P42

105 10 13
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...42*

                 Kamar yadda Ammi ta fa'da wata ta tura ta gyara masa inda yake kunfar baki akai 'din tamkar dama can shi ke aikin da kansa.

Amra duk bata san me ake ba sai bayan da aka gyara wajen dan 'karshe ma bacci ne me nauyi yayi gaba da ita ta batare da ta shirya masa ba.

      Ko da ta fito bata tarar da kowa ba Rayyan ya riga yayi ficewar sa..haushi sosai Amra taji da ganin baya gidan, acewar ta taya zai hana ta fita shi kuma yayi ficewar sa batare ma da ta sani ba.
Ta mance cewar fushi tayi ta shige dakin ta ta barshi shi.

Jin wani jiri jiri yasa ta koma ta zauna tana sakin numfashi 'kasa- 'kasa.
Ammi bata tankawa Zaitun kan maganar ba har sai washegari, nan Zaitun tai mata bayanin komai da ya faru, Ammi bata ga laifin ta ba, sai ma laifin Rayyan da ta gani dan shi ya mayar da abin babba, ta kuma san ba wai laifin Zaitun 'din ne asali damuwar sa ba da alamu dama da 6acin ransa yake tafe Zaitun ta taka sahun 6arawo ne, laifin ta 'daya ta gani martani da zagin da tai masa, ta kuma yi mata fada sosai kan hakan domin tamkar 'diya take ganin ta fadan da zata yiwa su Marwa shi zata yiwa Zaitun, kuma ko ba komai Rayyan ya girme mata bai dace ace ta zage shi ta wannan sigar ba.
Itama Zaitun sai a lokacin da ga kuskuren ta, nan tayi nadamar zagin ta kuma bawa Ammi hakuri da alkawarin Insha Allahu bazata sake maimaita irin hakan ba.

Sosai Ammi taji dadi dan haka nasiha ta 'kara yi mata gami da sake bata damar cigaba da komawa bakin aikin ta.

Duk da Zaitun bata so komawa can 6angaren ba amma Ammin ta wuce haka awajen ta...ta koma amma da takatsantsan fin wanda take yi abaya...duk wata hanyar da zata hda ta da Rayyan a gidan bata binta, aikin ta kuma tana yi yadda yakamata amma tafi sakewa tayi aikin idan ta tabbatar ya fita, hatta 'dakin sa ita ke gyarawa ta sharo ada amma daga baya ya hana yace baya so dole ya tilasta Amra take yi masa iya nashi 'dakin ta sharo kullum wataran ma bata yi sai ya kusa dawowa.

A wannan karon an samu sauye- sauye sosai daga Amra, musamman wajen abinci, Zaitun ta rasa dalili, sam bata san mugunta ke sata yi mata hakan ko kuwa menene ba, amma sai ta hada musu abinci Amra zata ce sam ba shi take so ga wanda take so, wani sa'in ma ko tayi wanin kuma ba kula shi zata yi ba.

Ba 'karamin haushi ke kama Zaitun ba, ta kuma rasa yadda zata 6ullo mata.

Ranar kawai ta yanke shawarar yi musu abincin gargajiya, duk da Raleeya ta ta6a bata labarin yadda suka kwashe da ta ta6a yi musu, mai gidan kadai yaci amma Amra bala'i ta ringa surfa mata kuma bata ci abincin ba.
Amma ganin tsirfar da Amra ta tsiro da shi cikin kwanaki yasa ta yanke shawarar gwada sa'ar ta.

Cikin sauki ta ha'de komai ta kammala ta jera musu kan dinning tana dariyar mugunta ta koma 6angaren Ammi.

Cikin ranta take ayyana ita da su ganta sai kuma gobe, in sun so suci in sun so su kwan da yunwa amma ita babu ma mai ganin idanun ta balle tasha kananun surutai.

Ko lokacin da suka zo cin nasu abincin da dare data tuna da su Amra daria taji na shirin 'kwace mata, bata ta6a sanin ita muguwa bace sai yau.

Tuwon semo ta tu'ka musu da miyar kuka, kukan ma da 'kyar ta samu sai da ta zo kitchen 'din Ammi ta 'dauka.

Ga mamakin ta washegari da taje taga dishes 'din bata ga6a ganin sun ci abinci mai yawan na ranar ba.
Shi kansa Rayyan sai da yayi mamakin Amra dan yafi kowa sanin bata son tuwo amma yau ci na musamman tayi masa.
     Har sai da yayi mata daria yana tsokanan ta ko de tuwon Zaitun yafi na kowa dadi ne shiyasa take ci hadda 'kari.
'Yar daria tayi masa sannan tace.." Kai Baby bafa wani dadi, kawai danna taimaka mata naci shine yazam wani abu...".
" Ke de fa'di gaskia...".
" Allah ba wani da'di..ji nayi kawai ina son ci..".
" Hmm"
Yace yana mai cigab da cin tuwon sa.
Zaitun data shirya mugunta sai gashi ta kare da mamakin su.
Bata san shi Rayyan dama asali ma'abocin son tuwo bane samu ne da baya yi ya sa shi hakura, in kuwa ya samu baya yi mata da wasa.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now