P2

181 13 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
       *( 'Yata ce)*

  

*Salmerh MD*

🅿️....2

             .......Cike da zumudi ta shiga dakin can kasan zuciyar ta take jin wani irin kwanciyan hankali, sai dai fayau da taga dakin bayan shigan ta ya sanya mata tsinkan zuciya, ashe da sauran rina a kaba, ta zaci komai ya kammala kenan tunda ta sami dakin, shaf ta mance da cewa bata da komai na amfanin yau da kullun.

Take gadon ta dake a can gida ya fado ranta sai tayi saurin girgiza kai cike da karayar zuciya.
Duk da tasan cewa shima din ba wani gado ne na kirki har na azo agani b amma ko ba komai yayi mata amfani tsawon shekaru wanda ko a yanzun haka da take tsaye cikin wangamemen dakin nan da zata budi ido tagan sa anan gaban ta sai tafi kowa jindadi.

Dakin malale yake da lafiyyan siminti, ga kofa ma mai kyau haka ma windown dakin babu penti kam amma hakan bai sa taga rashin kyan dakin ba musamman da tasan cewa ya dinka nata na can gida.

Matsalar ta daya ne da taji yafi damin ta bata da komai na amfani ko kuma wanda zata rika yiwa yarinyar ta shinfida da shi kuma bazata iya kwantar da yarinyar haka nan kan simintin dakin ba musamman ma dayake a yanzun ana cikin yanayi ne na damina.

Bata ta6a zaton abin zai iya kaiwa har haka ba, sai yanzun idanun ta suka fara raina fata, yanzu ne ma tafara ji aranta cewa meyasa ta aikata hakan.

Ban dama Allah ya dube ta ya tsaida ruwa a iya kwanakin da tayi tana kwanan layi da bata san ya zata yi a wancan lokacin ba, amma da ikon Allah ko digon ruwa dis bai sauka ba sai ma zafi da take kyautata zaton na nunan gero ne.

Jakan tan kawai ta ajiye ta sake fitowa harabar gidan da ya kasance matsakaici, zai yi wahala ace mutun yayi uzurin sa cikin gidan har ya gama batare da gani ko jin motsin kowa ba saboda rashin wadataccen fili da gidan ke dashi sai dai in ya kasance masu rayuwa cikin gidan basa kusa ne.

Cikin kankanin lokaci ta karewa gidan kallo babu laifi yana da kyau da kuma tsabta dai dai gwargwado dan kuwa ko kusa ba ta isa ta hada wannan gidan da can gida da ta baro ba.

Wata kofa dake gefe da nata dakin kadan tabi da kallo ganin sa garkame da katoton kwado bata yi wani dogon nazari ba wajen fahimtar cewa mamallakan dakin basa sa nanne ko kuma shima din layin haya yake da ba a riga an shiga ba tukunna duba da cewa nata dakin ma sai da ta zo kafin aka bude shi gami da bata makullin.

Sallama tayi cikin sassanyan muryar ta daga bakin 6angaren da tun dazun take dan jiyo motsin mutun amma sai taji shiru ba'a amsa mata ba.

Sallaman ta sake rerawa wannan karan da dan sauti tayi shi..can ciki taji an amsa mata bayan wasu dakiku kuma wata mata mai matsakaicin tsayi ta fito.
" a a bakuwa ce ma..barka da zuwa ga gurin zama nan zauna."
Tayi maganar tana daidaitawa Zaituna kujera daga gefe kadan sai kuma ta koma bakin kofar dakin ta ta zauna.

Zama Zaitun tayi itama sannan ta gaida matar dan sakin fuska musamman da ta lura matar kamar bata da matsala ta wajen sakin fuskar ta ga ko wanda ma bata sanshi ba.

" Sai dai ban gane ki ba wallahi.."
Matar ta fada tana 'yar dariya.
Zaituna ma murmushin tayi " Bakuwa ce, amma ta gida...wancan dakin na hanyan waje nake dazun na shigo..."
"...a a Masha Allahu...gaskiya nayi farin ciki sosai kice zan samu abokan hira, gashi kamar ma bayan ki da goyo..."

Takai karshen maganar ne tare da mikewa ta taho ga Zaitun da alamu abinda ke goye abayan Zaitun din take da niyyan karba.

Fahimtar hakan da Zaitun tayi ne ya sanya ta ware goyon ta sauko da ita ta bawa matar idanun ta kur akan yarinyar tana sassanyan murmushi.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now