P32

122 10 2
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
_Serlmerh-md_

🅿️ *...32*

                 .......Washegari misalin 9:13pm.
Kwance take tana maida numfashi 'kasa 'kasa fuskar ta yalwace da murmushin da ya 'kawata ilahirin fuskar ta, lullu6e take da wani babban duvet da ya mamaye dukkanin jikin ta illah kanta dake waje,  ba 'karamin gajiya tayi ba, gaba 'daya ta jikkata, bata jin 'karfi cikin jikin ta kona miskala zarratin, hakan yasa ta kasa yin wani kyakkyawan yun'kuri balle ace ta mi'ke tsaye.
Tunani da shau'kin abinda ya wakana tsakanin su bada jimawa ba ya sanya murmushi kasa barin fuskar ta...sosai take so da kaunar sa take kuma girmama lamuran sa.

Tsawon mintina goma sha takwas tana ahakan sannan 'kofan bathroom da take fuskanta ya bu'du.

Tun daga 'kafafun sa ta fara bi da kallo har zuwa saman fuskar sa.
'Kugun sa 'daure yake da towel fari 'kal yayin da hannun sa ke rike da wani 'karamin towel 'din yana tsane ruwan jikin sa da shi.
Gargasar jikin sa ya kwanta luf sakamakon jikuwa da jikin nasa ke da ruwa har kana iya ganin 'digan su tun daga sumar kanshi har izuwa 'kafafuwan sa.

Kallo 'daya zakai masa kasam yana 'daga 'karfe sakamakon irin 'kirar da zaka fuskanta game da shi, ba fari yake can ba skin 'din sa choculate color ne sai idanun sa da suke da 'dan fa'di, sumar kansa kwance take luf gwanin birgewa, murmushi tayi tuno yadda suka sha drama da mahaifiyar sa kwanakin.baya kan ya rage gashin amma ya ki dole ta kyale shi.
Yana da dogon hanci da madaidaicin baki da ya taimaka wajen 'kayatuwar kyan fuskar sa.
Babban abinda yafi birgeta da shi shine jarumtar sa.

Sau 'daya ya dube ta ya 'dauke kansa.
Gaban mirror ya isa ya tsaya, 'kurawa mirrorn idanu yayi yana ganin kansa aciki tamkar wanda akace masa an canza masa kalar fuska ne, idanun sa yake gani da suke ja har yanzun basu washe ba.

Ciki ciki ya saki tsaki sannan ya waiga gami da tahowa cikin wani irin yanayi kamar zai nufi kan gadon sai kuma yayi turus ya tsaya batare da ya 'karasa ba, ko me ya tuno oho.
"...Amrah je ki tsabtace jikin ki kafin kiyi baccin pls..."

Ya fa'di a sanyaye a kuma dake sai dai kana jin muryar sa kasan farinciki bai gama wadatar sa ba.

Mi'ka tayi da ilahirin jikin ta tana daga kwancen..da wata muryar shagwa6a tace.." Baby ban gama hutawa ba fa...".
Ta 'karashe da turo bakin ta gaba.
Ido ya waro yana duban inda take da hannuwan da duk biyu ya kama kugunsa cike da mamakin ta yace " Amrah....."
" Baby Pleeease..".
Ta tare shi da fa'din hakan tana sake narkewa.

Yana shirin sake magana 'karan wayar sa ya dakatar da shi, duban sa ya kai ga wayar dake ajiye kan side drawer yamma da hadadden gadon dake 'dakin.

A hankali ya isa ga wayar... _Mum_ da ya ga ke yawo kan fuskar wayar da alamun hoton zuciya ya sanya shi saurin 'dagawa ya kai kunnen sa.

Sallama yayi gami da gaishe da ita ta amsa cike da nuna kulawa gami da bashi uzurin rashin responding call 'din sa da batai ba 'dazun da yammaci da yai kiran ta.
" Hope kiran nawa bai takura ka ba ganin dare ya 'dan yi..".
"..oh no bakomai Ammi...ban yi bacci ba ai ina wani aiki ne...abubuwa sun cushe min a company ga Sultan ya'ki dawowa..."
"..Sorry son zan mai magana ya dawo, Allah ya yi muku albarka ya kare min ku.."
" Ameen Ammi...".
" Ya Amrah fa..?"
"...Tana nan lafia, thought tayi bacci ma.."
Ya fa'di maganar yana duban inda take idanun su kafar suka ha'de da juna.
" Alright my regards...".
"..Insha Allah Ammi..."
" Ba wata matsala ko..?"
"   Nop, bakomai Ammi..."
" Masha Allah..".
Ya fa'di yana shafo kansa da ruwa har yanzun ke bin bayan sa yana murmushin 'karyar da ya yiwa Ammi na cewar Amrah na bacci.

'Kiran sunan sa da Ammi ta sake yi ne yasa shi natsuwa dan ba.kasafai zakaji ta kira shi da sunan sa ba.

" Akwai ba'ki a gidan fa hope ana kula min da su yadda ya kamata...?"
" Baki kuma Ammi?...Raihana tazo ne...?"
" A a ba ita ba ce...kar kace min baka ma san da zaman kowa a gidan ba Rayyaan...?"
Ammi ta fa'di cike da son jin amsar sa.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now