P6

87 9 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
     *( ' Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️...6

         .....Wasa-wasa Bbn Abdul da ya tafi sai da ya shafe watanni uku cif bai waiwayo gida ba wanda yayi dai dai da cikan Feefy watan bakwai da haihuwa, Bbn Abdul sai dai aike kawai da ya saba yi musu ya cigaba...Mmn Abdul kadai abin ke damu domin tasan shirun nasa ba alkhairi yake shukawa acan din ba yayin da Hajja tayi mirsisi ko ajikin ta tamkar ba shi ne kadai kyautar da Allah ya bata na haihuwa ba.

Tuni Mufeedah ma ta fara takawa kadan kadan ba karami dadi hakan yayi wa Zaitun ba ji tayi tamkar zata hadiye ta saboda farin ciki, hatta Adam sai da tai masa albishir washegari cewa Mufeeda ta fara taka kafar ta, bai boye farin cikin sa ba shima in da kara da alkawarin zuwa yaga tafiyar Mufee a ranar da yamma hadda guzurin dandasheshen takalmi.

Matakin kaunar da Zaitun ke wa yarinyar bai ta6a yin kasa cikin zuciyar ta ba sai ma karuwa, zaku yi mamaki idan kuka a yadda Zaitun ke kwana da yarinyar bata ta6a bari Mufee tai juyi ba'a cikin jikin ta ba, kullun kan cikin ta take kwantar da yarinyar ta bata ta6a gajiya da hakan ba sai dai in gari ya waye lokacin in zata yi sallah sannan take kwantar da ita zuwa wayewar gari, shiyasa ko baccin rana mai kyau Mufeeda bata iyawa saboda sabo da jikin Zaitun da tayi.  

Zuwa yanzun kuwa tuni Mufee ta gama sakin jikin ta da kowa na gidan banda Hajja kadai da kullun kyara da tsangwama ce tsakanin su hakan yasa Mufee kokadan bata kaunar zama inda Hajjan take, yarinya ce amma tana da tsananin wayo da takatsantsan sosai tasan me kaunar ta da me kyarar ta.

Su Siyama kadai ne abokan wasan ta sai su yini suna wasa bata damu ba in kuwa suna makaranta da Ahmad take wasan ta.

In ka jiyo tashin dariyar Feefy toh kuwa da Siyama ne ko kuma Zaitun.
Takan ci ko wani irin abinci yanzu shiyasa tuni Zaitun ta huta siyan madara sai dai dan hada mata shayi, dan kullun dare Mufee sai ta tashe ta tasha shayin nan.

Duk lokacin da Zaitun ta dawo gida daga wajen aikin ta farin cikin Mufee bai ta6a 6oyuwa haka zata zo da gudu tana " Mammi!..Mammi..!!" Tana daga hannuwa sama tana dariya.

Kamar dai yau ma hakan ne ya faru Zaitun na dariya ta dago ta sama " Oyoyo Mamana...oyoyo 'yan mata na.".

'Dago Mufeen da tayi idanun ta sak ya sauka kan gashin Mufee ta kalla ta sake kalla take sai ta dan dama fuskar ta tana duban Maman Abdul dake zaune tana jifan su da kayataccen murmushi da yake tasan me hakan da Zaitun tayi yake nufi.
" Kwantar da hankalin ki Hajjaju ba ma tayi kuka ba...ke baki ga yanayin kitson bane bafa sosai na kama mata ba.."

Murnushi Zaitun tayi itama tana lakutan kumatun Mufee tace" Kinyi kyau Feefy na, kin yi kyau sosai 'yar albarka.." Ta karashe da fadin" kuma fa kitson ya haska ta sosai, Mmn Siyama dole abaki tukuici tunda yake bata yi kuka ba...yarinya ta tayi kyau wlh.." Ta karashe maganar tana saukar da Mufee ta dago Ahmad da shima yake 'dago hannayen sa yana fadin.." Feefy.."
Da son shima a daga sa.

" Ahmadi na Feefyn ka yau an sha kitso an zama 'yan mata kyakykyawa..".
" Dama asali mai kyau ce ita, ki ringa bari ana mata kitso kiga yadda yarinyar nan zata dawo, yau ma din kawai gashin ne naga kamar idan aka biye ta taki ahaka zai ta lalacewa shiyasa na kama mata kuma ma in ba a yi mata ai bazata saba da kitson da wuri ba..".

Bata bi takan wannan zancen na Mmn Abdul ba kawai ta gaida Maman Abdul din tare da yi mata barka da gida da kuma ban gajiyar kula mata da yarinya da take yi kullun...yau din haka kawai take jin zuciyar ta wasai..shiyasa murmushi ya kasa barin fuskar ta.

Biskuit, sweet da cheese balls da ta saba siyowa yaran yauma shi ta raba musu kowa ya ansa cike da annashuwa.

" Bari in dan watsa ruwa yau din wlh duk na gaji sosai.
  Ko bayan shigewar ta Maman Abdul tunani kawai ta lula tana duban fuskar Mufee da kullun asalin kyawun yarinyar ke kara fitowa, musamman yanzu da yake Maman Abdul din na kulawa da ita sosai tamkar daga cikin ta ta haife ta...idan baka san Mufee tun farko da Zaitun ba bazaka ta6a tunanin yarinyar ta bace sam.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now