P59

80 7 1
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...59*

               ........Koda ranar Monday tayi ba'a samu damar mi'ka Mufeeda skul 'din ba kamar yadda suka tsara sbd yanayin jikin ta, hakan yasa Ammi tace abari sai ranar Tuesday kawai akaita that's  washegari kenan.

      Ai kuwa washegarin gudun karya manta ma Ammi da kanta ta 'kira wayar shi da sassafe ta tunatas da shi.

Sam ba haka yaso ba amma da yake Ammi ta dage sai shi da kansa zai kai yarinyar ya sanya shi amincewa domin bashi hujja ko ikon yin jayayya da ita.

7:02am ya fito cikin shirin sa, sai da ya duba Amrah ya tabbatar babu wata matsala kafin ya fito zuwa sashen Ammi.

        Shirye ya tadda su duk a Palorn 'kasa, Ammi da Mufee zaune gefen ta tasha wanka cikin wata ha'daddiyar shiga sai Zaitun dake daura da su fuskar ta babu yabo babu fallasa.

   Ammi ce ta amsa sallamar tashi yayin da Zaitoon ta amsa ciki- ciki ahakan ma sbd kawai sau'ke nauyin addini ne amma ko kallo bai ishe ta ba har a zuciyar ta.

       Taso kawar da kai daga kallon sa amma tuna cewa a yau shi ke da ragamar  rayuwar su ya sanya ta dole maido da hankalin ta gare shi.

Gaishe shi tayi a takaice Rayyan kam bai ma amsa ba illah kallon ta da yayi ya kuma 'dauke kansa, tasan amsar kenan matukar baiyi niyyan yin magana da bakin sa ba.

    " Shikenan kuje toh.. idan yaso duk abinda ake ciki naji labari daga bakin Zaitoon idan ta dawo..."
Ammi ce ta fa'di hakan bayan sun gama gaisawa da shi.

Har ya mi'ke sai kuma ya dubi Ammi cikin hanzari, yana ha'de gira yace..." Wace Zaitoon kuma Ammi...?"
" ina nufin uwar Mufeeda, idan baka santa ba gata nan gefe na toh 'dan nema kawai...".
Cewar Ammi a 'dan kufule.

Sau 'daya ya kalle ta ya wani 'dauke kansa yana sake ha'de rai sosai" wai Ammi hadda ita za'a ne? Gaskia ni bazan kuma dawowa gida dan kawai in sau'ke ta ba tayi zaman ta tunda ba cinye mata 'diyar zanyi ba..."

Ya fa'da ransa 6acin rai na son taso masa yana me kama hannun Mufeeda dake gaban Ammi.

Mufeeda bata yi gardamar binsa ba dan Ammi ta gama lalla6an ta tun 'dazun akan  zasu je da Mammyn ta da Uncle Rayyan skul a siya mata kayan wasa.
          
                   Sai da Mufeeda taga suna shirin barin Palorn ne kafin ta dan waigo ganin Zaitoon a zaune yasa ta fara 'kiran sunan ta tana shirin kya6e baki.

Fahimtar hakan da Rayyan yayi ya sashi 'dago ta cak zuwa gefen kafa'dar sa ya rungume ta yana fa'din " shiii"...suka cigaba da tafiyar.

Zaitoon kam mutuwar zaune tayi, kamar wasa kamar gaske take ganin fitar Rayyan da Mufeeda su ka'dai daga gida, motsin kirki ma kasawa tayi sbd al'ajab 'din maganar sa.

Rayyan kuwa bai zame ko'ina ba sai motar sa da aka ware masa zai fita da ita, ciki ya sanya Mufeeda sai dai yana ajiye ta tana sake 'kan'kame shi da sakin kukan da bai fito mata tun 'dazun ba...tana 'kiran" Mammi.."

          Rasa yadda zai yi da ita ma yayi.
Da farko iska ya hura abakin sa yana jin tamkar ya maida musu yarinyar ciki, shi bazai iya raino haka nan kawai babu gaira ba dalili ba.
Haushin wannan lamari duk ya tsaye masa a zuci, meyasa Ammi zata tilasta lallai sai shi bacin ga mutane da yawa da zasu iya sada yarinyar da skul ba lallai sai shi da kansa ba.

Idan kuma tafiso na gida ya kaita ina laifin Sultan toh amma wai sai shi...abinda ko Marwa ma aka bawa dama zata iya mi'ka ta.

Dabara ce ta fa'do masa dan har ga Allah bai san ta yadda zai lallashi yarinyar ba, shi ba gwanin lallashi bane balle yace zai ma gwada, wayar sa ya zaro yana sake gyara ri'kon da Mufeeda tayi masa.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now