P70

84 8 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...70*

               ......." Saboda Allah na amince Ammi da kuma ke...."!
    Zaitoon ta bata amsa cike da dakiya domin in dai zata biyewa zuciyar ta, yadda take ji da banda kuka babu abinda zata sawa Ammi a wannan lkcn, sai dai dole ne ta bawa kanta 'kwarin gwiwa bisa abubuwa masu dama, ba dan komai ba sai dan kawai taga bata karya zu'katan wa'danda suka mutunta a rayuwa ba, taga cewar ta rama alkhairin da suka yi mata da wani alkhairin ko da bai kai wanda su suka yi mata ba.

A ganin ta Ammi tafi 'karfin komai a wajen ta musamman ma a yanzu da ta tabbatar tana da bu'katar taimakon nata da gasken gaske.
" Zaitoon kar ki biyewa su Raihana ki takurawa zuciyar ki akan abinda kika san ba ra'ayin ki bane, aure wa Rayyan ba wai dole bane kawai sbd wasu dalilai ne da na tabbatar akwai auren da babu shi babu abinda zai canza shi, sai dai kasancewar auren na iya sau'ka'ka al'amura ba ma ka'dan ba, kar ki tilastawa zuciyar ki dan nima ba wai na sa auren nasa araina sosai bane...".
Kai Zaitoon ta girgiza tana kallon gefen Ammi tace.." Ammi in dai har su Anty Raihana da Anty Madeena da kansu zasu same ni har 'dakin da nake zaune kan wata magana toh na tabbata mai muhimmanci ne, kuma akwai dalili kwakkara da zai sa su nemi taimako na, Ammi ban manta ku 'din su waye agare ni ba balle na iya juyawa maganar ku baya, Ammi kiyi fatan alkhairi tsakanin yin sa ko barin sa Allah ne zai bayyana mana,  nima din ta 6angare na hakan ne, bazan kuma gushe ina neman za6in Allah ba har sai naga abinda ya tabbatar min...".

" Zaitoon ki fahimce ni, bana so a takura mk ko shiga hakkin ki akan wannan maganar koka'dan asan wace ke na kuma wasu daga cikin ra'ayoyin ki duk da ba kowanne ba amma ina da tabbacin baki da ra'ayin wani aure dai dai da 'kwayar zarra cikin ranki..toh mene amfanin sa...?"
Shiru Zaitoon tayi tana duban gefe ban da sara babu abinda kan ta ke mata amma bata so tun yanzu Ammi ta gama fahimtar rikitar yanayin ta balle ta cigaba da tuhumar kanta bisa tursasawar da ta ganin sun mata bayan tasan Ammin sai tafi kowa farin ciki idan ta amince da auren Rayyan kawai 6oyewa take cikin ranta.
Ammi ce ta cigaba da fa'din..." Ki 'kara zurfafa tunani kinji 'diya ta, idan kin tabbatar zuciyar ki tayi na'am da batun ina tabbatar miki da cewa sai na fi kowa farin ciki akasin hakan ma bazan ta6a ganin laifin ki ba Zaitoon..."
    Wasu siraran 'kwallan da suka zubo mata tayi saurin sharewa cikin ranta ta ayyana" _Anzo wurin_ !...dama tasan hakan ne kamar Ammi tasan menene cikin ranta adaidai lkcn.
Tana mai 'kakalo murmushi a zahiri ta furta" Ammi na gama tunanin fa shiyasa ma na yanke shawara kuma har zuciya ta, ba wannan ba Ammi ko wani abin ne daban da ya fi wannan girma matu'kar bai sa6awa addini ba Insha Allahu zan iya mk shi Ammi indai har zai sa zakuyi farin ciki da faruwar shi, domin kun min fiye da yadda zan iya yi muku a duniyan nan...ba kuma zan yi sbd abinda kukai min bane kadai Ammi, ba kuma sbd kunyar kar in ce a a kuji babu da'di ba ne, zan yi ne kawai sbd Allah da manzon sa, baya ga haka ma Ammi kin manta na 'dan lokaci ne ba wai na har abada ba Insha Allah ba wata matsalar da za'a samu daga 6angare na na kuma yi mk al'kawari zan yi fiye da yadda kuke tsammani daga gareni da iznin Allah Ammi.....".

Cike da farin cikin da ke fitowa tun daga zuciya Ammi take fa'din " Nagode..'diyata, nagode sosai Zaitoon Ubangiji Allah yayi mk albarka ya albarkaci rayuwar ki data zuri'ar ki, Insha Allah nima nai mk alkwari da zaran Rayyan ya samu lafiya hankula suka 'dan kwanta zan bincika mk iyayen ki zan kuma fahimtar da su su kar6e ki ke da 'diyar ki a yadda 'kaddara ta gina ku, Insha Allah za ki rayu cikin farin ciki tsakanin 'yan uwa da dangin ki tamkar kowa...".
" Allah yasa..!Nagode Ammi..."

Yadda Ammi tayi farin ciki da wannan lamari kar ku tona zuciyar Raihana, Marwa da Anty Madeena, banda sauran 'yan uwa da suka zo daga wasu garuruwan domin duba jikin Rayyan din, suma da zarar sunji labarin abinda mahaifiyar Amrah tayi sai suji babu dadi, gashi Raihana da Anty Madeena sam basa rufe maganar da gangan suke bayyana ta ga kowa sbd a 'kalubalanci lamarin a kuma yi saurin amincewa da batun Zaitoon.

BINTEEE ( 'Yata ce)Kde žijí příběhy. Začni objevovat