P87

139 16 5
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...87*

               .......Cikin sa'a zuwa yammaci ma sai naji 'kirjin nawa ya sake ni sai dai ciki na dake min mur'da haka kuma na kwana ina fama da shi, da 'kyar ma na 'dan samu na saka wani abu a baki na lokacin sahur sanin da nayi cewar banci wani abin kirki lokacin bu'de baki ba gudun kar azumin ya wahal da ni.

Kusan kwana nayi idanu na biyu, ina jin babu da'di sosai cikin raina, na kan kuma yawaita jin fa'duwar gaba duk da dama ba yau na fara fuskantar irin hakan ba, da jimawa na ta6a yiwa Hamma na maganar yace in rin'ka maimaita _La'ilaha illalallahu wahdahu laa sharikalahu yuhyi wa yumit, wa huwa ala kulli shai'in qadeer.._ a lokacin ban ta6a mantawa ba na kan yawaita yin sa kuma Alhamdulillah na samu sassaucin jin yawan fargabar at times ma sai inji kamar ana bin bayana idan ina tafiya amma yanzu duk hakan babu su, sai dai a yau 'din a yadda na lura fargabar tawa kusan duk bayan wasu mintina 'kara tsanani take yi.

Sosai jiki nake jin raina babu dadi, gashi har a lkcn banajin dadin yanayin ciki na dan bai sake ni gaba 'daya ba....

Ban 'dora duk wannan matsalolin kan komai ba face Dambu da naci, na kuma 'dauki al'kawari cikin zucia ta kan cewa da iznin Allah.. bazan 'kara cin dambu ba koda kuwa shine ka'dai abinda ya rage da zanci a gidan matu'kar ba shine abu na 'karshe da zanci ya min sanadin aljanna ba, ya wahal da ni kuma yana kan wahal da ni 'din ba da wasa ba.

Komin kadan din sa naci baya bari na yin rayuwa cikin natsuwa ta.

Yanzu haka fa zawo nake yi zaryar yi, daga lokacin sahur zuwa yanzu na shiga bayi fin sau hu'du...ka'dan-ka'dan nake ji kamar zazza6i na shirin kamani, ga uban fargaba ga mur'dawar ciki dake 'karuwa min, gefe guda kuma zaryar zuwa bayi gashi banda wani da zai tsaya akaina ya kula ni ko in samu arzikin samun magani sai dai Hamma Bukar ka'dai.

A hakan a daddafe ina yi ina hutawa na samu na kammala ayyuka na na cikin gida da wuri dan nasan yau kam ciro ganyen Iyami babu fashi ne sai dai in gangan jiki na baya tare da numfashi.

Sai dai na kammala komai kafin rana yayi zafi na shirya tafiya jejin da 'yar ledan buhu na da na saba 'debo mata a ciki.

Ina ninke ledar nake ce da Iyami " Iyami na tafi jejin..".

" Adawo lafiya...kuma a tsinko min masu yawa dan kinga ko dabbobi na ma tun jiyan basu samu ciyawa sun ci ba..kuma ki dawo da wuri babu mamaki Goni shigar safia zai yi..."

Da sauri na waigo..." Iyami Goni zai dawo ne dama yau...".
Na tambaya cike da jin dadi duk da cewa ba wani shirin kirki ke tsakani na da shi ba...amma 'dan uwa yafi gaban wasa..kuma ba shakka nayi kewar 'dan uwa na sosai...tunda yasa kai ya tafi can kudancin 'kasa ban 'kara jin ko da labarin sa ba sai yanzun da Iyami tace zai dawo.

Iyami harara ta 6alla min batare da ta bani amsa ba.
Ina 'karasa ninke ledan hannu nake fadin" Allah ya dawo da shi lafia..Allah ya sa ya kawo mana tsarabar kankana..."
" Da yake 'kanin ubanki ne ai dole kice haka..."

Yadda naji suka da 'dacin wannan zagi na Iyami bazan iya kwatantashi ba.
Sosai abin ya min ciwo.

Shin menene laifin magana ta..?
Ko kuwa laifi ne dan furta hakan ga 'dan uwa na jini na wanda muke uba 'daya da shi.

Bansan meyasa naji ciki na ya mur'da daidai da wanzuwar 6acin da naji zucia ta tayi ba.

Ledar nayi saurin ajiyewa na 'dauki buta da sauri na nufi bayi domin hakan nafi bukata a dai- dai wannan lokaci.

Inaso ina kuka, amma sam ya kasa samuwa gare ni, hawaye nake so in fidda ko zai tafi min da ba'kin cikin da ke cikin zucia ta amma ya gagare ni.

Hakan yasa nake jin wani 'daci da bugawar zucia na daban ba irin wanda nake ji a safiyar ranar ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now