P49

93 13 12
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...49*

                 ........Fa'da sosai Ammi tai mata kan yanke shawarar tafiya da tayi batare da ta sanar da ita ba, ita Ammi a sonta daga nan gidan Zaitun bazata sake zuwa ko'ina ba sai gaban iyayen ta, tafi so ta damkata a hannun su kamar yadda ta yiwa kanta alkwari tun farko.
Meyasa Zaitun din bazata yi hakuri ba, ita kanta tasan ba gaskia Amrah ke fadi ba kuma ko awajen bata goyi bayan ta ba meyasa daga baya Zaitun din zata yi fushi ta tafi.

Tana ganin kamar batai mata adalci bane ko me take nufi.
Hakuri Zaitun ta bawa Ammin sannan ta sake komawa dakin su da ta baro.

Ta 'dauki tsawon kwanaki kafin walwalar ta ta dan dawo dai- dai, ba komai yafi tsaye mata ba face zancen satan nan, Ammi kuwa bata tashi sanin cewa Amrah bata gidan ba har sai da aka shafe tsawon sati guda.

Rayyan ne da ya shigo 6angaren ta take tambayar sa Amrah fa tace har yanzu fushin take yi dani ne naga bata leko nan ba, ka sanar da ita nace tayi hakuri ba nufi na in 6ata ranta ba ne.
" Ammi ai Amrah tun ranar can bata kwana gidan nan ba.."
Ya bata amsa a ta'kaice
Yana shirin mi'kewa.

Gira sosai Ammi ta ha'de tana duban sa" Me kake nufi Rayyaan..?"
" Ta tafi gida naje bayan kwanaki biyu da tafiyar tata amma ban samu ganin ta ba.."
Shima fa'da sosai Ammi tayi masa na rashin sanar da ita da wuri da bai yi ba ta inda take shiga bata nan take fita ba, tace meyasa zai yi kan irin wannan maganar bacin yasan yanayin da Amrahn ke ciki, kai ko 'dar ma bakaji, taya zaka bari har sati guda bata tare da kai bayan kasan da 'karamin ciki ajikin ta, idan wani abu ya samu cikin fa..."
" Ammi ni bazan iya zarya ana cimin zarafi haka nan kawai ba, 'karshe ma nayi magana Amaran yanzu haka bata Kano tana Kaduna nayi bincike kuma na tabbatar da hakan ne dagaske...babu yadda zanyi ne Ammi, umarnin mahaifiyar ta take bi itama."
" Kuma da aure da cikin duk take wannan yawon..?"
Ammi ta tambaya cike da 6acin rai.
" Rabu da su Ammi..in hauka suke ji na 'dara su, na riga na sanar da ita, ko kwarzanen abu ya samu cikina I would not hesitate in 'daure mutum babu ruwa na, nd tasan zan aikata.."
Tsaki Ammi tayi ta wuce sama.

Washe gari tana da tafiya agaban amma ta soke shi zuwa rana ta gaba.

Da kanta taje gidan su Amrah dan ganawa da mahaifan ta kan batun amma kamar yadda mahaifiyar Amrah ta shaidawa Rayyan haka ta shaida ga Ammi.

Sosai ran Ammi ya 6aci, sai taga ma kamar raina musu hankali kawai suke son yi, bayaga haka taya za ace sai su ne zasu bata dokar yadda rayuwar gidan ta zai kasance, kamar dai yadda Rayyan ya bar gidan cike da 6acin rai haka ma Ammi, inda duk suke yin tafiyar su batare da an tsaida magana guda muhimmiya ba.

Tun faruwar lamarin can Zaitoon bata sake aikin komai cikin gidan ba, wannan karon koda Marwa ta dawo gidan Ammi ta tare gaba daya, dan Sultan yayi wata doguwar tafiya zuwa kasar senegal.

Sosai suke samun time susha hira yadda ya kamata da Marwa.

Sosai take zuzuta girman da Moopy ta kara a idanun ta,
round face ne da ita da manyan idanuwa da hasken fata dan Mufee fara ce tas ba kamar Zaitun ba take choculate ba fara sosai ba, yanayin shape din fuska da yanayin jikin su iri daya ne  haske ne dai ya bambanta su hakan yasa tace ko batace ba ba kasafai ake tantama wurin bayyana Mufeeda 'diyar tace ko ba tata ba.

Wannan zuwa na Marwa shi ya 'karo sha'kuwa mai 'karfi tsakanin su da Zaitun dan Marwa har ta fara zancen zasu shiga Islamiya tare.
Bacci ka'dai ke raba su da Zaitun, hatta abinci tare suke ci da Marwa adakin ta, kokadan bata nuna musu kyama.
Suttura kuwa yanzu Zaitun sai dai ta bada ga wasu, duk wani nauyin kayan 'kawa na rayuwa itama yanzu kewaye take da su.
Sosai ta kara samun wayewar rayuwa, ta murje ita da Moopy tamkar basu ba.
Tare suke komin su da Marwa hatta unguwa tare suke zuwa har gidan Anty Madeena da ta kasance kanwa ga mahaifin su.
Aikin da yaka ma su suyi tare suke yi, in an gama abinci ma suci cikin plate guda hatta Moopy yanzu sun kara sha'kuwa da Marwa sosai, yarinya ta fito tsab ta juye kalar 'yan gayu.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now