P60

88 13 10
                                    

💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...60*

......Wayar ta tasa a akawo mata ta k'ira shi sai dai bai samu zuwa akan lokaci ba sai bayan ya tashi a aiki.
Anty Madeena cike da 6acin rai take duban sa har abin yaso bashi tsoro.
Sai dai wannan kallon da take masa shafan mai akan tambayar da ta jefa masa wacce ya jita tamkar saukan ruwan zafi saman fatan jikin sa.
erh mana ruwan zafi dan shine zafi da radain.sa ke rasawa direct izuwa ga zuciyar ka...amsa kuwa maganar tata ta fara yi masa har bai san lokacin da ya mike tsaye ba a firgice..." Wai Rayyan dama wannan yarinyar 'diyar kace shine kk 6oye mana ko kuwa ni ka'dai kake 6oyewa.....?"
Da 'kyar ya iya sau'ke idanun sa kanta la66an sa na rawa ya furta"...Anty wace yarinyar kike magana akai...?"

Harara ta buga masa " Wace kuwa banda Mufeeda..kar ka raina min hankali Rayyan...".

Ido yazaro cike da firgici yace " Anty Mufeedah kuma...? Ni 'din...?"

Kai ya girgiza yana sau'ke ajiyar zuciya yace" wlh kin bani tsoro Anty, ni har na isa in 6oye mk abinda na jima ina nema ne Anty?"

" Maganar fahimta nk so muyi Rayyan kar ka 6oye min komai...wato dama munafurtar mu kayi ganin ta haifa ma yarinya shine ka shirya kawo ta gida ta hanyar Ammi Aseeya da sunan taimako mata ko...?"

"...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..Haba Anty mana, haba dan Allah..sai kace baki sanni ba, Anty manta waye Muhammad Rayyan kika yi ne...ban san inda maganar ki ta nufa ba sam how I wish mafarki nake...".

Ya 'akarsa da dafe kansa da duk hannuwan sa biyu, sosai yake jin babu da'di da kalaman Antyn tasa.

Wani gatsau- gatsau yake jin suke sukar sa hatta kansa juya masa yake yi.

Bata ce da shi komai ba sai ta fara kiran mai aikin ta..." Nuwairah!...Nuwairah!!... Nuwairah!!!.."
" Na'am Hajia.."
" Kawo min yarinyar nan".

Rungume a jikin Nuwaira suka fito an sake mata wanka sai dai babu kayan da zata saka hakan yasa aka maida mata da nata bayan an wanke shi har ya bushe.

Moopu kuwa na ganin sa sai ta 'kura masa idanu duk da bata shiri da shi sosai amma kunsan yaro wanda ya saba gani shine nasa sau da dama zaki ga yaro na 'kin mutum agida amma dazarar kun ke6e inda bb kowa da ya sani sai kaga ya za6e ka akan sauran....

Haka ma Moopy, dan tana ganin sa da ta gama 'kare masa kallo bayan ta tabbatar shine sai ta fara mi'ka masa hannu tana kya6e baki.

Nuwairah kam Anty Madeena ta kalla sai ta ce da ita kaita wurin sa.."
Tuni Moofy ta fara kuka ganin kamar Baza'a kaita wurin san ba, ana bata shi ta rungume shi tsam tana 'kara volume 'din kukan ta...shima rumgume ta yy sosai a jikin sa yana jin wani iri cikin zuciyar sa..." Mam..mie.! Mammie!!
Ta fa'da da alamun son ganin ta kawai take yi.

Jikin sa sanyi 'kalau yy cikin ransa ya jinjina irin wannan 'kaunar, lalle ya 'dauki alhakin bayin Allahn nan, Itama uwar ya tabbatar tana can ta fice hayyacin ta ita kuma wannan ta makalkale shi da tunanin zai kaita wurin Mammie...

'Yar murmushi yayi yace" Aiki Jaa..."
Wannan fari ne, jan na zuwa daga baya...
Kallon ta yayi da alamun tambaya sai ta 'dora da" Cire rigar jikin ta ka gani..."

Kallan Antyn yayi amma ganin yanda ta saka serious face ya sanya shi yin kamar yadda tace.

Rigar ya cire yana 'dan lalla6a ta da fa'din" Mamin ki kk so ko Baby...bari I wld take u to her...pls stop crying Mammies Angel..?"
Ita kam sai ajiyar zuciya take saukewa.

Yana gama cire rigar Anty Madeena tace" Kalli gefen cikin ta..."
Dubawa yayi amma baiga komai ba..sai ya 'daga kai ya kalli Anty yace" me yake faruwa ne Anty banga komai bafa..hala ciwo taji...?"

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now