P77

164 12 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...77*

               ........" Sannu".
yace mata yana shirin zama gefen ta.
Da sauri ta matsar da jikin ta gefen ta tana kuma 'ko'karin cire hannun sa da ke kan goshin ta amma ta kasa 'dagewa, ya kuma 'ki bata damar da zata 'daga 'din.

Sai da yaga ta matsa ne sannan yace.." What..."!
Tayi shiru.
" Ashe babu da'di...ni da kullum kike ta6a min jiki na fa...?"
Yatsina fuska tayi tana kawar da kai gefe.
Rayyan sai yayi 'yar murmushi...a hankali yace..." Ya jikin fa.."
Da sar'kewar murya ta amsa shi..." Alhamdulillah...lafiya ta ma kalau....".
" Kin tabbatar...?"
Ta 'dage kanta.
" Toh zafin jikin fa...?"
" Haka nan kawai....".
Yana shirin sake magana yaji 'karan wayar sa dake aljihun gaban rigar sa.

Duban sa ya kai ga wayar kafin a hankali ya 'dauke hannun sa dake saman goshin ta ya ciro wayar Ammi ya gani...

Yaje gaishe ta ya tarar bata nan sassafe yau ta fita.

Gaishe ta yayi ta amsa sannan ta 'dora da fa'din" Ina 'diya ta?"
" Wace...?"
" Gidan ku Rayyan...".
'Yar dariya yayi" Toh Ammi ai Marwa na can part 'din yau bata zo nan ba...".
" Aww toh...Zaitoon nake nufi, Marwa tace min wai bata ji da'di ba in jika...?".
'Dan kallan inda take yayi sannan ya amsata da fadin.." erh wlh Ammi, tana bacci ne amma da sauki dai Alhamdulillah...".

" Dama me ya same ta?"
'Dan jim yy sai kuma yace" Bata da lafiya ne Ammi?"

" Subhanallah, toh Rayyan a duba ta, in kuma bazaka iya ba, a 'kira Doctor ko kuma a kaita can a duba ta zaifi ko?"

" Toh Ammi.."
" Wanne za'ayi ?"
Ta sake tambayar sa dan tabbatarwa sbd tasan halin.sa da 'kyar ne idan zai bawa maganar muhimmanci.

" Ammi fa na duba ta kuma naga jikin ne da sauki yanzu sai dai zafin zazza6i"
" Baka da hankali Rayyan, ai ba a raina ciwo, plz ka duba ta ko kuma kasa a duba ta, shi ciwo ba'a raina wanzuwar sa..."

'Kayataccen murmushi kawai yy bai ce komai ba, sai da ta sake magana sannan yace" Insha Allah Ammi za'a yi kamar yadda kika ce..".

Ga Zaitoon ya maida duban sa yana fa'din har baccin ya ishe ki..?
Shiru tayi masa bata bashi amsa ba.
Shima bai damu da rashin masawar tata ba dan in da sabo ya riga ya saba da halin ta batun yau ba.
Juyawa tayi 'daya 6angaren tana gyara kwanciyar ta.
" Ba kiji ba...?"
Sai ta 'dan waigo tana 'kan'kance idanu..ina ke miki ciwo yanzu?"
da kai ta bashi amsa alamar bako ina ta hanyar girgiza masa kanta.

" Ammi ta 'kira tace wai akaiki clinic a duba ki, kuma ai naga jikin da sau'ki ko?"
kai ta sake 'daga masa tana 'ko'karin tashi zaune...

" Ke ya kika gani, ko kema kin fiso aje can 'din...?"
Har cikin ranta bata so 'din amma sbd kar Ammi taji babu da'di idan taji cewar ta 'kiya yasa ta fa'din
Bai kai ga rufe baki ba tace" ai ma naji sau'ki, bana jin komai yanzu...."

" Toh...kawai idan ta nemi magana da ke kice da ita anje kinji?"

Shiru tayi bata bashi amsa ba...dan haka ya mi'ke ya fita a 'dakin Zaitoon bata ko sake kallon inda yake ba...damuwar da ke cin zuciyar ta yafi damun ta a yanzun.

Ko dare sai da ya shigo duba ta kafin ya kwanta bacci, anan sai yag kamar ya bayyana damuwar sa akanta da yawa kar taga kamar wani abin ne daban.
Harcya juya zai fita sai kuma ya waigo, bai yi mamakin kama ta da yayi tana kallon sa ba, yasan dole sai anyi hakan..." Kallo na kike..?"

Yi tayi kamar bata jisa ba, me kuma yake so ta fada masa bayan ya ganta ta tana kallon nasa... Kar fa kiyi tunanin wani damuwa nayi dake kema kice zaki kwatanta musamman dan kinga ina ta zuwa duba ki, badan komai bane face dan naga baki da lafia ne, sannan ni ba mugu bane, na kuma san hakkin na kusa da ni, bayaga haka ma rama taimakon da kikai ta min nk mk ba komai ba...kin fahimta...?"

BINTEEE ( 'Yata ce)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن