P12

63 7 2
                                    

💕 *BINTEE* 💕
        *( 'yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...12*

            ......Kimanin sati guda kenan Zaitun na zama cikin mabaratan bakin titi kuma har a lokacin magana be ta6a ha'da ta da ko guda daga cikin masu baran ba.

    Ba burin ta tayi bara dan ta samu kudi ko wani abin ba a a kawai ta za6i zama cikin masu baran ne sbd tana ganin nan ne kawai ya dace da ita haka zuciyar ta yafi natsuwa da su...

Cikin wani kango take kwana gefe ka'dan da titin anan take rayuwar ta ita da yarinyar ta, sai dai babu batun wanka yanzun, babu batun wanki ba kuma wajen kwanciya mai da'di, baccin ma ba samu take tayi sa cikin natsuwa ba sbd tsoron kar tayi bacci wani abin ya saman mata Mufeeda ba karamin kaffa kaffa take da yarinyar ba.

Duk Zaitun ta lalace ta 'kara duhu ta zam tamkar wata zararriya, abinci kam bata rasawa sbd tana da 'dan guntun ku'da'den ta da ta6a bada hankali ta tara shi da niyyan canza musu muhalli, da shi take ta amfani yanzun duk dama ta cinye fiye da rabin sa daga zuwan ta waken zuwa yanzun.

Ta kanzo bakin titin ne ta zauna kan jakan kayan ta gefe kadan da su, bata iya barin jakan ta a gefe ne sbd tsoron kar a raba ta da kayan nata domin akwai abu muhimmi da bata san ta rabu da shi sam aciki, sau 'daya wata mata ta ta6a bata sadaka har ta Naira dari biyu wanda daga nan bata sake samin wata sadakan ba..domin a yadda ta lura ma hatta su masu baran ba sosai suke samin sadakan ba.

Ko yau din ma daga inda take zaune take iya hango wata yarinya daga can tsallake suna fuskantar inda take zaune, yarinyar 'karama ce da bazata haura shekara goma ba wacce ta kasance 'yar jagora ce ga wata mata wacce dukkan alamu suka bayyana cewar idanun ta ne basa gani duba da yadda take tsaye rike da wata sanda, lokaci lokaci yarinyar ke share hawaye.

Duk da Zaitun bata san mene dalilin kukan yarinyar ba amma haka kawai sai taji ta bata tausayi, da farko tayi niyyar basar da ita amma sai taji sam bazata iya ba..rashin nuna jin 'kai da tausayi ba halayyar ta bane ba.

Haka ta tashi rike da jakar kayan nata ta tsallaka inda suke..." 'yan mata me ya same ki ne naga kina share hawaye..."
Ta tambayi yarinyar tana duban ta cike da kulawa.
"...yunwa...nake ji..Yawuro kuma tace bata da ku'din da zanci abinci yanzu...".
Yarinyar ta bata amsa cikin shashshekan kuka.
Wannan mata me sandan ne ta zaburo da niyyan masife yarinyar nan...Zaitun da ta lura da hakan sai tayi saurin dakatar da ita..." Yi hakuri Baaba abin ai bai kai nan ba, kinsan yunwa ba kara ce da ita ba..."
" Nasani Hajiya amma cewa nayi ta'dan dakata mu samu sadaka sannan nima din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..."
Zaitun kam kalmar _Hajiya_ da akai mata la'kabi da shi shine yafi tsaya mata take ya ya dauki hankalin ta gaba daya, wai " _Hajiya_ "ta tabbata dan matar bata gani ne shiyasa, bayaga haka da ko kusanta ta da wannan kalmar bazata yi ba.
....Maganar ta ta karshe ce kadai ta shiga kunnuwan Zaitun..."... _nima 'din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..."_
Hakan ne yasa ta fa'din " ayi hakuri dai Baaba, itan ai yarinya ce...ga wannan ta sama muku abinda zaku ci kafin zuwa anjiman za'a rage kaifin yunwar ai.."
Zaitun ta 'karashe da mika musu Naira dari biyu da aka bata sadakar sa rannan har lokacin bata kashe ba ba kuma ta canza ta ba.
" Allahu Akbar..'yata angode..Allah yashi albarka ya 'kara arziki, Yah Allah ya daukaki darajar ki ya kare ki da dukkan sharri..Allah Ubangiji yayi miki abinda kikai mana, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi."

Cikin zuciyar ta ta amsa da Amin tana mai jin dadin addu'ar...batun yau tasan irin dadin da mutun ke tsintan kansa idan akai masa taimako musamman sa'in da yake cikin halin bukata ba, tabbas itan ganao ce ba jiyau ba.

Goyon dake bayan ta ta gyarawa zama 'dam sannan ta dauki jakar kayan ta da zuwa yanzun ko nauyin sa ma daina ji tayi, domin ya kasance mata ne tamkar abokin tafiya...duk motsin da zata yi yana nan a hannun ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt