P38

85 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...38*

              .........Tun dawowar Sultan da Marwa kusan kullum sai ta shigo gidan Ammi, da yake ba wata tazara ce tsakanin su ba, hakan yasa ta maida gidan tamkar wajen yinin ta, dan Sultan in ya fita bada wuri yake dawowa gida ba kamar dai Rayyan, duk lokacin da ya dawo kuma ya kan 'karaso ya 'dauke ta su wuce ko kuma ya sanar da ita dawowar tasa a waya sai ta koma da kanta.

Cikin sati biyu kacal Marwa ta saba da Zaitun sosai musamman saboda Mufeeda da farat 'daya yarinyar ta shige ranta, ta kan kuma 6ata lokaci sosai wajen yarinyar tanai mata wasa tun bata saba da ita ba har ta fara sakewa da ita.

Sau tari kuma indai ranar da zata koma gidan ta da kanta ne Zaitun ke rakata sbd tazarar ba mai yawa bace  gidaje basu fi biyar bane tsakanin su.
Sunyi sabo da Marwa kasantuwar ta surutacciya wanda awajen Marwa ta tsinci wasu abubuwa daya shafi ahalin su.

Cikin hirar Marwa take sanar da Zaitun cewa ai mijinta ma 'dan gidan nan ne Zaitun bata yi mamaki musamman duba da yadda hankali kwance Amrah ke lamuran ta cikin gidan, bata ta6a damuwa da komawa gidan ta on time dan acewar ta matukar ta yini anan babu abinda take tsinanawa a gidan ta in yunwa yake jima ya kanzo nan yaci abincin sai su wuce nasu gidan batare da damuwa ba.
Tace in kuwa baya gari gida take tarkatowa har sai ya dawo.

Hajja Ladi ce mai zuba ma yan aiki magani ko su gudu da kansu ko kuma kowa gidan yaji bai sansu 'karshe dole su rabu da su, da 'dai'dai ta ringa koran duk wa'danda ake kawowa aiki saboda hassada kawai da kanta, ita a dole sai ta zama shugaba kuma tafi so duk abinda za'ayi ya zam ita ake wakiltawa ba wata ba.

Ta gwammaci ta kwashe ayyukan gidan kaf akanta da ta bari wata ta shigo dan taimaka mata..dayake in ita kadai ne dinne akan ninka mata albashin ta banda wasu kyaututtuka datale samu daga Ammi musamman sbd yabawa kwazo da kokarin ta.

Ko Raleeya da ta bari suke zama dan 6angare daban take aiki ne shiyasa.

Haka take yi kowani lokaci shiyasa take ita ka'dai har zuwa kan Zaitun da Sultan ya yakama tana barba'de kan abincin ta tana surutsi 'kasa 'kasa, bai ci abinda take fadi ba amma kallo 'daya yai mata yasan ba ta da gaskiya.

Sultan bai tanka mata ba har sai da ta gama ta kuma maida maganin bakin zanin ta sam bata damu ba ko damuwar wani zanta dan tasan ita ka'dai ke da lokacin shiga kitchen da wannan lokacin so bata yi tunanin wani zai zo ba tana juyowa tana yatsina fuska sai tayi arba da shi tsaye hannayen sa har'de bisa kirjin sa yayi crossing kafafuwa yana 'kare mata kallo.

Take jikin ta ya fara kyarma ta fara waige-waigen da ya tabbatar da cewa bata da gaskiya.

A hankali Sultan ya 'karaso ciki yana mata kallon kin yiwa kanki duk da bai san mai ta aikata ba bai kuma san manufar ta ba amma hk kawai yaji bai yadda da ita bai.

Duk girma da shekarun Hajja ladi hakan bai hana Sultan tsare ta akan sai taci abincin ba...duk yadda Ammi ta so hana shi wannan hukuncin amma fir Sultan ya rufe idanu ya'ki sauraron kowa dan shima gwani ne wajen rikici da kafiya da rashin mutunci.

Tana kuka tana ro'kon sa amma hk ya murje idanu ya ce sai taci, ita kuwa bata son taci itama gudun kar maganin yayi aiki akanta ne dan idan ta bar gidan bata san kuma inda zata kai kanta kwatankwacin wannan gidan ba a wannan zamanin.

'Karshe su Jessy da Yussy ya 'kira 6oyayyun securities 'din shi da Rayyan ne da ba kowa ya san da zaman su ba sbd tsaro, mutun biyu ne da bindigogin su a hannu suka tsaya akanta dolen ta sai da ta ci abincin nan da ganin bindigu saitin kanta....Hajja Ladi tana ci tana kukan bakin ciki kuma Sultan yace duk abincin zata cinye ba ragi.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now