ta nuna alamun babu 'karfi isashshe tattare da ita ban kuma ta6a zaton zai min irin wannan butulcin ba...irin Ghana must go 'din nan ce kuma ta jima ana amfani da ita.

Ban damu da yagaewar tata ba kawai na tsugunna cikin hanzari domin ji nake tamkar za'a zo a 'kwace ta ne a waje na, da sauri na baza kayan gaba 'daya, cikin wani zani na mayar da su na 'daure sannan na cigaba da tafiya ta.

Nayi tafia mai nisan gaske domin tuntuni na bawa mahaifata baya kuma har a lkcn ban tsagaita da tafiyar ba, har a lkcn kuma idanu na basu daina zunar da 'kwalla ba.

Lokaci- lokaci nake sa bayan hannu in 'dauke hawayen na kuma waiga idan naji tahowar mota amma da alamu duk babu mai shirin 'dauka ta.

Har na fara gajia da tafiyar amma ban yi yun'kurin tsagaita tafiyar ba.

Koka'dan ban ji araina na damu da kaina ba ko kuma abinda zai biyo bayan tafiya ta ba..ni dai damuwa ta yarinyar ne kawai..burina in ga na bata gata, ta bata farin ciki, domin nasan hkn ka'dai ne zanyi ya kasance na kwatanta cika al'kawarin da na daukan ma mahaifiyar ta...na kuma san ko da tana a wajen su gatan zata samu fiye ma da wanda nake da niyyar wadata ta da shi.

Da 'kyar na samu abin hawa na tare na kuma shiga, sau 'daya na juya na yiwa mahaifata kallon 'karshe, nasan tuni na yiwa jama'ar ta nisa amma akwai wa'danda duk nisan da nayi su suna nan ne kusa kusa da zucia ta.

Bansan inda tafiyar su ta faro ba balle insan inda suka dosa amma sam banji karaya a cikin zucia ta ba...abu guda da nake da tabbaci akai shine sun taso ne daga garin Maiduguri tabbas nasan bazai wuce nan ba sai dai ban san inda suka nausa ba kuma amma hakan ba hana ni shiga cikin motar in zauna ba.

Haka ta cigaba da basu lbrn barin ta mahaifar ta garin iyaye da kakannin ta har zuwa sa'in ha'duwar ta hajia Talatu, zaman su da mwakbciyar kirki Maman Abdul, ba kowa ke dacen samun makwabci irin ta ba, duk da yk zaman haya ya ha'da su amma Mmn Abdul bata rike ta da wannan matsayin ba, sun yi zama ne matsayin Yaa da 'kanwa, rayuwar su gwanin birgewa kafin bayyanar halin Bbn Abdul da yaso tarwatsa mata zucia, irin 'kalubalen da ta fuskanta daga ma'kwabta da 'yan unguwa har ma Tsohuwa mahaifiyar Bbn Abdul da sauran su, irin gwagwarmayar da tasha da mutane akan aibanta mata yarinya domin tana da tabbaci akan cewa yarinyar ta 'diyar halak ce akan hakan kuma ta tsaya ta kuma hana kanta shakkar kowa indai akan kare martabar 'diyar ta ne..sannan Adam bawan Allah, Adam Jibrin 'Dan Maliki masoyin gaskia da take yawan maimaita cewa har ta mutu bazata iya mancewa da shi ba, wanda sanadiyar tarayyar su aka koreta a gidan da dake haya, ta kuma san zai yi ba'kin ciki da tafiyar ta bata kuma sake waiwaiyan inda yake ba har yau 'din nan, yawon titi da yawon bara da duk tayi da Mufeeda, ha'duwar ta Hajjaju uwar 'yan mata, rayuwar ta tare da su har zuwa lokacin da ta gudu ta bar gudan Hajjaju wanda shine sanadin ha'duwar ta da Dr Rasheed da matar sa wa'danda suka kasance mata ba'kin 'kaddara da ya gitta rayuwar ta akaro na farko, a kuma licn da bata ta6a zata ba balle ta shiryawa zuwan ta, tayi kuka sosai, tayi bakin ciki da takaici, a lkcn babu irin tunanin da bata yi ba, ta kuma yi nadaman barin ta gida a wannan lkcn yafi sau shurin masaki, ha'kika Dr Rasheed ya bar mata ta6o a zucia, irin tabon da bata jin yana iya 'ko'kewa har abadan, ko tunowa da lamarin bata fiye 'kaunar yi ba domin yana matukar karya mata zucia, Dr Rasheed dai har abada bata fatan Allah ya sake ha'data da makamancin mutum irin sa ma balle irin 'kaddarar sa.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now