P71

115 11 3
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...71*

                .......'Kan'kance idanu Zaitoon tayi sosai tana duban sa da mamaki..." Yah Sultan Dutse kuma..? waye dutsen...?"
Shima a zuciye ya bata amsa sbd yanayin 6acin ransa ke 'kara hauhawa musamman daya ga yau gashi ga ita wuri guda amma lkc kadan ya rage ta zama mallakin wani ba shi ba.
Ji yake tamkar ya 'dauke ta gaba 'daya ya gudu da ita yaje ya killace akabar sa kowa ma ya daina ganin ta sai shi ka'dai.

           " Wancan dake kwance yake irga kwanakin mutuwar san nake nufi..!
Yayi maganar tare da yin nuni da hannun sa idanun sa na sake rinewa
".....me kike tunanin zaki samu tattare da shi? Me kike tunanin zai amfanar miki da shi baya ga bauta da zaki yi ta masa har 'karshen rayuwar sa..."
Baya kadan taja sbd yadda yake.fitar da maganar tasa tamkar zai hadiye ta 'danya.
Tana 'dan yamutsa fuska gami da takure jikin ta waje guda tace.
" Yah Sultan dama ai ba dan in samu wani abu na amince da auren ba face dan inyi bautar ka'dai...".
  Sultan ji yake tamkar ya make ta sbd takaicin ta, meyasa ta kasa fahimtar inda ya dosa ne? meyasa sam kwakwalwar ta bata ja koka'dan..shi aganin sa Zaitoon tafi 'karfin tayi wannan bautar har abada sbd itan mallakin sa ce, be san me ya hana Rayyan 'din mutuwa tun a ranar farko ba, bai san me ya tsaya jira ba da har za'a bautar masa da Zaitoon sbd shi.
Ya 'karashe tunanin yana mai watsa hannu alamun dai takaici ke cin sa.

Har ya juya sai kuma yy turus, still dai idanun sa na nan a rine.

Babu komai...a yanzu damar tasa ce gaba 'daya, damar sa ne ya bar Rayyan ya cigaba da rayuwa, damar sa ne kuma ya 'karasar da shi ga hanyar barin.duniyar da ya kamk....amma tabbas bazai bari ba, dole ne sai yayi wani abu guda...wala alla hakan zai iya haifar masa da kwanciyar hankali mai 'dorewa.

      *****
             Ha'ki'ka a wasu lokutan 'kaddara abu ne mai matu'kar ban mmk, mai rikitar da tunani sanya ru'dani da kuma haifar da kwanciyar hankali ga wasu yayin da ga wasu abin ba hk yk ba, sai dai a mafi yawan lokuta 'kaddara takan riski bawa ne cikin yanayi na bazata ko rashin shirya zuwan ta, kuma ta kan zo ne cikin siga guda biyu da suke mabambantan juna, inma kayi farin ciki da zuwan ta ko kuma akasin haka, sai dai ga Zaitoon sam abin ba haka yake ba, sam ko alama har a yanzun ta kasa hasaso yanayin 'kaddararta ta kasancewar ta gidan Ammi Aseeya, ta kasa hasaso karshen 'kaddarar tun daga farkon zuwan ta har zuwa yau 'din nan, har a yanzu da take amsa suna matar Rayyan bata san wani gurbi zata sanya wannan karkatacciyar 'kaddarar ba.

        Abin ya kasance mata ne tamkar wasa ko shirin drama, yayin da ta wani 6angaren take gani tamkar a gaske.

Ga dai ta a yanzu tana nan na da wani gagarumin abu akanta mai suna aure, auren da ta kasa tantance matsayin sa wajen ta kamar yadda ta kasa tantance asalin dangantaka da kuma halayen ahalin gidan Ammi Aseeya.

Tuni ta gama fahimtar mafiya yawan ahalin sun yi na'am sun kuma yi farin ciki da wanzuwar auren, yayin da 'kalilan daga cikin su a fili suka nuna 'kiyayyar su bata kuma san dalili ba.

Abin kuma bai kasance abu mai saukin fahimta ba kwatankwacin yadda auren ta da Rayyan ya kasance mai sauki kuma ya faru cikin sauki, illa bride price da ya kasance mai nauyin da ya bata matu'kar mamaki.

Da ace saukin fahimtar su ya kasance mai sau'ki kamar yadda sau'kin kasantuwar auren ta yake da sai tafi kowa farin ciki sbd cikin kalilan din lkc zata fahimci inda ra'ayin kowa cikin ahalin ya fuskanta....amma ina abin ba haka yake ba, shiyasa duk suka bar zuciyar ta cikin kokonto da wasi- wasi, banda tsoro da fargaba dake 'kara shiganta kusan kowani lokaci.

Cikin lokaci 'kan'kani duk wasu hidindimun Rayyan a hankali kaf suka dawo hannun ta, ita ke masa komai, tun tana jin nawi har tazo ta dan saki jikin ta ganin babu wani mai bi takan kunyar ta.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now