P99

116 11 5
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...99*

               .......Tunda Amra taji batun kotun nan hankalin ta ya kasa kwanciya, gaba 'daya ta nemi natsuwar ta ta rasa...tsoro da fargabar ta a kullum 'kara yawaita yake, kusan kullum da shi take kwana ta kuma tashi da shi...tsoron tonuwar sirrin ta da ta riga tayi amanna da cewa rufe ruf yake.....

Dama tunda taji Anty Madeena ta ta6a fara yin maganar ta fara jin fargaba dan ta fahimci sirrin nata ya fara bayyana amma bayan haka bata kuma jin komai game da hakan ba, kwatsam sai kuma ga batun kotu.
Ita kanta tasan Sultan mai laifi ne, amma shakkan da take ji a halin yanzu ta tabbata ko shi Sultan din bai kaita shiga firgici ba.
Tsoro take ji sosai, ba na komai ba kuwa sai na ratsowar sunan ta ko yaron ta Arfan cikin kotu gaban alkali, gaban 'dimbin jama'ar da ita kanta bata san iyakar su..kuma a har yanzun babu wani makami guda da ta rike da tke tunanin zai iya fidda ta cikin zargi domin bata kawo tonuwar sirrin ta nan kusa ba.
Sai yanzu ma take ganin wautar ta, gaba daya ta rainawa kanta da wayon ta a halin yanzu...wannan sanarwa da Ammi ta fito tayi sai take ji tamkar dan ita kawai aka yishi, domin a tara jama'ah a kuma bayyana sirrin ta gare su.
Innalillahi kawai take fada.

Baki 'daya wa'danda ke tare da Amra sai da suka fahimci sauyin yanayi da tsantsan damuwa da ta shiga.

Tsoron makomar ta take a wajaje da dama..ba ga iyaye ba, ba ga al'umma ba, ba ga kotun ba, ba ga shi kanshi uwa uba Rayyan ba.

Bayan yanke Ameera,  layin Marwa tayi ta nema bata samu ba sbd wayar da ta sake 'din na 'dan bata matsala hakan yasa ba ko da yaushe ake samun ta ba..uwa uba yanayin da itama take ciki.

Gidan Ammi Ameera ta fara zuwa kuma tun asali dama ita tana da 'dabi'ar fara zuwa sashen Ammi gaida ta kafin isa 6angaren Amra..tun ma lokacin Amra na gidan haka take.

Ko yanzun ma kamar yadda ta saba haka tayi.
Ammi na jin da'din wannan halayya Ameeran sosai, ta kuma ji dadin zuwan ta na yau 'din bisa na ko yaushe.

Dan ko bb komai tana so taji motsin su Amra amma Rayyan ya hana kowa zuwa ko tuntu6ar su acewar sa ai da kanta ta tafi so shi bb ruwan sa.
Anan ne Ameera ke sanin cikakken bayanin ai Amra na gida sun je hutu tuntuni inda Ammi ta sakaya maganar sbd fahimtar cewa Ameeran bata san komai ba.

Bata sha wani wahalar zuwa gidan mahaifin Amran ba da yake ta sanshi, sunsha hira da Amra sosai anan take bata labarin duk abinda ta sani game da zaman kotun.

Sai a lkcn hankalin Amra ya 'dan kwanta bayan fahimtar ai bb sunan ta a zaman kotun har akayi aka gama.
Dan tana da tabbaci da ace akwai sunan ta da Ameera bazata 6oye mata komai ba.

Da kanta take bawa Ameeran labari a ta'kaice na abinda ke faruwa da har yasa ta dawo gida sai dai bata fito fili ta fadi mata waye Arfan ba, ta dai ce 'yan uwan Rayyan da 'kannen sa ke neman raina mata hankali ita kuma bazata iya zama tana kallon su ba, ba ma zata iya zuva idanu ana ci mata fuska akaran banza ba, hakan yasa ta dawo gida a kwatan mata 'yancin ta.

'Yar murmushin gefen baki Ameera tayi sannan tace" ban ta6a sanin baki da wayo ko na sisin kobo ba sai yau Amra.."
Idanu ta waro akan Ameera da alamun tambaya.
Kai Ameera ta jinjina mata alamun tabbatarwa ta sake fadin tabbas Amra baki da wayo sam sam".
" akan wasu can 'yan uwan mijin ki, bama shi ba fa Amra..'yan uwan sa kk ce amma sai ki ri'ka wasa da auren ki? Shin bake ce kk ce min sun yi masa wani auren da 'yar aikin ki ba...?"
Shiru Amra tayi tana me tunanin yaushe ma ta fa'di wannan abin kunyar.

Ameera ta cigaba" Toh wlh tun wuri ki shafa kanki ruwa ki yiwa kanki fa'da, bb inda ya kai mk 'dakin mijin ki, ke in takaice mk ko yaron ki kular da zai samu gaban mahaifin sa ba 'daya yake da na wani wajen daban ba, haka kawai akan wani dangin da bama kullum kk ganin juna ba sai ki tattare ki taho gida da yaro..sai kace babu gurbin kwakwalwa cikin kanki...?"
Da sauri Amra tace
" Ke..har fa da mahaifiyar sa..?"
Ameera ma cike da 6acin rai ta cigaba
Sai kuma kiyi ai..ni dai ban ta6a ganin alamun hkan tattare da Ammi ba tun sani na da ita, matar nan tayi ne a rayuwa, kima gode Allah da ya azurta da samun irin ta matsayin uwar miji, wannan rawan kan tun wuri ki nema masa mashiga ki kama kanki...duk wanda zaice miki kin yi daidai toh wlh bb kaunar ki a ransa amma kin ga cewa batuna da kuskure ba tilasta nake yi ba, kina da ra'ayin kanki...kiyi yadda kk so..."
" Matar da ko ba'ko me yaje gidan sai ya yaba da kirkin ta balle matar dake a  matsayin matar 'danta...wlh Amra ki nutsu ki san inda ke mk ciwo, kinsan yadda 'yan mata ma ke bibiyan irin mijin ki kuwa? kina sane da kalar zamanin da muke a halin yanzu ko? kina nan zaune wata zatayi mk wuff da shi sai dai ki kuma jin labarin an mk wata kishiyar banda waccan da kk barsu tare a gida...."

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now