P9

72 11 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
        *( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...9*

        
     " Zaitun dan Allah ki amsa ni, u don't have idea about yadda nake jin zuciya ta..ko har yanzu bani da wannan matsayin da zan iya sanin matsalar ki..?"
Shiru Zaitun tayi illa kai da ta girgiza masa kwalla na sauko mata, ba karamin kokari take cikin ranta wajen har hado amsar da zata bashi ba.
Adam da bai fahimci hakan ba ajiyan numfashi ya sauke mai nauyi..." Well!..bazan tilasta ki fadin abinda baki yi niyya ba Zaitun ki rike damuwar ki tunda hakan kika ga yafi miki, amma ki sani ni Adam ina tsananin kaunar ki, ban damu da sai nasan kullin da ke cikin rayuwar ki ba tunda baki yi ra'ayin sanar da ni ba, abinda kadai na sani shine _INA SON KI!.._ I love u Zaitun with all my heart, a shirye nake da kar6ar ko wacce irin kaddara dake tare dake cikin ko wani irin yanayi ina tare da ke".
Duban sa ya maida kan Mufee da ke wasa da agogon hannun sa wani choculate ya ciro cikin aljihun sa ya sa mata a hannu.
Bai dubi inda Zaitun take ba ya cigaba da fadin" Zaitun bana fata zuwa na ya zam miki tamkar takura ne duba da yanayin dana sameki.."
Sai yanzun ya juya ya kalli fuskar ta dake kallon kasa illah hawayen da ke sauko mata" Damuwar ki a zuciya ta nake jin sa Zaitun, kuncin ki, farin cikin ki, walwalar ki ko akasin hakan duk tafiyar su dai dai yake da nawa in baki sani ba yau in fada miki...zan wuce yanzu amma duk lokacin da kika shirya sanar dani damuwar nima a shirye nake in saurare ki.."
Daga haka ya juya ya fara tafiya da takun sa mai birgewa.
Taku uku yayi bai kai ga yin na hudu ba Zaitun ta mike tsaye daga dakalin dake shinfide a kofan gidan.
" Yah Adam.."
Ta kira sunan shi da raunin murya mai raunin amo, bai yi kasa a gwiwa ba ya waigo.." Dan Allah kayi hakuri Yah Adam, ba nufi na in 6ata ranka ba..."
" Na san hakan Zaitun karki damu"
Ya fada yana mai kokarin cigaba da tafiyar sa.." Yah Adam!!".
Ta sake kiran sa a karo na biyu.
Tsayawa ya sake yi amma bai waigo ba" Kar kayi fushi da ni dan Allah".
Maganar tata ma dariya ta bashi amma da yake baya cikin yanayi mai dadi madadin dariyar sai yayi murmushi kawau...sai da ya juyo sosai ya dube ta kafin yace" Me kuma zai sa inyi fushi da abar kaunata..baki min laifin komai ba ai da zai sa inyi fushi da ke".
Mufee dake rungume da kafafun ta tun ganin mikewar Zaitun din tasa hannu ta dago ta sama ta rungume ta sosai.
" Zan fada maka abinda ya faru".

.......*****

                     " Kika ce shine wanda jiya na ganki tare da shi..?"
Adam yayi tambayar bayan Zaitun ta gama bashi labarin kaf yadda lamarin ya faru tun a farkon zuwan ta gidan.
Da kai Zaitun ta amsa shi tana duban gefen sa lokaci lokaci take sa hannu ta share hawaye yayin da Mufee tayi luf cikin jikin ta kamar me fahimtar abinda suke tattaunawa.
" Meyasa baki ta6a sanar dani hakan ba toh..?"
Shiru tayi..." Yanzu da wani mugun abin ya faru dake fa? a tunanin ki zan iya dauka ne? kinsan halin da zan iya shiga ne...?"
" Kayi hakuri..!"
" Mtheew..."
Ya fada yana sake mikewa tsaye dafe da kansa.
Kai kawo ya fara daga gabas zuwa yamma yana tunanin mafita.
Dole ne sai yayi wani abu a wannan ga6ar gudun abinda kan iya zuwa ya dawo...ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi, ga dukkan alamu ya samo mafita ne.
Gaban ta ya dawo ya duka kamar me shirin neman tuba.
" Kinsan yadda za'ayi Zaitun? dole ne sai kin bar gidan nan, bana so ki kara cikakken sati guda a cikin sa in so samu ne ma kafin satin ki kasance karkashin ikona amma duk hakan ba zai faru ba sai da amincewar ki kinsan hakan ko...?"
Da kai Zaitun ta bashi amsa tunanin ta na rarrabewa sashi zuwa sashi.
" Zan yi magana da Hajiya  amma kafin hakan dan Allah banaso ki sake komawa wajen aikin kin nan ki zauna a gida, kuma ki kula da kofar ki duk inda zaki ki ringa kulleshi hatta bathroom bana son kiyi kuskuren sake barin kofa a bude in zaki shiga, dama ni tun farko mutanen gidan kun ba kwanta min suka yi ba amma zan san abinyi, dole zan yi magana da Hajiya ta..tashi ki koma gida...".
Ya karasa maganar da mikewa tsaye hadi da matsawa baya kadan daga gaban ta.

Ko da ya koma gida bacci kaurace masa yayi throughout daren, sake sake yake ta inda zai fara fuskantar Hajiya da maganar.
Shi da ake shirin turashi cigaba da karatu matakin masters shine kuma zai zo musu da wannan sabon batun..yasan sai sun sha drama da Hajiya kafin ta amince.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now