P37

63 11 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...37*

            ........Kamar yadda ya bu'kata haka Amrah ta shirya washegari suka sake ha'dewa, dan ita kanta bata san dalili ba bata iya bijirewa maganar sa.
Komai Sultan yace ko bata ra'ayin abin haka sai taji zuciyar ta ta tilasta mata yin sa.

Ko Rayyan bai san ta fita ba dan ko daren jiya daya dawo ya tarar zazza6in nata ya dawo da kansa yayi mata treatment ganin yanda duk tayi laushi, har ya fara zargin ko shigan ciki ne amma bai sawa ransa ba dan gudun kar azo kuma ba hakan bane.

Duk da haka washegari sai daya ja jinin ta ya mi'ka asbitin da yake aiki a take aka gwada masa aka tabbatar masa da cewa babu komai sai 'yar maleria.

     Baiyi mamaki ba dan shima yafi kyautata zaton malerian ne kuma treatment 'din sa yake mata.

Haka yake yini 'kiran wayar ta dan tabbatar da lafiyar ta da kuma shan maganin ta akan lokaci.

Yayin da duk amsa wayar da Amrah ke yi bata a gidan, tana can tare da Sultan a wani tsadadden hotel.

Shiri sosai tayi kafin ta fita, harda socks da ni'kabi ga dogon hijabi da ta sanya, in ba dai wanda yai mata farin sani ba ba lallai ne a gane ta ba.

Kwanaki kusan shida kenan tana yiwa Rayyan 'karyar ciwo yayin da gefe guda babu ranar da bata ha'duwa da Sultan kuma duk abinda yake so yake yi da ita...gajiyar ha'duwar ta da Sultan take bayyanawa ga Rayyan matsayin bata da lafia, hatta Ammi sai da tazo duba ta har side 'din ta, haka ma Marwa musamman tazo gaida ta.

      Bata samu lokacin Rayyan ba har sai da Sultan ya sarara mata akaran kansa bisa shiryawar ta, dan tasan yanayin ta ita, jikin ta irin jikin nan dake son gyara akai- akai a koda yaushe yakan bu'kaci gyara, matu'kar ta 'dan 'dauki lokaci bata yi amfani da kayan gyaran jiki ba ita kanta ta kan fahimci wasu canze- canze, ganin yadda Sultan ya ri'ke mata wuta kuma ya sanya ta'ki yarda tayi amfani da komai dan matukar tayi toh bazai fasa neman ta ko na rana guda ba, tana.shan azaba kam amma haka take jurewa har sai da ya 'kure da kansa...ai kuwa shirin ta yayi aiki dan Sultan da kansa ya sarara ya kyale ta yana sake jaddada mata cewar ta tambayi Rayyan ku'di tayi gyaran jikin ta.

Baki ta tura tana kukkuni 'kasa- 'kasa da ta tabbatar zai ji ta.
" Shi ina ruwan sa, ba cin duk kaine ka lalata komai shi yaushe ma ya bani ku'din, kuma idan ya bani ku'din bakai ke amshewa ba.
" Kar ki damu wannan karan wlh bazan amsa ba, ai dani za'a kwashi garar, dole in bari kiyi dan kina bukatar hakan sosai, Matata ba haka take ba kuma ban ta6a bata ku'din gyaran jiki ba...".

Fa'dan hakan da yayi ne ya sanya suka yi rabuwar baran baran, tana masifar yana ha'da ta da matar sa bacin shi ne yafi nace mata.
Yana mata daria yace " Kema ai kinaso kinga sabon jini kin li'ke min shiyasa da nace hy kike cewa Yesss..."
Fuu ta tashi ta nufi bayi cike da haushin maganar sa tace " Zan kuwa baka mamaki.
" Babu yadda kika iya dani 'yan mata..".
Ya 'karashe yana dariyan mugunta.

Abinda ya faru kenan tsakanin Amrah da Sultan aranar ha'duwar su ta 'karshe da shi.

Tasan gaskia ya fa'da mata tana bukatar gyaran ita kanta ta sani amma ko giyar wake tashe bata isa taje ga Rayyan da wannan batun a yanzu ba sai dai ta nema tayi da kanta, shi kuma Sultan tasan bazai ta6a bata ku'di ba, dole ta yanke shawarar neman ku'di wajen mahaifiyar ta.

Cikin rashin sa'a kuma a daren ranar Rayyan ya nemi hakkin sa wajen ta ta sigar da yasan bata ta6a iya bijirewa bukatar sa.

Ba 'karamin mamaki yayi ba da jin Amrahn tasa ba kamar yadda ya tsammata ba, bayan duk ku'da'den da ya ajiye mata kwanaki tara baya, kuma yana da tabbacin tun ranar bai sake kusanta kansa gareta ba sai yau 'din, kenan bata yi komai ba, amma ai Anty Madeena ta sanar da shi cewa ta ha'da mata komai ya akayi haka.
Ko dai bata yi amfani da su bane.

BINTEEE ( 'Yata ce)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu