P21

67 8 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

_Wattpad@_
_Serlmerh-md_

🅿️ *...21*

            ......" Ba'kin talauci, fatara, damuwa da matsalolin rayuwa ne suka da'kushe komai da ya dangance ta suka kuma 6oye duk wani sirrin kyawun da Allah ya bata, dan bana jin ko ita kanta tasan ta mallaki wannan sirrin, amma wlh da zarar duk wa'dannan sun kau abu ne mawuyaci Dr Rasheed ya sake yimin duba irin na 'ya mace cikakkiya da daraja matukar yana ganin yarinyar nan gaban idanun sa kuma yasa ta a zuciya...tsoro nk ji kar abin yazo yafi karfi na watarana Anty...".
Bayanin Hameeda kenan da ke zaune kan 'daya daga cikin kujera mai zaman mutun 'daya dake madaidaicin Parlon da ya kasance maha'di ga bedroom din ta, kuma tayi duk wannan bayanin ne ga 'yar uwar ta Anty Saleeha wacce ta cika alkawarin kiran da tace zatai wa Hameedan washegari bayan ta samu isasshen lkcn da zata iya ganawa da ita.
" Ki kwantar da hnkalin ki nace, amma tuntuni kin kasa yin hakan kan wani abu da bai taka kara ya karya ba ki ke ragewa kanki daraja da baiwar da Allah ya baki, abu mai tsananin saukin da ke da kanki ma zaki iya samawa kanki mafita idan kin nutsu kk bi a hankali.."
" Kar kice haka wlh Anty Saleeha dan baki ga yarinyar bane kk ganin kamar abin ba na kirki ba, ki dai na ganin abin kamar me sauki, ni nasan halin da zuciya ta take ciki a yanzu, wani baiwar kyau Allah yy mata da duba 'daya zakai mata ba sai ka 'kara ba za ka fahimta matukar kana da kula, taya zan iya zama da ita cikin gida na Anty na kuma kasance cikin natsuwa da kwanciyar hnakalin da kk fada alhali nasan shi kansa Rasheed 'din abinda nk gani game da yarinyar shima hkn ya fahimta ne yasa shi ajiyan ta zuwa wani lkc, abin takaicin ma fa har yarinya gare ta Anty, kuma na tabbata garin biye- biyen tituna da kwararo ta samo cikin har ta haife, sai ma kin ga yarinyar...wlh duk lkcn da na tuno da su bama na gansu ba sai gaba na ya fadi bazan iya jure yawan ganin suna wulgawa gaba na ba wlh, ina kishin miji na sosai....".
"...Shin ke Hameeda kyanta ne ka'dai ya dame ki..?, baki tunanin makomar ki bayan abubuwan da ake gudu sun gudana, bakin tunanin cushewar al'amura da canzawar su? baki tunanin me ze biyo baya? da bakin ki fa kk ce har yarinya gareta bakya tunanin cewa ta fiki sanin dunia da budewar ido? ba mmk lamfo kawai take mk amma da zarar ta saita komai zaki yi mmk, irin su bada wasa ake bin su ba, domin su 'din tamkar maciji suke, dole sai an musu tashin wuf lokaci guda, cire batun kyawun ta a lissafin ki, kiyi tunanin makomar ki da ta yaran ki anan gaba...a lokacin nasan zaki fi fahimtar duk wasu bayanan da zan mk..."
Da gama fa'din hakan ta fara kokarin datse kiran, fahimtar hakan da Hameeda tayi ne yasa ta zabura ta dakatar da ita da sauri " wlh Anty yanzu ma a shirye nk zan fahimce ki, me zan tsaya jira da har sai nayi tunani?.."
" Naga kamar inda tunanin ki ya tafi daban da inda nawa yk...".
Cewar Anty Saleehan cike da gatsali..cikin ranta kuwa ayyana irin tagomashin Nairori da zata samu take matukar Hameeda ta amince da batun ta.
"...Na dawo daidai nima yanzu, fada min koma menene..."
Cewar Hameeda tana gyara zama cikin 'kaguwa da son jin mafita me 6illewa daga yayar tata.
Murmushi Saleeha tayi sannan ta 'dora da fa'din " Nan kusa da ni ne ba nisa da gidan nan, kisan yadda zaki yi kawai ki taho da ita gida na, chamber ce da ake tara irin su ake mi'ka su aikatau ko wani abin daban ga masu bukata amma za'a yi komai ne bisa tsari da kuma sirrantawa kar ta fahimta kar kowa ma ya fahimta sbd rufin asirin ki, da zarar ta shiga hannun su an dam'kata gare su shikenan bata kuma da wata mafita,  dan suna da tsaro sosai, chamber ce da wani attajiri ke jagoranta kuma be 'dauki abin da wasa ba...da zaran ta shiga hannun su shikenan tunanin ta zai canza sai yadda suka yi da ita, sai abinda suka ce da ita zata yi, wannan shine ka'dai mafita agareki in kinga zaki iya amma..."
Sosai Hameeda tayi na'am da zancen sbd a ganin ta yama fiye mata sau'ki akan shawarar da zuciyar ta ta fara yanke mata na yiwa Zaitun korar kare a gidan, sbd in korar tata tayi gateman zai iya fallasa ta ga maigidan, kuma bata da ikon aiken sa ko'ina domin Rasheed bai yadda ya matsa ko nan da can ba daga jikin gate din, da yake ma ba sallah zai yi ba dan ba musulmi bane..baya ga haka ma in korar tata tayi ba mamaki ta sake komawa can asbitin wajen sa ya kara dawo da ita aikin banza kenan tayi, amma in tabi shawarar Anty Saleeha zata kashe maciji ne tare da sare kansa duk lkc guda dan haka sosai shawarar tayi mata.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now