P98

147 11 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...98*

               ......Zaitoon dai bata waigo ba har yanzun kamar yadda bata 'daga 'kafa ta cigaba da tafiya ba.

Lura da Rayyan yayi Mufee bazata zo wajen shi ba yasa ya ciro wayar sa sakamakon yawan hotunan su da yake gani da Marwa a status yasa wannan dabarar saurin fa'do masa.

Camera ya shiga ya nuno mata fuskar wayar ai kuwa tana ganin hakan tatafi da gudu wajen sa tana washe baki.

Murmushi ne shima ya wadaci ilahirin fuskar sa, batare da 6ata lkc ba kuwa ya 'dauke abar sa cak yayi gaba da ita.

Duk wani yanayi na bakin ciki da yake ciki neman su yayi ya rasa sakamakon kasancewa tare da gudan jinin sa da yayi...wata ni'imtacciyar fara'a da yanayi na annashuwa ne suka maye gurbin yanayin sa na baya.

Shirun da Zaitoon taji yasa ta waigowa da sauri nan taga wayam,
babu Mufee babu Rayyan, alamar wanzuwar ta wajen ma bata gansa ba, take ta ha'de gira, sake fitowa tayi sosai ta le'ka gefe da gefe amma babu su gabas da yamma ta kalla bata gansu ba.

Haushi taji ya kama ta amma matakin sa bai kai ba yadda take jin haushin sa abaya ba.

Haushin ta fitowar da Mufee ta sa tayi ta kuma 'dauki 'kafa ta bisa.
Itama cike da jin haushin ta koma 'daki sai kuma ta kasa zama...sarai tasan bazai cutar da yarinyar ba amma sam har a zuciar ta ta kasa jin nutsuwa.

Window ta tafi tana hango waje...direct wajen parking windown ta ke hangowa, hakan ya sa ta 'kurawa wajen idanu ko kyaftawa ba bisa ka'ida take yin sa ba.

Sai dai ko alamun gifatwan mutum kamar sa ma bata gani ba.

Rayyan kam 6angaren sa ya tafi da Mufee haka kawai sai yake jin sanyi aran sa, wani farin ciki yake ji na taso masa marar misaltuwa, yana kuma 'kara godewa Allah da bai bawa Sultan nasarar kawar masa da ita a dunia ba har ya bashi sa'an gano matsayin sa gare ta.

Youtube ya shiga ya sanya mata Nursery Rhymes a wayar sa nan ya fara ganin dariyar ta sosai tana nuna su kamar ta san su dama can.

Rayyan zama kawai yy yana kallon ta kamar hoto, wai wannan halittar tashi ce...gudan jinin sa ce da gasken gaske..?

Ji yake tamkar cikin mafarki.
Wani murmushi ne mai kayatarwa ya kwace masa.
Bai ma san lokacin da bakin sa ya bu'de ba.
A hankali ya furta.
" Nagode Nadia, ubangiji Allah ya gafarta mk, Allah yayi miki rahama ya saki cikin bayin sa muminai..."

Kallon da yaga Mufee tayi masa ne yasa ya fahimci a fili yy maganar.

Murmushin sa ne ya 'kara fa'da'da, da duk hannuwan sa biyu ya kama kuncin ta..." Bazan ta6a gajia da gode ma Allah ba Mamana, bazan kuma ta6a gajia da sanyawa mahaifiyar ki albarka ba na kyautar ki da ta barmin kafin barin ta dunia....daga yanzu har zuwa girman zanci gaba ne da jaddada miki cewar kiyi tasbihi ga mahalicci, ki gode masa ki kuma dawwama kinawa mahaifan ki biyu addu'a da ya azurta ki dasu, masu kaunar ki masu sadaukar da komai domin kiyi farin ciki kiyi walwala..."!

Ba fahimtan komai tayi ba amma yadda taga yana murmushi itama sai ta murmusa har gefen kumatun ta na lotsawa...a hankali ta mayar da idanun ta kan abinda take kallo.

Rayyan tashi yayi tsaye sannan ya sa hannun sa daya bisa kanta, cike da 'kauna ya shafa kan sannan ya shiga ciki da niyyan yin wanka, har kuwa ya gama ya fito Mufee na nan tana kallon wayar bata nuna alamun gajia ba.

Murmushi ne ya kubce masa saman fuskar sa...kusa da ita ya matsa yana mi'ka mata hannu yace..." Precious how far..?"
Kallon hannun tayi, sai kuma ta kalli fuskar shi.
Kamar an tsikare ta sai ta ajiye wayar tana 'ko'karin sau'kowa bisa gadon da ya ajiye ta.
" Tea.." tace tana duban sa.
Ido ya waro domin bai fahimci abinda take fa'di ba.
" Mammi..tea.."!
Ta sake fa'da tana 'ko'karin neman hanyar waje tana dame fuska.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now