P81

97 11 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...81*

               ........Shigowan Marwa da Anty Marwa ne ya dakatar da maganar da Zaitoon ke yi, sakamakon ji da tayi ko sallaman Marwan an rasa mai amsawa a cikin su sbd yadda suka bada dukkan hankalin su gareta.

Saman la66a ta amsa sallamar tana mai waigawa ta dubi Marwa.

Idanu Marwa ta waro ganin yanayin Zaitoon da hannuwa tayi mata alamun tambaya.." Lafiya..me ya faru kuma...?"

Hankalin Both Ammi da Rayyan ma kanta suka koma sbd ganin Zaitoon ta mayar da hankali wajen ta.

Kafin su 'dauke idanun su daga kan Marwa sai wata sallamar suka sake tsinkaya ciki- ciki da wata sautin muryar da suka tabbatar da cewa ba sabuwa take a wajen su ba.

Kusan dukkan su atare suka raya sunan ta cikin zu'katan su amma ko 'daya babu wanda ya nuna alamun farin ciki da ganin ta har ta 'karaso ciki ta samu waje ta zauna.

Sai lokacin Ammi ta budi baki tace..." Amrah..! daga ina haka...?"
" Daga gida muke Ammi munzo..."

Bata ma bari Amrah ta kai aya ba ta jinjina kai gami da fadin..." Sannun ku toh...ya wajen su Mummyn naki...?"
" Suna nan lafia.."
" Haka ake so...".

Duk wannan maganar Rayyan ko sau 'daya bai dubi inda suke ba balle ya nuna alamun yasan da zuwan su, Marwa kuwa tuni ta 'karasa kusa da Zaitoon 'kasa 'kasa tayi mata ra'da a kunne.." Dan Allah me ya faru..naga fuskar ki da hawaye...?"
Zaitoon bata ce da ita 'kala ba illah juya idanu da tayi ta dubi gaban ta hakan yasa Marwa ma ta kai duban ta wajen.

Dabas ta zauna yanayin na sauyawa izuwa na alhini ta kai hannu ta 'dago hoto 'daya..saman la66a ta furta" Anty Nadia...!"

Muryar Amrah ne ya hana Marwa cigaba da magana jin tana mi'kawa Rayyan gaisuwa hadda mikewa ta isa wajen sa tana mai mi'ka masa yaron dake hannun ta.

Rayyan sam bai iya bude baki ya amsa gaisuwar da take yi masan ba sbd tsananin mamakin ta.

Wai yau Amrah haka ko kuwa idanun sa ke yi masa gizo.
Sai yanzu ne ta san da cewar yana da muhimman ci? Bayan sun gama lalaceqar su da Sultan hadda binsa tafia wata 'kasa ta barshi kwance cikin jinya..bata damu ba, bata damu da ko ya mutu ko ya rayu ba sai yanzun da ta tabbatar ya warke shine ya zama mutun ko...?"

Kallon ta yayi ya kuma duban yaron, jikin su fresh sun yi kyau sosai amma kokadan bai ji dai dai da kwayar zarra na kewar su ko farin ciki da zuwan su ba.

Kan yaron ya tsayar da duban sa take yaji wani murmushi na shirin 'kwace masa, bai kuma hana faruwar hakan ba, domin bai ga aibun sa ba idan yayin...cikin ransa ya jinjina wannan iko na rabbiz izzati, yaron bai bar komai na Sultan ba sai ma kamannin su da ya 'kara fitowa.

Alamu yayi wa Amrah da cewar hannun sa baya aiki balle ya kar6e shi sai ta 'dan nuna jimami saman fuskar ta tana shirin magana tajiyo hayaniya na tunkaro palorn saman Ammin da 'dan gudu gudu.

Badi'a ce ta shigo, bayan ta Mufeeda ce sai Imran daga 'karshe.
Yayin da sautin muryar Anty Madeena daga bayan su tana tahowa take yi musu masifar rashin natsuwa.." Ke de Badi'a ban san lkcn da zaki girma ba wlh...".
" Wallahi Anty itama rigima gareta wai fa sai na goya ta kuma nawi gare ta yanzu...".
Badi'an ta fa'da tana mai 'kara hanzari zuwa saman...tace" Mutum sai shegen son jikin tsiya..."

Anty Madeena ce tace" Daina zagar min ita..ai duk laifin ki ne, ba ke kk koya mata ba kuma sai yanzu ki wani ce zaki guje mata...?"

Sallamar da Badi'a tayi ya hana ta sake tanka maganar kasantuwar itace a farko, Imran yayi jin haka yasa Mufeeda ma yin sallamar.

BINTEEE ( 'Yata ce)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora